< דברים 12 >
אלה החקים והמשפטים אשר תשמרון לעשות בארץ אשר נתן יהוה אלהי אבתיך לך לרשתה כל הימים--אשר אתם חיים על האדמה | 1 |
Waɗannan su ne ƙa’idodi da kuma dokokin da za ku lura, ku kuma kiyaye a ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku, yake ba ku don ku ci gādonta, muddin kuna zama a ƙasar.
אבד תאבדון את כל המקמות אשר עבדו שם הגוים אשר אתם ירשים אתם--את אלהיהם על ההרים הרמים ועל הגבעות ותחת כל עץ רענן | 2 |
Ku hallaka dukan wuraren da al’umman da kuke kora suke yi wa allolinsu sujada, a kan duwatsu masu tsawo, da a kan tuddai, da kuma ƙarƙashin kowane itace gaba ɗaya.
ונתצתם את מזבחתם ושברתם את מצבתם ואשריהם תשרפון באש ופסילי אלהיהם תגדעון ואבדתם את שמם מן המקום ההוא | 3 |
Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku kuma ƙone ginshiƙan Asheransu da wuta; ku yayyanka gumakan allolinsu, ku kuma shafe sunayensu daga waɗannan wurare.
לא תעשון כן ליהוה אלהיכם | 4 |
Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba.
כי אם אל המקום אשר יבחר יהוה אלהיכם מכל שבטיכם לשום את שמו שם--לשכנו תדרשו ובאת שמה | 5 |
Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin dukan kabilanku, inda zai sa Sunansa, yă mai wurin mazauninsa. A wannan wuri ne za ku tafi;
והבאתם שמה עלתיכם וזבחיכם ואת מעשרתיכם ואת תרומת ידכם ונדריכם ונדבתיכם ובכרת בקרכם וצאנכם | 6 |
a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki.
ואכלתם שם לפני יהוה אלהיכם ושמחתם בכל משלח ידכם אתם ובתיכם--אשר ברכך יהוה אלהיך | 7 |
A can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku da iyalanku za su ci, su kuma yi farin ciki a kome da kuka sa hannunku a kai, domin Ubangiji Allahnku zai albarkace ku.
לא תעשון--ככל אשר אנחנו עשים פה היום איש כל הישר בעיניו | 8 |
Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama.
כי לא באתם עד עתה--אל המנוחה ואל הנחלה אשר יהוה אלהיך נתן לך | 9 |
Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.
ועברתם את הירדן וישבתם בארץ אשר יהוה אלהיכם מנחיל אתכם והניח לכם מכל איביכם מסביב וישבתם בטח | 10 |
Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, zai kuwa ba ku hutu daga dukan abokan gābanku da suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya,
והיה המקום אשר יבחר יהוה אלהיכם בו לשכן שמו שם--שמה תביאו את כל אשר אנכי מצוה אתכם עולתיכם וזבחיכם מעשרתיכם ותרמת ידכם וכל מבחר נדריכם אשר תדרו ליהוה | 11 |
sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa.
ושמחתם לפני יהוה אלהיכם--אתם ובניכם ובנתיכם ועבדיכם ואמהתיכם והלוי אשר בשעריכם כי אין לו חלק ונחלה אתכם | 12 |
A can kuma za ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, ku da’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, waɗanda ba a ba su rabo ba, ba su kuma da gādo na kansu.
השמר לך פן תעלה עלתיך בכל מקום אשר תראה | 13 |
Ku kula fa kada ku miƙa hadayun ƙonawa a wani wurin da kuka ga dama.
כי אם במקום אשר יבחר יהוה באחד שבטיך--שם תעלה עלתיך ושם תעשה כל אשר אנכי מצוך | 14 |
Ku miƙa su kawai a wurin da Ubangiji zai zaɓa a cikin ɗaya daga kabilanku, a can za ku yi kowane abin da na umarce ku.
רק בכל אות נפשך תזבח ואכלת בשר כברכת יהוה אלהיך אשר נתן לך--בכל שעריך הטמא והטהור יאכלנו כצבי וכאיל | 15 |
Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci.
רק הדם לא תאכלו על הארץ תשפכנו כמים | 16 |
Amma kada ku ci jini, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
לא תוכל לאכל בשעריך מעשר דגנך ותירשך ויצהרך ובכרת בקרך וצאנך וכל נדריך אשר תדר ונדבתיך ותרומת ידך | 17 |
Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman.
