< בראשית 19 >
ויבאו שני המלאכים סדמה בערב ולוט ישב בשער סדם וירא לוט ויקם לקראתם וישתחו אפים ארצה | 1 |
Mala’ikun nan biyu suka iso Sodom da yamma. Lot kuwa yana zama a hanyar shiga birnin. Da ya gan su, sai ya tashi don yă tarye su, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa.
ויאמר הנה נא אדני סורו נא אל בית עבדכם ולינו ורחצו רגליכם והשכמתם והלכתם לדרככם ויאמרו לא כי ברחוב נלין | 2 |
Ya ce, “Ranku yă daɗe, ina roƙonku ku ratsa zuwa gidan bawanku. Ku wanke ƙafafunku, ku kwana, sa’an nan ku kama hanyarku da sassafe.” Suka ce, “A’a, za mu kwana a dandali.”
ויפצר בם מאד--ויסרו אליו ויבאו אל ביתו ויעש להם משתה ומצות אפה ויאכלו | 3 |
Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka tafi tare da shi, suka kuma shiga gidansa. Ya shirya musu abinci, ya gasa burodi marasa yisti, suka ci.
טרם ישכבו ואנשי העיר אנשי סדם נסבו על הבית מנער ועד זקן כל העם מקצה | 4 |
Kafin suka shiga barci, sai ga dukan mutane, ƙanana da manya daga kowane ɓangare na birnin Sodom, suka kewaye gidan.
ויקראו אל לוט ויאמרו לו איה האנשים אשר באו אליך הלילה הוציאם אלינו ונדעה אתם | 5 |
Suka kira Lot, suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka a daren nan? Fito mana da su waje domin mu kwana da su.”
ויצא אלהם לוט הפתחה והדלת סגר אחריו | 6 |
Lot ya fita daga cikin gida, ya rufe ƙofar a bayansa. Ya je wurin mutanen
ya ce musu, “A’a, abokaina kada ku yi wannan mummunan abu.
הנה נא לי שתי בנות אשר לא ידעו איש--אוציאה נא אתהן אליכם ועשו להן כטוב בעיניכם רק לאנשים האל אל תעשו דבר כי על כן באו בצל קרתי | 8 |
Duba, ina da’ya’ya mata biyu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, bari in kawo muku su ku yi kome da kuke so da su. Amma kada ku taɓa waɗannan mutane, gama su baƙina ne kuma dole in tsare su.”
ויאמרו גש הלאה ויאמרו האחד בא לגור וישפט שפוט--עתה נרע לך מהם ויפצרו באיש בלוט מאד ויגשו לשבר הדלת | 9 |
Sai mutanen birnin suka amsa, “Ba mu wuri! Wannan mutum ya zo nan kamar baƙo, ga shi yanzu yana so yă zama alƙali! Za mu wulaƙanta ka fiye da su.” Suka ci gaba da matsa wa Lot lamba, suka matsa kusa domin su fasa ƙofar.
וישלחו האנשים את ידם ויביאו את לוט אליהם הביתה ואת הדלת סגרו | 10 |
Amma mutanen da suke ciki suka miƙa hannunsu, suka ja Lot zuwa cikin gida, suka rufe ƙofar.
ואת האנשים אשר פתח הבית הכו בסנורים מקטן ועד גדול וילאו למצא הפתח | 11 |
Sai suka bugi mutanen da suke a bakin ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu, suna lalluba inda ƙofar take.
ויאמרו האנשים אל לוט עד מי לך פה--חתן ובניך ובנתיך וכל אשר לך בעיר הוצא מן המקום | 12 |
Mutanen nan biyun suka ce wa Lot, “Kana da wani a nan, ko surukai, ko’ya’ya maza ko mata, ko kuwa wani dai a cikin birni wanda yake naka? Ka fitar da su daga nan,
כי משחתים אנחנו את המקום הזה כי גדלה צעקתם את פני יהוה וישלחנו יהוה לשחתה | 13 |
gama za mu hallaka wannan wuri. Kukan da aka yi ga Ubangiji game da mutanen birnin nan ya yi yawa sosai, ya sa har ya aiko mu domin mu hallaka birnin.”
ויצא לוט וידבר אל חתניו לקחי בנתיו ויאמר קומו צאו מן המקום הזה כי משחית יהוה את העיר ויהי כמצחק בעיני חתניו | 14 |
Saboda haka Lot ya tafi ya yi magana da surukansa waɗanda suka yi alkawari za su aure’ya’yansa mata. Ya ce, “Ku yi sauri ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi.
וכמו השחר עלה ויאיצו המלאכים בלוט לאמר קום קח את אשתך ואת שתי בנתיך הנמצאת--פן תספה בעון העיר | 15 |
Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”
ויתמהמה--ויחזיקו האנשים בידו וביד אשתו וביד שתי בנתיו בחמלת יהוה עליו ויצאהו וינחהו מחוץ לעיר | 16 |
Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai.
ויהי כהוציאם אתם החוצה ויאמר המלט על נפשך--אל תביט אחריך ואל תעמד בכל הככר ההרה המלט פן תספה | 17 |
Da suka fitar da su, sai ɗaya daga cikin mala’ikun ya ce, “Ku gudu domin ranku; kada ku duba baya, kada kuma ku tsaya ko’ina cikin kwarin! Ku gudu zuwa cikin duwatsu, don kada a hallaka ku!”
