< בראשית 25 >
ויסף אברהם ויקח אשה ושמה קטורה | 1 |
Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura.
ותלד לו את זמרן ואת יקשן ואת מדן ואת מדין--ואת ישבק ואת שוח | 2 |
Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.
ויקשן ילד את שבא ואת דדן ובני דדן היו אשורם ולטושם ולאמים | 3 |
Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin.
ובני מדין עיפה ועפר וחנך ואבידע ואלדעה כל אלה בני קטורה | 4 |
’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.
ויתן אברהם את כל אשר לו ליצחק | 5 |
Ibrahim ya bar wa Ishaku kome da ya mallaka.
ולבני הפילגשים אשר לאברהם נתן אברהם מתנת וישלחם מעל יצחק בנו בעודנו חי קדמה אל ארץ קדם | 6 |
Amma yayinda Ibrahim yake da rai, ya ba wa’ya’yan ƙwarƙwaransa maza kyautai, ya kuma sallame su daga ɗansa Ishaku zuwa ƙasashen gabas.
ואלה ימי שני חיי אברהם--אשר חי מאת שנה ושבעים שנה וחמש שנים | 7 |
Duka-duka, Ibrahim ya yi shekara ɗari da saba’in da biyar.
ויגוע וימת אברהם בשיבה טובה זקן ושבע ויאסף אל עמיו | 8 |
Sa’an nan Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu da kyakkyawar tsufa, tsoho da kuma shekaru masu yawa; aka kuma tara shi ga mutanensa.
ויקברו אתו יצחק וישמעאל בניו אל מערת המכפלה אל שדה עפרן בן צחר החתי אשר על פני ממרא | 9 |
’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti,
השדה אשר קנה אברהם מאת בני חת--שמה קבר אברהם ושרה אשתו | 10 |
filin da Ibrahim ya saya daga Hittiyawa. A nan aka binne Ibrahim tare da matarsa Saratu.
ויהי אחרי מות אברהם ויברך אלהים את יצחק בנו וישב יצחק עם באר לחי ראי | 11 |
Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku wanda a lokacin yana zama kusa da Beyer-Lahai-Royi.
ואלה תלדת ישמעאל בן אברהם אשר ילדה הגר המצרית שפחת שרה--לאברהם | 12 |
Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.
ואלה שמות בני ישמעאל בשמתם לתולדתם בכר ישמעאל נבית וקדר ואדבאל ומבשם | 13 |
Ga jerin sunayen’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu, Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam,
חדד ותימא יטור נפיש וקדמה | 15 |
Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema.
אלה הם בני ישמעאל ואלה שמתם בחצריהם ובטירתם--שנים עשר נשיאם לאמתם | 16 |
Waɗannan su ne’ya’yan Ishmayel maza, waɗanda kuma suke sunayen kabilu goma sha biyu masu mulki bisa ga wuraren zamansu da sansaninsu.
ואלה שני חיי ישמעאל--מאת שנה ושלשים שנה ושבע שנים ויגוע וימת ויאסף אל עמיו | 17 |
Duka-duka Ishmayel ya yi shekara ɗari da talatin da bakwai; sai ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa.
וישכנו מחוילה עד שור אשר על פני מצרים באכה אשורה על פני כל אחיו נפל | 18 |
Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran’yan’uwansu.
ואלה תולדת יצחק בן אברהם אברהם הוליד את יצחק | 19 |
Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim. Ibrahim ya haifi Ishaku,
ויהי יצחק בן ארבעים שנה בקחתו את רבקה בת בתואל הארמי מפדן ארם--אחות לבן הארמי לו לאשה | 20 |
Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rebeka’yar Betuwel, mutumin Aram, daga Faddan Aram,’yar’uwar Laban mutumin Aram.
ויעתר יצחק ליהוה לנכח אשתו כי עקרה הוא ויעתר לו יהוה ותהר רבקה אשתו | 21 |
Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki.
ויתרצצו הבנים בקרבה ותאמר אם כן למה זה אנכי ותלך לדרש את יהוה | 22 |
Jariran suka kama kokawa da juna a cikinta, sai ta ce, “Me ya sa wannan yake faruwa da ni?” Saboda haka ta tafi don ta nemi nufin Ubangiji.
ויאמר יהוה לה שני גיים (גוים) בבטנך ושני לאמים ממעיך יפרדו ולאם מלאם יאמץ ורב יעבד צעיר | 23 |
Ubangiji ya ce mata, “Al’ummai biyu suna a cikin mahaifarki mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban kuma zai bauta wa ƙaramin.”
וימלאו ימיה ללדת והנה תומם בבטנה | 24 |
Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga’yan biyu maza a mahaifarta.
ויצא הראשון אדמוני כלו כאדרת שער ויקראו שמו עשו | 25 |
Wanda ya fara fita ja ne, dukan jikinsa kuwa kamar riga mai gashi. Don haka aka sa masa suna Isuwa.
ואחרי כן יצא אחיו וידו אחזת בעקב עשו ויקרא שמו יעקב ויצחק בן ששים שנה בלדת אתם | 26 |
Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su.
ויגדלו הנערים ויהי עשו איש ידע ציד איש שדה ויעקב איש תם ישב אהלים | 27 |
Yaran suka yi girma, Isuwa kuwa ya zama riƙaƙƙen maharbi, mutumin jeji, yayinda Yaƙub, shiru-shiru ne mai son zama a tentuna.
ויאהב יצחק את עשו כי ציד בפיו ורבקה אהבת את יעקב | 28 |
Ishaku, mai son ci naman jeji, ya ƙaunaci Isuwa, amma Rebeka ta ƙaunaci Yaƙub.
ויזד יעקב נזיד ויבא עשו מן השדה והוא עיף | 29 |
Wata rana sa’ad da Yaƙub yana dafa fate. Isuwa ya shigo daga jeji, da yunwa sosai.
ויאמר עשו אל יעקב הלעיטני נא מן האדם האדם הזה--כי עיף אנכי על כן קרא שמו אדום | 30 |
Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!” (Shi ya sa aka kira shi Edom.)
ויאמר יעקב מכרה כיום את בכרתך לי | 31 |
Yaƙub ya amsa ya ce, “Ka fara sayar mini da matsayinka na ɗan fari tukuna.”
ויאמר עשו הנה אנכי הולך למות ולמה זה לי בכרה | 32 |
Isuwa ya ce, “Duba, ina gab da mutuwa, me matsayina na ɗan fari zai yi mini?”
ויאמר יעקב השבעה לי כיום וישבע לו וימכר את בכרתו ליעקב | 33 |
Amma Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini tukuna.” Don haka ya rantse masa, ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yaƙub.
ויעקב נתן לעשו לחם ונזיד עדשים ויאכל וישת ויקם וילך ויבז עשו את הבכרה | 34 |
Sa’an nan Yaƙub ya ba wa Isuwa burodi da ɗan miyan lansir. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya tashi ya tafi. Ta haka Isuwa ya yi banza da matsayinsa na ɗan fari.