< שמות 10 >

ויאמר יהוה אל משה בא אל פרעה כי אני הכבדתי את לבו ואת לב עבדיו למען שתי אתתי אלה בקרבו 1
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,
ולמען תספר באזני בנך ובן בנך את אשר התעללתי במצרים ואת אתתי אשר שמתי בם וידעתם כי אני יהוה 2
don kuma ku gaya wa’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”
ויבא משה ואהרן אל פרעה ויאמרו אליו כה אמר יהוה אלהי העברים עד מתי מאנת לענת מפני שלח עמי ויעבדני 3
Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.
כי אם מאן אתה לשלח את עמי--הנני מביא מחר ארבה בגבלך 4
In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka.
וכסה את עין הארץ ולא יוכל לראת את הארץ ואכל את יתר הפלטה הנשארת לכם מן הברד ואכל את כל העץ הצמח לכם מן השדה 5
Za su rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za su cinye ɗan sauran abin da ya rage muku daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a gonakinku.
ומלאו בתיך ובתי כל עבדיך ובתי כל מצרים אשר לא ראו אבתיך ואבות אבתיך מיום היותם על האדמה עד היום הזה ויפן ויצא מעם פרעה 6
Za su cika gidajenka, da na fadawanka, da na dukan Masarawa, abin da iyayenka da kakanninka ba su taɓa gani ba, tun daga ranar da suka sami kansu a duniya, har yă zuwa yau.’” Sa’an nan Musa ya juya, ya rabu da Fir’auna.
ויאמרו עבדי פרעה אליו עד מתי יהיה זה לנו למוקש--שלח את האנשים ויעבדו את יהוה אלהיהם הטרם תדע כי אבדה מצרים 7
Fadawan Fir’auna suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai zama mana tarko? Ka bar mutanen su tafi domin su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Har yanzu ba ka san cewa Masar ta lalace ba?”
ויושב את משה ואת אהרן אל פרעה ויאמר אלהם לכו עבדו את יהוה אלהיכם מי ומי ההלכים 8
Sa’an nan aka dawo da Musa da Haruna wurin Fir’auna. Sai ya ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”
ויאמר משה בנערינו ובזקנינו נלך בבנינו ובבנותנו בצאננו ובבקרנו נלך--כי חג יהוה לנו 9
Musa ya amsa, “Za mu tafi tare da ƙanananmu, da tsofaffinmu, da’ya’yanmu maza da mata, da kuma garkunanmu na shanu da tumaki, gama dole ne mu yi bikin ga Ubangiji.”
ויאמר אלהם יהי כן יהוה עמכם כאשר אשלח אתכם ואת טפכם ראו כי רעה נגד פניכם 10
Fir’auna ya ce, “Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba! A fili yake kuna da niyyar mugunta.
לא כן לכו נא הגברים ועבדו את יהוה--כי אתה אתם מבקשים ויגרש אתם מאת פני פרעה 11
Sam! Wannan ba zai taɓa yiwu ba, sai ko maza kaɗai su tafi su yi wa Ubangiji sujada, gama abin da kuke so ke nan.” Sa’an nan aka kori Musa da Haruna daga gaban Fir’auna.
ויאמר יהוה אל משה נטה ידך על ארץ מצרים בארבה ויעל על ארץ מצרים ויאכל את כל עשב הארץ את כל אשר השאיר הברד 12
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka a bisa Masar domin fāra su sauko bisa ƙasar, su ci duk abin da yake girma a gonaki, duk abin da ƙanƙara ta rage.”
ויט משה את מטהו על ארץ מצרים ויהוה נהג רוח קדים בארץ כל היום ההוא וכל הלילה הבקר היה--ורוח הקדים נשא את הארבה 13
Saboda haka Musa ya miƙa sandansa bisa Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a kan ƙasar dukan dare da kuma dukan yini. Da safe kuwa iskar ta kawo fāra;
ויעל הארבה על כל ארץ מצרים וינח בכל גבול מצרים כבד מאד--לפניו לא היה כן ארבה כמהו ואחריו לא יהיה כן 14
suka mamaye ƙasar duka, suka sauka a ko’ina a ƙasar. Ba a taɓa ganin annobar fāra haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin fāra kamar haka ba.