ויאמר לוט אלהם אל נא אדני | 18 |
Amma Lot ya ce musu, “A’a, ranka yă daɗe, ka yi haƙuri!
הנה נא מצא עבדך חן בעיניך ותגדל חסדך אשר עשית עמדי להחיות את נפשי ואנכי לא אוכל להמלט ההרה--פן תדבקני הרעה ומתי | 19 |
Bawanku ya riga ya sami tagomashi daga gare ku, kun kuma nuna mini alheri mai yawa. Ba zan iya in gudu zuwa duwatsu ba, wannan masifa za tă same ni, zan kuma mutu.
הנה נא העיר הזאת קרבה לנוס שמה--והוא מצער אמלטה נא שמה הלא מצער הוא--ותחי נפשי | 20 |
Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”
ויאמר אליו--הנה נשאתי פניך גם לדבר הזה לבלתי הפכי את העיר אשר דברת | 21 |
Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba.
מהר המלט שמה כי לא אוכל לעשות דבר עד באך שמה על כן קרא שם העיר צוער | 22 |
Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa can.” (Domin haka ne ake kira garin Zowar.)
השמש יצא על הארץ ולוט בא צערה | 23 |
A lokacin da Lot ya isa Zowar, rana ta hau.
ויהוה המטיר על סדם ועל עמרה--גפרית ואש מאת יהוה מן השמים | 24 |
Sai Ubangiji ya yi ta zuba kibiritu a bisa Sodom da Gomorra daga sama.
ויהפך את הערים האל ואת כל הככר ואת כל ישבי הערים וצמח האדמה | 25 |
Haka ya hallakar da waɗannan birane da kuma kwarinsu gaba ɗaya, haɗe da dukan waɗanda suke zama a biranen, da kuma dukan shuke-shuke da suke cikin ƙasar.
ותבט אשתו מאחריו ותהי נציב מלח | 26 |
Amma matar Lot ta waiwaya baya, ta kuma zama ginshiƙin gishiri.
וישכם אברהם בבקר אל המקום--אשר עמד שם את פני יהוה | 27 |
Da sassafe kashegari, Ibrahim ya tashi ya koma wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji.
וישקף על פני סדם ועמרה ועל כל פני ארץ הככר וירא והנה עלה קיטר הארץ כקיטר הכבשן | 28 |
Ya duba ta wajen Sodom da Gomorra, da wajen dukan filayen ƙasar, sai ya ga hayaƙi baƙin ƙirin yana tashi daga ƙasar kamar hayaƙi daga matoya.
ויהי בשחת אלהים את ערי הככר ויזכר אלהים את אברהם וישלח את לוט מתוך ההפכה בהפך את הערים אשר ישב בהן לוט | 29 |
Saboda haka sa’ad da Allah ya hallaka waɗannan biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya kuma fitar da Lot daga masifar da ta hallaka biranen da Lot ya zauna.
ויעל לוט מצוער וישב בהר ושתי בנתיו עמו כי ירא לשבת בצוער וישב במערה--הוא ושתי בנתיו | 30 |
Lot da’ya’yansa biyu mata suka bar Zowar suka kuma zauna a cikin duwatsu, gama ya ji tsoro yă zauna a Zowar. Shi da’ya’yansa biyu mata suka zauna a ciki wani kogo.
ותאמר הבכירה אל הצעירה אבינו זקן ואיש אין בארץ לבוא עלינו כדרך כל הארץ | 31 |
Wata rana’yarsa babba ta ce wa ƙanuwarta, “Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wani mutum kusa a nan da zai yi mana ciki mu haifi’ya’ya; yadda al’ada take a ko’ina a duniya.
לכה נשקה את אבינו יין ונשכבה עמו ונחיה מאבינו זרע | 32 |
Bari mu sa mahaifinmu yă sha ruwan inabi, sa’an nan sai mu kwana da shi, don kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”
ותשקין את אביהן יין בלילה הוא ותבא הבכירה ותשכב את אביה ולא ידע בשכבה ובקומה | 33 |
A wannan dare, suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi,’yar farin ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba.
ויהי ממחרת ותאמר הבכירה אל הצעירה הן שכבתי אמש את אבי נשקנו יין גם הלילה ובאי שכבי עמו ונחיה מאבינו זרע | 34 |
Kashegari,’yar farin ta ce wa ƙanuwar, “Jiya da dare na kwana da mahaifina. Bari mu sa yă sha ruwan inabi kuma yau da dare, ke ma ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”
ותשקין גם בלילה ההוא את אביהן--יין ותקם הצעירה ותשכב עמו ולא ידע בשכבה ובקמה | 35 |
Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, a wannan dare ma, ƙanuwar ta shiga ta kwana da shi. Bai kuwa san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba.
ותהרין שתי בנות לוט מאביהן | 36 |
Ta haka’ya’yan Lot biyu mata duk suka yi ciki daga mahaifinsu.
ותלד הבכירה בן ותקרא שמו מואב הוא אבי מואב עד היום | 37 |
’Yar farin ta haifi ɗa, ta kuma ba shi suna Mowab, shi ne mahaifin Mowabawa a yau.
והצעירה גם הוא ילדה בן ותקרא שמו בן עמי הוא אבי בני עמון עד היום | 38 |
’Yar ƙaramar ma ta haifi ɗa, ta kuwa ba shi suna Ben-Ammi, shi ne mahaifin Ammonawa a yau.