< שמואל ב 15 >
ויהי מאחרי כן ויעש לו אבשלום מרכבה וססים וחמשים איש רצים לפניו | 1 |
Ana nan sai Absalom ya samo wa kansa wata keken yaƙi da dawakai tare da mutum hamsin da za su sha gabansa.
והשכים אבשלום ועמד על יד דרך השער ויהי כל האיש אשר יהיה לו ריב לבוא אל המלך למשפט ויקרא אבשלום אליו ויאמר אי מזה עיר אתה ויאמר מאחד שבטי ישראל עבדך | 2 |
Absalom yakan tashi da sassafe yă tsaya a gefen hanyar shigar ƙofar birni. Duk sa’ad da wani ya zo da ƙara don a kai gaban sarki yă yi shari’a, Absalom yakan kira shi yă ce, “Daga wane gari ka fito?” Sai mutumin yă amsa yă ce, “Bawanka ya fito a ɗaya daga cikin kabilan Isra’ila.”
ויאמר אליו אבשלום ראה דבריך טובים ונכחים ושמע אין לך מאת המלך | 3 |
Sai Absalom yă ce masa, “Ga shi, ƙararka daidai ne, tana kuma da gaskiya, sai dai ba wakilin sarkin da zai ji ka.”
ויאמר אבשלום מי ישמני שפט בארץ ועלי יבוא כל איש אשר יהיה לו ריב ומשפט--והצדקתיו | 4 |
Absalom kuwa yakan ƙara da cewa, “Da a ce an naɗa ni alƙali a ƙasar mana! Da duk mai ƙara, ko kuka wanda zai zo wurina, zan in tabbatar an yi masa adalci.”
והיה בקרב איש להשתחות לו ושלח את ידו והחזיק לו ונשק לו | 5 |
Kuma duk sa’ad da wani ya zo wurin Absalom ya rusuna don yă gaishe shi, sai Absalom yă sa hannunsa yă ta da shi, yă kuma rungume shi.
ויעש אבשלום כדבר הזה לכל ישראל אשר יבאו למשפט אל המלך ויגנב אבשלום את לב אנשי ישראל | 6 |
Absalom ya yi ta yin haka ga dukan Isra’ilawan da suka zo wurin sarki don neman adalci, ta haka kuwa ya saci zukatan mutanen Isra’ila.
ויהי מקץ ארבעים שנה ויאמר אבשלום אל המלך אלכה נא ואשלם את נדרי אשר נדרתי ליהוה בחברון | 7 |
A ƙarshen shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Bari in tafi Hebron in cika alkawarin da na yi wa Ubangiji.
כי נדר נדר עבדך בשבתי בגשור בארם לאמר אם ישיב (ישוב) ישיבני יהוה ירושלם ועבדתי את יהוה | 8 |
Yayinda bawanka yake zama a Geshur, a Aram, na yi wannan alkawari, na ce, ‘In Ubangiji ya komo da ni Urushalima, zan yi wa Ubangiji sujada a Hebron.’”
ויאמר לו המלך לך בשלום ויקם וילך חברונה | 9 |
Sarki ya ce, “Ka sauka lafiya.” Sai ya tafi Hebron.
וישלח אבשלום מרגלים בכל שבטי ישראל לאמר כשמעכם את קול השפר ואמרתם מלך אבשלום בחברון | 10 |
Sai Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra’ila, ya ce musu su ce, “Da zarar kuka ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom sarki ne a Hebron.’”
ואת אבשלום הלכו מאתים איש מירושלם קראים והלכים לתמם ולא ידעו כל דבר | 11 |
Mutum ɗari biyu daga Urushalima suka raka Absalom. An gayyace su a matsayin baƙi, suka kuwa tafi cikin rashin sani, ba su san wani abu game da al’amarin ba.
וישלח אבשלום את אחיתפל הגילני יועץ דוד מעירו מגלה בזבחו את הזבחים ויהי הקשר אמץ והעם הולך ורב את אבשלום | 12 |
Yayinda Absalom yake miƙa hadaya, ya aika a kira Ahitofel mutumin Gilo, mai ba wa Dawuda shawara, yă zo daga Gilo garinsa. Ta haka makircin ya ƙara ƙarfi, masu bin Absalom kuma suka yi ta ƙaruwa.
ויבא המגיד אל דוד לאמר היה לב איש ישראל אחרי אבשלום | 13 |
Wani manzo ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra’ila sun koma wajen Absalom.”
ויאמר דוד לכל עבדיו אשר אתו בירושלם קומו ונברחה--כי לא תהיה לנו פליטה מפני אבשלם מהרו ללכת פן ימהר והשגנו והדיח עלינו את הרעה והכה העיר לפי חרב | 14 |
Sai Dawuda ya ce wa dukan fadawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Ku zo! Mu gudu, in ba haka ba, babu wanda zai tsira daga hannun Absalom. Dole mu bar nan, nan da nan, in ba haka ba zai tashi da sauri yă fāɗa mana, yă kuma hallaka garin da takobi.”
ויאמרו עבדי המלך אל המלך ככל אשר יבחר אדני המלך הנה עבדיך | 15 |
Sai fadawan sarki suka ce masa, “Barorinka suna a shirye su yi duk abin da ranka yă daɗe, ya zaɓa.”
ויצא המלך וכל ביתו ברגליו ויעזב המלך את עשר נשים פלגשים--לשמר הבית | 16 |
Sarki ya kama hanya, dukan gidansa kuwa suna biye da shi; amma ya bar ƙwarƙwarai goma su lura da fada.
ויצא המלך וכל העם ברגליו ויעמדו בית המרחק | 17 |
Ta haka sarki ya kama hanya da dukan mutane suna biye da shi, suka yi sansani a wani wuri mai ɗan nisa da Urushalima.
וכל עבדיו עברים על ידו וכל הכרתי וכל הפלתי וכל הגתים שש מאות איש אשר באו ברגלו מגת עברים על פני המלך | 18 |
Dukan mutanensa suka wuce gabansa, tare da dukan Keretawa da Feletiyawa; da dukan mutane ɗari shida na Gittiyawan da suka raka shi daga Gat, suka wuce gaban sarki.
ויאמר המלך אל אתי הגתי למה תלך גם אתה אתנו שוב ושב עם המלך כי נכרי אתה וגם גלה אתה למקומך | 19 |
Sarki ya ce wa Ittai mutumin Gat, “Don me za ka zo tare da mu? Ka koma ka zauna tare da Sarki Absalom. Kai baƙo ne, ɗan gudun hijira daga garinka.
תמול בואך והיום אנועך (אניעך) עמנו ללכת ואני הולך על אשר אני הולך שוב והשב את אחיך עמך חסד ואמת | 20 |
Jiya-jiya ka zo. Yau kuma in sa ka yi ta yawo tare da mu, ga shi ban ma san inda za ni ba? Koma, ka tafi da’yan’uwanka. Bari alheri da amincin Ubangiji su kasance tare da kai.”
ויען אתי את המלך ויאמר חי יהוה וחי אדני המלך כי אם במקום אשר יהיה שם אדני המלך אם למות אם לחיים כי שם יהיה עבדך | 21 |
Amma Ittai ya ce wa sarki, “Muddin Ubangiji yana a raye kuma muddin ranka yă daɗe yana a raye, duk inda ranka yă daɗe sarki zai kasance, ko a yi rai ko a mutu, a can bawanka zai kasance.”
ויאמר דוד אל אתי לך ועבר ויעבר אתי הגתי וכל אנשיו וכל הטף אשר אתו | 22 |
Dawuda ya ce wa Ittai, “Wuce gaba, taka mu je.” Sai Ittai mutumin Gat ya shiga layi tare da dukan mutanensa da iyalan da suke tare da shi.
וכל הארץ בוכים קול גדול וכל העם עברים והמלך עבר בנחל קדרון וכל העם עברים על פני דרך את המדבר | 23 |
Dukan ƙauyuka suka yi ta kururuwa yayinda mutanen suke wucewa. Sarki shi ma ya haye ta Kwarin Kidron, mutane kuma suka ci gaba da tafiya zuwa wajen hamada.
והנה גם צדוק וכל הלוים אתו נשאים את ארון ברית האלהים ויצקו את ארון האלהים ויעל אביתר--עד תם כל העם לעבור מן העיר | 24 |
Zadok yana nan tare da su, kuma dukan Lawiyawan da suke tare da shi kuwa suna ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka sauke akwatin alkawarin Allah, Abiyatar ya miƙa hadaya sai da mutane suka gama fita daga birnin.