כי אם לפני יהוה אלהיך תאכלנו במקום אשר יבחר יהוה אלהיך בו--אתה ובנך ובתך ועבדך ואמתך והלוי אשר בשעריך ושמחת לפני יהוה אלהיך בכל משלח ידך | 18 |
A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku.
השמר לך פן תעזב את הלוי כל ימיך על אדמתך | 19 |
Ku yi hankali, kada ku manta da Lawiyawa, muddin kuna zaune a ƙasarku.
כי ירחיב יהוה אלהיך את גבלך כאשר דבר לך ואמרת אכלה בשר כי תאוה נפשך לאכל בשר--בכל אות נפשך תאכל בשר | 20 |
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fadada iyakarku kamar yadda ya yi muku alkawari, kuka kuma ji marmarin nama, kuka kuma ce, “Muna so mu ci nama,” to, za ku iya cin yadda kuke so.
כי ירחק ממך המקום אשר יבחר יהוה אלהיך לשום שמו שם וזבחת מבקרך ומצאנך אשר נתן יהוה לך כאשר צויתך--ואכלת בשעריך בכל אות נפשך | 21 |
In wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don yă sa Sunansa yana da nisa sosai daga inda kuke, za ku iya yankan dabbobi daga garkunanku na shanu da na tumakin da Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku, a cikin biranenku kuma za ku iya ci, yadda kuke so.
אך כאשר יאכל את הצבי ואת האיל--כן תאכלנו הטמא והטהור יחדו יאכלנו | 22 |
Ku ci su yadda akan ci barewa ko mariri. Marar tsarki da mai tsarki, za ku iya ci.
רק חזק לבלתי אכל הדם כי הדם הוא הנפש ולא תאכל הנפש עם הבשר | 23 |
Amma ku tabbata ba ku ci jinin ba, domin jini ne rai, ba kuwa za ku ci rai cikin naman ba.
לא תאכלנו על הארץ תשפכנו כמים | 24 |
Ba za ku ci jini ba, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
לא תאכלנו--למען ייטב לך ולבניך אחריך כי תעשה הישר בעיני יהוה | 25 |
Kada ku ci shi, don ku zauna lafiya, da ku da’ya’yanku bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
רק קדשיך אשר יהיו לך ונדריך תשא ובאת אל המקום אשר יבחר יהוה | 26 |
Amma ku ɗauki abubuwa masu tsarki, da kuma duk abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ku tafi inda Ubangiji ya zaɓa.
ועשית עלתיך הבשר והדם על מזבח יהוה אלהיך ודם זבחיך ישפך על מזבח יהוה אלהיך והבשר תאכל | 27 |
Ku miƙa hadayunku na ƙonawa a bagaden Ubangiji Allahnku, da naman da kuma jinin. Dole a zub da jinin hadayunku a gindin bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku iya cin naman.
שמר ושמעת את כל הדברים האלה אשר אנכי מצוך למען ייטב לך ולבניך אחריך עד עולם--כי תעשה הטוב והישר בעיני יהוה אלהיך | 28 |
Ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan waɗannan umarnan da nake ba ku, da kuma’ya’yanku, don ku zauna lafiya, da ku da’ya’yanku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai da kuma yake mai kyau a gaban Ubangiji Allahnku.
כי יכרית יהוה אלהיך את הגוים אשר אתה בא שמה לרשת אותם--מפניך וירשת אתם וישבת בארצם | 29 |
Ubangiji Allahnku zai kawar muku da al’umman nan da kuke niyyar shiga cikin ƙasarsu don ku kore su, bayan kuka kore su, kuka kuma zauna a ƙasarsu,
השמר לך פן תנקש אחריהם אחרי השמדם מפניך ופן תדרש לאלהיהם לאמר איכה יעבדו הגוים האלה את אלהיהם ואעשה כן גם אני | 30 |
to, sai ku lura, kada ku jarrabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku, kada ku tambayi kome game da allolinsu, kuna cewa, “Yaya waɗannan al’ummai suke bauta wa allolinsu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.”
לא תעשה כן ליהוה אלהיך כי כל תועבת יהוה אשר שנא עשו לאלהיהם--כי גם את בניהם ואת בנתיהם ישרפו באש לאלהיהם | 31 |
Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba, gama a cikin yin sujada wa allolinsu, sun yi dukan abubuwan banƙyaman da Ubangiji yake ƙi. Har ma sukan ƙone’ya’yansu maza da mata a wuta a matsayin hadayu.
את כל הדבר אשר אנכי מצוה אתכם--אתו תשמרו לעשות לא תסף עליו ולא תגרע ממנו | 32 |
Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku; kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin.