< בראשית 13 >

ויעל אברם ממצרים הוא ואשתו וכל אשר לו ולוט עמו--הנגבה 1
Saboda haka Abram ya haura daga Masar zuwa Negeb tare da matarsa, da dukan abin da yake da shi tare da Lot.
ואברם כבד מאד במקנה בכסף ובזהב 2
Abram ya azurta ƙwarai da dabbobi, da azurfa, da kuma zinariya.
וילך למסעיו מנגב ועד בית אל--עד המקום אשר היה שם אהלה בתחלה בין בית אל ובין העי 3
Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari
אל מקום המזבח אשר עשה שם בראשנה ויקרא שם אברם בשם יהוה 4
da kuma inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
וגם ללוט--ההלך את אברם היה צאן ובקר ואהלים 5
Lot wanda yake tafiya tare da Abram, shi ma yana da garken shanu da tumaki da kuma tentuna.
ולא נשא אתם הארץ לשבת יחדו כי היה רכושם רב ולא יכלו לשבת יחדו 6
Wannan ya sa har ƙasar ba tă ishe su yayinda suke zama tare ba, saboda mallakarsu ta yi yawa har ba za su iya zama tare ba.
ויהי ריב בין רעי מקנה אברם ובין רעי מקנה לוט והכנעני והפרזי אז ישב בארץ 7
Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne.
ויאמר אברם אל לוט אל נא תהי מריבה ביני ובינך ובין רעי ובין רעיך כי אנשים אחים אנחנו 8
Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu’yan’uwa ne.
הלא כל הארץ לפניך הפרד נא מעלי אם השמאל ואימנה ואם הימין ואשמאילה 9
Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.”
וישא לוט את עיניו וירא את כל ככר הירדן כי כלה משקה--לפני שחת יהוה את סדם ואת עמרה כגן יהוה כארץ מצרים באכה צער 10
Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)
ויבחר לו לוט את כל ככר הירדן ויסע לוט מקדם ויפרדו איש מעל אחיו 11
Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna.
אברם ישב בארץ כנען ולוט ישב בערי הככר ויאהל עד סדם 12
Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom.
ואנשי סדם רעים וחטאים ליהוה מאד 13
Mutanen Sodom kuwa mugaye ne, sun aikata zunubi ƙwarai ga Ubangiji.
ויהוה אמר אל אברם אחרי הפרד לוט מעמו שא נא עיניך וראה מן המקום אשר אתה שם--צפנה ונגבה וקדמה וימה 14
Bayan Lot ya rabu da Abram, sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ɗaga idanunka daga inda kake, ka dubi arewa da kudu, gabas da yamma.
כי את כל הארץ אשר אתה ראה לך אתננה ולזרעך עד עולם 15
Dukan ƙasar da kake gani zan ba ka, kai da zuriyarka har abada.
ושמתי את זרעך כעפר הארץ אשר אם יוכל איש למנות את עפר הארץ--גם זרעך ימנה 16
Zan sa zuriyarka tă yi yawa kamar ƙurar ƙasa, har in wani yana iya ƙidaya ƙurar, to, za a iya ƙidaya zuriyarka.
קום התהלך בארץ לארכה ולרחבה כי לך אתננה 17
Tafi, ka ratsa tsawo da fāɗin ƙasar, gama zan ba ka ita.”
ויאהל אברם ויבא וישב באלני ממרא--אשר בחברון ויבן שם מזבח ליהוה 18
Saboda haka Abram ya cire tentunansa, ya zo ya zauna kusa da manyan itatuwan Mamre a Hebron, inda ya gina bagade ga Ubangiji.

< בראשית 13 >