ויאמר המלך לצדוק השב את ארון האלהים העיר אם אמצא חן בעיני יהוה--והשבני והראני אתו ואת נוהו | 25 |
Sa’an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka komar da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a idon Ubangiji, zai dawo da ni, yă kuma sa in sāke gan shi a mazauninsa.
ואם כה יאמר לא חפצתי בך הנני--יעשה לי כאשר טוב בעיניו | 26 |
Amma in ya ce, ‘Ina baƙin ciki da kai,’ to, ina a shirye; bari yă yi abin da ya fi masa.”
ויאמר המלך אל צדוק הכהן הרואה אתה שבה העיר בשלום ואחימעץ בנך ויהונתן בן אביתר שני בניכם--אתכם | 27 |
Sarki ya kuma ce wa Zadok firist, “Ashe, kai ba mai duba ba ne? Ka koma cikin birnin lafiya, tare da ɗanka Ahimawaz, da kuma Yonatan ɗan Abiyatar. Kai da Abiyatar ku tafi da’ya’yanku biyu.
ראו אנכי מתמהמה בעברות (בערבות) המדבר--עד בוא דבר מעמכם להגיד לי | 28 |
Zan kuwa jira a mashigai a hamada, sai na ji daga gare ku.”
וישב צדוק ואביתר את ארון האלהים ירושלם וישבו שם | 29 |
Saboda haka Zadok da Abiyatar suka ɗauki akwatin alkawarin Allah suka komar da shi Urushalima, suka zauna a can.
ודוד עלה במעלה הזיתים עלה ובוכה וראש לו חפוי והוא הלך יחף וכל העם אשר אתו חפו איש ראשו ועלו עלה ובכה | 30 |
Amma Dawuda ya ci gaba yana hawan Dutsen Zaitun, yana kuka yayinda yake tafiya; kansa a rufe, kuma babu takalma a ƙafafunsa. Dukan mutanen da suke tare da shi suka rufe kawunansu suna ta kuka yayinda suke haurawa.
ודוד הגיד לאמר אחיתפל בקשרים עם אבשלום ויאמר דוד סכל נא את עצת אחיתפל יהוה | 31 |
To, an gaya wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin waɗanda suka hadasa maƙarƙashiya tare da Absalom.” Saboda haka Dawuda ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji ka mai da shawarar Ahitofel ta zama shiririta.”
ויהי דוד בא עד הראש אשר ישתחוה שם לאלהים והנה לקראתו חושי הארכי קרוע כתנתו ואדמה על ראשו | 32 |
Da Dawuda ya isa ƙwanƙoli, inda mutane sun saba yi wa Allah sujada, Hushai, mutumin Arkitawa kuwa yana can don yă tarye shi, taguwarsa a yage, ga kuma ƙura a kansa.
ויאמר לו דוד אם עברת אתי והית עלי למשא | 33 |
Sai Dawuda ya ce masa, “In ka tafi tare da ni, za ka zama mini kaya.
ואם העיר תשוב ואמרת לאבשלום עבדך אני המלך אהיה--עבד אביך ואני מאז ועתה ואני עבדך והפרתה לי את עצת אחיתפל | 34 |
Amma in ka koma birni, ka gaya wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; dā ni bawan mahaifinka ne, amma yanzu zan zama bawanka,’ ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.
והלוא עמך שם צדוק ואביתר הכהנים והיה כל הדבר אשר תשמע מבית המלך--תגיד לצדוק ולאביתר הכהנים | 35 |
Ba Zadok da Abiyatar firistocin nan suna nan tare da kai ba? Ka gaya musu duk abin da ka ji a fadan sarki.
הנה שם עמם שני בניהם--אחימעץ לצדוק ויהונתן לאביתר ושלחתם בידם אלי כל דבר אשר תשמעו | 36 |
’Ya’yansu biyu maza, Ahimawaz ɗan Zadok, da kuma Yonatan ɗan Abiyatar, suna can tare da su. Ka aike su wurina da duk abin da ka ji.”
ויבא חושי רעה דוד העיר ואבשלום יבוא ירושלם | 37 |
Saboda haka Hushai abokin Dawuda ya isa Urushalima yayinda Absalom yake shigowa birnin.