< דברי הימים ב 21 >

וישכב יהושפט עם אבתיו ויקבר עם אבתיו בעיר דויד וימלך יהורם בנו תחתיו 1
Yehoshafat ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
ולו אחים בני יהושפט עזריה ויחיאל וזכריהו ועזריהו ומיכאל ושפטיהו כל אלה בני יהושפט מלך ישראל 2
’Yan’uwan Yehoram,’ya’yan Yehoshafat maza su ne, Azariya, Yehiyel, Zakariya, Azariyahu, Mika’ilu da Shefatiya. Dukan waɗannan su ne’ya’yan Yehoshafat sarkin Isra’ila maza.
ויתן להם אביהם מתנות רבות לכסף ולזהב ולמגדנות עם ערי מצרות ביהודה ואת הממלכה נתן ליהורם כי הוא הבכור 3
Mahaifinsu ya ba su kyautai masu yawa na azurfa da zinariya da kayayyaki masu daraja, tare da birane masu katanga a Yahuda, amma ya ba da mulki ga Yehoram domin shi ne ɗan farinsa.
ויקם יהורם על ממלכת אביו ויתחזק ויהרג את כל אחיו בחרב וגם משרי ישראל 4
Sa’ad da Yehoram ya kafa kansa sosai a bisa mulkin mahaifinsa, sai ya kashe dukan’yan’uwansa da takobi tare da waɗansu sarakunan Isra’ila.
בן שלשים ושתים שנה יהורם במלכו ושמונה שנים מלך בירושלם 5
Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas.
וילך בדרך מלכי ישראל כאשר עשו בית אחאב--כי בת אחאב היתה לו אשה ויעש הרע בעיני יהוה 6
Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri’yar Ahab. Ya aikata mugayen ayyuka a idon Ubangiji.
ולא אבה יהוה להשחית את בית דויד--למען הברית אשר כרת לדויד וכאשר אמר לתת לו ניר ולבניו--כל הימים 7
Duk da haka, domin alkawarin da Ubangiji ya yi wa Dawuda, Ubangiji bai so yă hallaka gidan Dawuda ba. Ubangiji ya riga ya yi alkawari zai ci gaba da riƙe fitila domin Dawuda da zuriyarsa har abada.
בימיו פשע אדום מתחת יד יהודה וימליכו עליהם מלך 8
A zamanin Yehoram, Edom ya tayar wa Yahuda ya kuma naɗa sarkinsa.
ויעבר יהורם עם שריו וכל הרכב עמו ויהי קם לילה ויך את אדום הסובב אליו ואת שרי הרכב 9
Saboda haka Yehoram ya tafi can tare da shugabannin sojojinsa da kuma dukan keken yaƙinsa. Mutanen Edom suka kewaye shi da shugabannin keken yaƙinsa, amma ya tashi ya fatattaki su da dare.
ויפשע אדום מתחת יד יהודה עד היום הזה--אז תפשע לבנה בעת ההיא מתחת ידו כי עזב את יהוה אלהי אבתיו 10
Har yă zuwa yau Edom na tawaye a kan Yahuda. Libna ya yi tawaye a lokaci guda, domin Yehoram ya yashe Ubangiji Allah na kakanninsa.
גם הוא עשה במות בהרי יהודה ויזן את ישבי ירושלם וידח את יהודה 11
Ya gina masujadan kan tudu a tuddan Yahuda, ya kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, ya sa Yahuda suka kauce.
ויבא אליו מכתב מאליהו הנביא לאמר כה אמר יהוה אלהי דויד אביך--תחת אשר לא הלכת בדרכי יהושפט אביך ובדרכי אסא מלך יהודה 12
Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.
ותלך בדרך מלכי ישראל ותזנה את יהודה ואת ישבי ירושלם כהזנות בית אחאב וגם את אחיך בית אביך הטובים ממך הרגת 13
Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki.
הנה יהוה נגף מגפה גדולה--בעמך ובבניך ובנשיך ובכל רכושך 14
Saboda haka a yanzu Ubangiji yana shirin ya bugi mutanenka,’ya’yanka maza, matanka da kuma kome da yake naka, da bugu mai ƙarfi.
ואתה בחליים רבים במחלה מעיך עד יצאו מעיך מן החלי ימים על ימים 15
Kai kuma za ka kamu da ciwon hanji wanda zai yi ta cinka kowace rana sai har hanjinka sun fito.’”
ויער יהוה על יהורם את רוח הפלשתים והערבים אשר על יד כושים 16
Ubangiji ya sa Filistiyawa da Larabawa waɗanda suke zama kusa da Kushawa su yi gāba da Yehoram
ויעלו ביהודה ויבקעוה וישבו את כל הרכוש הנמצא לבית המלך וגם בניו ונשיו ולא נשאר לו בן כי אם יהואחז קטן בניו 17
Suka yaƙi Yahuda, suka kai masa hari, suka kwashe dukan abubuwa masu kyau da suka samu a fadan sarki, tare da’ya’yansa maza da kuma matansa. Ba wanda aka bari, sai dai Ahaziya autansa.
ואחרי כל זאת--נגפו יהוה במעיו לחלי לאין מרפא 18
Bayan dukan wannan, sai Ubangiji ya sa wa Yehoram cuta marar warkarwa ta ciki.
ויהי לימים מימים וכעת צאת הקץ לימים שנים יצאו מעיו עם חליו וימת בתחלאים רעים ולא עשו לו עמו שרפה כשרפת אבתיו 19
Cikin lokaci, a ƙarshen shekara ta biyu, sai hanjin cikinsa suka fito saboda cutar, ya kuma mutu cikin tsananin zafi. Mutanensa suka hura wuta don girmama shi, kamar yadda suka yi wa kakanninsa.
בן שלשים ושתים היה במלכו ושמונה שנים מלך בירושלם וילך בלא חמדה ויקברהו בעיר דויד ולא בקברות המלכים 20
Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya mutu, ba ma wanda ya kula, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda, amma ba a makabartan sarakuna ba.

< דברי הימים ב 21 >