< דברים 34 >
ויעל משה מערבת מואב אל הר נבו ראש הפסגה אשר על פני ירחו ויראהו יהוה את כל הארץ את הגלעד עד דן | 1 |
Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan,
ואת כל נפתלי ואת ארץ אפרים ומנשה ואת כל ארץ יהודה עד הים האחרון | 2 |
da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum,
ואת הנגב ואת הככר בקעת ירחו עיר התמרים--עד צער | 3 |
da Negeb da dukan yankin Kwarin Yeriko, Birnin Dabino, har zuwa Zowar.
ויאמר יהוה אליו זאת הארץ אשר נשבעתי לאברהם ליצחק וליעקב לאמר לזרעך אתננה הראיתיך בעיניך ושמה לא תעבר | 4 |
Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.”
וימת שם משה עבד יהוה בארץ מואב--על פי יהוה | 5 |
Nan fa, a ƙasar Mowab Musa bawan Ubangiji ya mutu, yadda Ubangiji ya faɗa.
ויקבר אתו בגי בארץ מואב מול בית פעור ולא ידע איש את קברתו עד היום הזה | 6 |
Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake.
ומשה בן מאה ועשרים שנה--במתו לא כהתה עינו ולא נס לחה | 7 |
Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba.
ויבכו בני ישראל את משה בערבת מואב שלשים יום ויתמו ימי בכי אבל משה | 8 |
Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab kwana talatin, sai da lokacin kuka, da na makoki suka ƙare.
ויהושע בן נון מלא רוח חכמה--כי סמך משה את ידיו עליו וישמעו אליו בני ישראל ויעשו כאשר צוה יהוה את משה | 9 |
To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa.
ולא קם נביא עוד בישראל כמשה אשר ידעו יהוה פנים אל פנים | 10 |
Tun daga nan ba a sāke yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska,
לכל האתת והמופתים אשר שלחו יהוה לעשות בארץ מצרים--לפרעה ולכל עבדיו ולכל ארצו | 11 |
wanda kuma ya yi dukan waɗannan alamu banmamaki da al’ajaban da Ubangiji ya aike shi yă yi a Masar, da a kan Fir’auna, da a kan dukan shugabanninsa, da kuma a kan dukan ƙasarsa.
ולכל היד החזקה ולכל המורא הגדול אשר עשה משה לעיני כל ישראל | 12 |
Gama babu wani wanda ya taɓa nuna iko mai ƙarfi, ko yă aikata ayyukan banrazana waɗanda Musa ya yi a gaban dukan Isra’ila.