< יחזקאל 14 >
ויבוא אלי אנשים מזקני ישראל וישבו לפני | 1 |
Waɗansu dattawan Isra’ila suka zo wurina suka zauna a ƙasa a gabana.
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
בן אדם האנשים האלה העלו גלוליהם על לבם ומכשול עונם נתנו נכח פניהם האדרש אדרש להם | 3 |
“Ɗan mutum, waɗannan mutane sun kafa gumaka a cikin zukatansu suka sa mugayen abubuwan sa tuntuɓe a gabansu. Zan bar su, su taɓa nemi ni?
לכן דבר אותם ואמרת אליהם כה אמר אדני יהוה איש איש מבית ישראל אשר יעלה את גלוליו אל לבו ומכשול עונו ישים נכח פניו ובא אל הנביא אני יהוה נעניתי לו בה (בא)--ברב גלוליו | 4 |
Saboda haka ka yi musu magana ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da wani mutumin Isra’ila ya kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuma sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina game da babban bautar gumakarsa.
למען תפש את בית ישראל בלבם אשר נזרו מעלי בגלוליהם כלם | 5 |
Zan yi haka don in sāke ƙame zukatan mutanen Isra’ila, waɗanda duk suka yashe ni don gumakansu.’
לכן אמר אל בית ישראל כה אמר אדני יהוה שובו והשיבו מעל גלוליכם ומעל כל תועבתיכם השיבו פניכם | 6 |
“Saboda haka ka faɗa wa gidan Isra’ila cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tuba! Ku juyo daga gumakanku ku kuma furta dukan ayyukanku masu banƙyama!
כי איש איש מבית ישראל ומהגר אשר יגור בישראל וינזר מאחרי ויעל גלוליו אל לבו ומכשול עונו ישים נכח פניו ובא אל הנביא לדרש לו בי--אני יהוה נענה לו בי | 7 |
“‘Duk sa’ad da mutumin Isra’ila ko baƙo mai zama a Isra’ila ya rabu da ni ya kuma kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuna sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi don yă neme ni, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina.
ונתתי פני באיש ההוא והשמתיהו לאות ולמשלים והכרתיו מתוך עמי וידעתם כי אני יהוה | 8 |
Zan yi gāba da mutumin in kuma sa ya zama misali da kuma abin karin magana. Zan ware shi daga mutanena. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
והנביא כי יפתה ודבר דבר--אני יהוה פתיתי את הנביא ההוא ונטיתי את ידי עליו והשמדתיו מתוך עמי ישראל | 9 |
“‘In kuma aka ruɗi annabin har ya yi annabci, Ni Ubangiji na rinjayi wannan annabi, zan kuma miƙa hannuna gāba da shi in hallaka shi daga cikin mutanena Isra’ila.
ונשאו עונם כעון הדרש--כעון הנביא יהיה | 10 |
Za su ɗauki hakkin laifinsu annabin zai zama mai laifi daidai da wanda ya zo neman shawararsa.
למען לא יתעו עוד בית ישראל מאחרי ולא יטמאו עוד בכל פשעיהם והיו לי לעם ואני אהיה להם לאלהים--נאם אדני יהוה | 11 |
Sa’an nan mutanen Isra’ila ba za su ƙara kauce daga gare ni ba, ba kuwa za su ƙara ƙazantar da kansu da dukan zunubansu ba. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
ויהי דבר יהוה אלי לאמר | 12 |
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
בן אדם ארץ כי תחטא לי למעל מעל ונטיתי ידי עליה ושברתי לה מטה לחם והשלחתי בה רעב והכרתי ממנה אדם ובהמה | 13 |
“Ɗan mutum, in wata ƙasa ta yi mini zunubi ta wurin rashin aminci na kuma miƙa hannuna gāba da ita don in toshe hanyar samun abincinta na kuma aika da yunwa a kanta na kashe mutanenta da dabbobinta,
והיו שלשת האנשים האלה בתוכה--נח דנאל (דניאל) ואיוב המה בצדקתם ינצלו נפשם נאם אדני יהוה | 14 |
ko da waɗannan mutum uku Nuhu, Daniyel da kuma Ayuba suna a cikinta, za su iya ceton kansu ne kawai ta wurin adalcinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
לו חיה רעה אעביר בארץ ושכלתה והיתה שממה מבלי עובר מפני החיה | 15 |
“Ko kuwa in na aika da namun jeji su ratsa cikin wannan ƙasa suka kuma bar ta babu yaro, ta kuma zama kufai har babu wanda zai ratsa cikinta saboda namun jeji,
שלשת האנשים האלה בתוכה--חי אני נאם אדני יהוה אם בנים ואם בנות יצילו המה לבדם ינצלו והארץ תהיה שממה | 16 |
muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da ma waɗannan mutum uku suna a cikinta, ba za su iya ceton’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto, amma ƙasar za tă zama kufai.
או חרב אביא על הארץ ההיא ואמרתי חרב תעבר בארץ והכרתי ממנה אדם ובהמה | 17 |
“Ko kuma in na kawo takobi a kan wannan ƙasa na kuma ce, ‘Bari takobin ya ratsa cikin dukan ƙasar,’ na kuma kashe mutanenta da dabbobinsu,
ושלשת האנשים האלה בתוכה--חי אני נאם אדני יהוה לא יצילו בנים ובנות כי הם לבדם ינצלו | 18 |
muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da waɗannan mutum uku suna cikinta, ba za su iya ceton’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto.
או דבר אשלח אל הארץ ההיא ושפכתי חמתי עליה בדם להכרית ממנה אדם ובהמה | 19 |
“Ko kuma in na aika da annoba a cikin wannan ƙasa na kuma yi fushi a kanta ta wurin kisa, ina kisan mutanenta da dabbobinsu,
ונח דנאל (דניאל) ואיוב בתוכה--חי אני נאם אדני יהוה אם בן אם בת יצילו המה בצדקתם יצילו נפשם | 20 |
muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da Nuhu, Daniyel da Ayuba suna a cikinta, ba za su iya ceton ɗansu ko’yarsu ba. Za su iya ceton kansu ne kaɗai ta wurin adalcinsu.
כי כה אמר אדני יהוה אף כי ארבעת שפטי הרעים חרב ורעב וחיה רעה ודבר שלחתי אל ירושלם--להכרית ממנה אדם ובהמה | 21 |
“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa balle fa sa’ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi takobi da yunwa da namun jeji da annoba don su kashe mutanenta da dabbobinsu!
והנה נותרה בה פלטה המוצאים בנים ובנות--הנם יוצאים אליכם וראיתם את דרכם ואת עלילותם ונחמתם על הרעה אשר הבאתי על ירושלם--את כל אשר הבאתי עליה | 22 |
Duk da haka za a sami mutanen da za su ragu’ya’ya maza da matan da za a fitar daga cikinta. Za su zo wurinka, kuma sa’ad da ka gan halinsu da ayyukansu, za ka ta’azantu game da bala’in da na kawo a kan Urushalima kowane bala’in da na kawo a kanta.
ונחמו אתכם כי תראו את דרכם ואת עלילותם וידעתם כי לא חנם עשיתי את כל אשר עשיתי בה--נאם אדני יהוה | 23 |
Za ka ta’azantu sa’ad da ka ga halinsu da kuma ayyukansu, gama za ka san cewa ban aikata wani abu a cikinta ba dalili ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”