ויכס את עין כל הארץ ותחשך הארץ ויאכל את כל עשב הארץ ואת כל פרי העץ אשר הותיר הברד ולא נותר כל ירק בעץ ובעשב השדה בכל ארץ מצרים 15
Suka rufe ƙasar har ta zama baƙi. Suka cinye abin da ƙanƙara ta rage, kowane tsiron da yake girma a gonaki, da dukan’ya’yan itatuwa. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.
וימהר פרעה לקרא למשה ולאהרן ויאמר חטאתי ליהוה אלהיכם--ולכם 16
Fir’auna ya kira Musa da Haruna da gaggawa ya ce, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.
ועתה שא נא חטאתי אך הפעם והעתירו ליהוה אלהיכם ויסר מעלי רק את המות הזה 17
Yanzu ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yă ɗauke wannan muguwar annoba daga gare ni.”
ויצא מעם פרעה ויעתר אל יהוה 18
Sai Musa ya bar Fir’auna ya kuma yi addu’a ga Ubangiji.
ויהפך יהוה רוח ים חזק מאד וישא את הארבה ויתקעהו ימה סוף לא נשאר ארבה אחד בכל גבול מצרים 19
Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar.
ויחזק יהוה את לב פרעה ולא שלח את בני ישראל 20
Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba.
ויאמר יהוה אל משה נטה ידך על השמים ויהי חשך על ארץ מצרים וימש חשך 21
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama domin a yi duhu a bisa Masar, duhun da za a iya taɓawa.”
ויט משה את ידו על השמים ויהי חשך אפלה בכל ארץ מצרים שלשת ימים 22
Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuma yi duhu baƙi ƙirin bisa dukan ƙasar Masar na kwana uku.
לא ראו איש את אחיו ולא קמו איש מתחתיו--שלשת ימים ולכל בני ישראל היה אור במושבתם 23
Ba wanda ya iya gani wani ko yă bar wurinsa na kwana uku. Amma dukan Isra’ilawa sun kasance da haske a inda suke zama.
ויקרא פרעה אל משה ויאמר לכו עבדו את יהוה--רק צאנכם ובקרכם יצג גם טפכם ילך עמכם 24
Sai Fir’auna ya aika aka kira Musa, ya kuma ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji sujada. Matanku da yaranku ma za su iya tafiya tare da ku; sai dai ku bar garkunanku na shanu da tumaki.”
ויאמר משה גם אתה תתן בידנו זבחים ועלת ועשינו ליהוה אלהינו 25
Amma Musa ya ce, “Dole ka bari mu kasance da hadayu, da kuma hadayu na ƙonawa waɗanda za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu.
וגם מקננו ילך עמנו לא תשאר פרסה--כי ממנו נקח לעבד את יהוה אלהינו ואנחנו לא נדע מה נעבד את יהוה עד באנו שמה 26
Dole dabbobinmu ma su tafi tare da mu; ko kofato ma, ba za a bari a baya ba. A cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu yi wa Ubangiji Allahnmu sujada. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.”
ויחזק יהוה את לב פרעה ולא אבה לשלחם 27
Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, har bai yarda yă sake su ba.
ויאמר לו פרעה לך מעלי השמר לך אל תסף ראות פני--כי ביום ראתך פני תמות 28
Fir’auna ya ce wa Musa, “Fita, ka ba ni wuri! Ka mai da hankali, kada ka ƙara bayyana a gabana, gama ran da ka sāke ganin fuskata, a ran nan za ka mutu.”
ויאמר משה כן דברת לא אסף עוד ראות פניך 29
Musa ya amsa, “Madalla, kamar yadda ka faɗa, ba zan ƙara bayyana a gabanka ba.”

< שמות 10 >