< יחזקאל 7 >

ויהי דבר יהוה אלי לאמר 1
Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,
ואתה בן אדם כה אמר אדני יהוה לאדמת ישראל--קץ בא הקץ על ארבעת (ארבע) כנפות הארץ 2
“Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila, “‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar.
עתה הקץ עליך ושלחתי אפי בך ושפטתיך כדרכיך ונתתי עליך את כל תועבותיך 3
Ƙarshe yanzu yana a kanki. Zan fashe fushina a kanki. Zan shari’anta ki bisa ga halinki in sāka miki kuma saboda dukan ayyukan banƙyamar da kika yi.
ולא תחוס עיני עליך ולא אחמול כי דרכיך עליך אתן ותועבותיך בתוכך תהיין וידעתם כי אני יהוה 4
Ba zan dube ki da tausayi; ko in ƙyale ki ba. Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji.’
כה אמר אדני יהוה רעה אחת רעה הנה באה 5
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba tana zuwa.
קץ בא בא הקץ הקיץ אליך הנה באה 6
Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo! Ya farka a kanki. Ga shi, ya zo!
באה הצפירה אליך יושב הארץ בא העת קרוב היום מהומה--ולא הד הרים 7
Ƙaddara ta auko miki, ya ke wadda ke zama cikin ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato; akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu.
עתה מקרוב אשפוך חמתי עליך וכליתי אפי בך ושפטתיך כדרכיך ונתתי עליך את כל תועבותיך 8
Ina gab da fasa hasalata a kanki in kuma aukar da fushina a kanki; zan shari’anta ke bisa ga halinki in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama.
ולא תחוס עיני ולא אחמול כדרכיך עליך אתן ותועבותיך בתוכך תהיין וידעתם כי אני יהוה מכה 9
Ba zan dube ki da tausayi ko in ƙyale ke ba; zan sāka miki bisa ga halinki da kuma ayyukan masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji wanda yake bugunki.
הנה היום הנה באה יצאה הצפרה--צץ המטה פרח הזדון 10
“‘Ga shi ranar ta zo! Ta iso! Ƙaddararki ta keto, sandar ta yi toho, girman kai ya yi fure!
החמס קם למטה רשע לא מהם ולא מהמונם ולא מהמהם--ולא נה בהם 11
Rikici ya yi girma ya zama sandar da za a hukunta mugunta; babu wani daga cikin mutanen da za a bari, babu wani dukiyarsu da za a bari, babu wani abin amfani.
בא העת הגיע היום--הקונה אל ישמח והמכר אל יתאבל כי חרון אל כל המונה 12
Lokaci ya yi! Ranar ta gabato! Kada mai saya ya yi farin ciki ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama hasala tana a kan dukan jama’a.
כי המכר אל הממכר לא ישוב ועוד בחיים חיתם כי חזון אל כל המונה לא ישוב ואיש בעונו חיתו לא יתחזקו 13
Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba. Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa.
תקעו בתקוע והכין הכל ואין הלך למלחמה כי חרוני אל כל המונה 14
“‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome, ba wanda zai tafi yaƙi, gama hasalata tana a kan dukan jama’a.
החרב בחוץ והדבר והרעב מבית אשר בשדה בחרב ימות ואשר בעיר רעב ודבר יאכלנו 15
A waje takobi ne, a ciki annoba ne da yunwa; waɗanda suke fili za su mutu ta wurin takobi, waɗanda kuma suke cikin birni yunwa da annoba za su cinye su.
ופלטו פליטיהם והיו אל ההרים כיוני הגאיות כלם המות--איש בעונו 16
Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu, suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka, kowanne saboda zunubansa.
כל הידים תרפינה וכל ברכים תלכנה מים 17
Kowane hannu zai raunana, kowace gwiwa kuma za tă zama marar ƙarfi kamar ruwa.
וחגרו שקים וכסתה אותם פלצות ואל כל פנים בושה ובכל ראשיהם קרחה 18
Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba. Fuskokinsu kuma za su rufu da kunya a kuma aske kawunansu.
כספם בחוצות ישליכו וזהבם לנדה יהיה--כספם וזהבם לא יוכל להצילם ביום עברת יהוה נפשם לא ישבעו ומעיהם לא ימלאו כי מכשול עונם היה 19
“‘Za su zubar da azurfarsu a tituna, zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu a ranar hasalar Ubangiji ba. Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi.
וצבי עדיו לגאון שמהו וצלמי תועבתם שקוציהם עשו בו על כן נתתיו להם לנדה 20
Sun yi fariya kyan kayan adonsu suka kuma yi amfani da su don su yi gumakansu masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa.
ונתתיו ביד הזרים לבז ולרשעי הארץ לשלל וחללוה (וחללוהו) 21
Zan ba da su duka kamar ganima ga baƙi da kuma kamar abin da aka washe ga mugayen duniya, za su kuma ƙazantar da su.
והסבותי פני מהם וחללו את צפוני ובאו בה פריצים וחללוה 22
Zan juye fuskata daga gare su, za su kuwa ƙazantar da wurina mai daraja;’yan fashi za su shiga su kuma ƙazantar da shi.
עשה הרתוק כי הארץ מלאה משפט דמים והעיר מלאה חמס 23
“‘Ka shirya sarƙoƙi, domin ƙasar ta cika da alhakin jini, birnin kuma ya cika da rikici.
והבאתי רעי גוים וירשו את בתיהם והשבתי גאון עזים ונחלו מקדשיהם 24
Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku; zan kawo ƙarshen fariyar masu ƙarfi, Wurare Masu Tsarkinsu za su ƙazantu.
קפדה בא ובקשו שלום ואין 25
Sa’ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.
הוה על הוה תבוא ושמעה אל שמועה תהיה ובקשו חזון מנביא--ותורה תאבד מכהן ועצה מזקנים 26
Masifa a kan masifa za su zo, jita-jita kuma a kan jita-jita. Za su yi ƙoƙarin samun wahayi daga annabi; koyarwar doka ta wurin firist za tă ɓace, kamar yadda shawarar dattawa za tă ɓace.
המלך יתאבל ונשיא ילבש שממה וידי עם הארץ תבהלנה מדרכם אעשה אתם ובמשפטיהם אשפטם וידעו כי אני יהוה 27
Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya, hannuwan mutanen ƙasar kuma za su yi rawa. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su bisa ga ma’auninsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’”

< יחזקאל 7 >