< Romawa 9 >
1 Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki.
Sandhed siger jeg i Kristus, jeg lyver ikke, min Samvittighed vidner med mig i den Helligånd,
2 cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata.
at jeg har en stor Sorg og en uafladelig Kummer i mit Hjerte.
3 Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki.
Thi jeg kunde ønske selv at være bandlyst fra Kristus til Bedste for mine Brødre, mine Frænder efter Kødet,
4 Sune Isra'ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari'a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai.
de, som jo ere Israeliter, hvem Sønneudkårelsen og Herligheden og Pagterne og Lovgivningen og Gudstjenesten og Forjættelserne tilhøre,
5 Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin. (aiōn )
hvem Fædrene tilhøre, og af hvem Kristus er efter Kødet, han, som er Gud over alle Ting, højlovet i Evighed! Amen. (aiōn )
6 Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra'ilawa ne suke Isra'ilawa na gaskiya ba.
Ikke dog som om Guds Ord har glippet; thi ikke alle, som stamme fra Israel, ere Israel;
7 Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne 'ya'yansa ba. Amma ''ta wurin Ishiyaku ne za'a kira zuriyarka.''
ej, heller ere alle Børn, fordi de ere Abrahams Sæd, men: "I Isak skal en Sæd få Navn efter dig."
8 Yana nuna mana cewa ba 'ya'yan jiki su ne 'ya'yan Allah ba. Amma 'ya'yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su.
Det vil sige: Ikke Kødets Børn ere Guds Børn, men Forjættelsens Børn regnes for Sæd.
9 Wanna ce kalmar alkawari, ''badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da.''
Thi et Forjættelsesord er dette: "Ved denne Tid vil jeg komme, så skal Sara have en Søn."
10 Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku.
Men således skete det ikke alene dengang, men også med Rebekka, da hun var frugtsommelig ved een, Isak, vor Fader.
11 Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira—
Thi da de endnu ikke vare fødte og ikke havde gjort noget godt eller ondt, blev der, for at Guds Udvælgelses Beslutning skulde stå fast, ikke i Kraft af Gerninger, men i Kraft af ham, der kalder,
12 kamar yadda Ya ce, mata, “babban zaya yiwa karamin bauta,'' haka nassi yace,
sagt til hende: ""Den ældste skal tjene den yngste,""
13 ''Kamar yadda aka rubuta: “Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi.”
som der er skrevet: ""Jakob elskede jeg, men Esau hadede jeg."
14 To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan.
Hvad skulle vi da sige? mon der er Uretfærdighed hos Gud? Det være langt fra!
15 Gama ya ce wa Musa, ''Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa.''
Thi han siger til Moses: "Jeg vil være barmhjertig imod den, hvem jeg er barmhjertig imod, og forbarme mig over den, hvem jeg forbarmer mig over."
16 Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai.
Altså står det ikke til den, som vil, ej heller til den, som løber, men til Gud, som er barmhjertig.
17 Gama nassi ya ce da Fir'auna, '' Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya.''
Thi Skriften siger til Farao: "Netop derfor lod jeg dig fremstå, for at jeg kunde vise min Magt på dig, og for at mit Navn skulde forkyndes på hele Jorden."
18 Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama.
Så forbarmer han sig da over den, som han vil, men forhærder den, som han vil.
19 Za kuce mani, to don me, ''Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?''
Du vil nu sige til mig: Hvad klager han da over endnu? thi hvem står hans Villie imod?
20 In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, ''Don me yasa ka ginani haka?''
Ja, men, hvem er dog du, o Menneske! som går i Rette med Gud? mon noget, som blev dannet, kan sige til den, som dannede det: Hvorfor gjorde du mig således?
21 Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki?
Eller har Pottemageren ikke Rådighed over Leret til af den samme Masse at gøre et Kar til Ære, et andet til Vanære?
22 In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa?
Men hvad om nu Gud, skønt han vilde vise sin Vrede og kundgøre sin Magt, dog med stor Langmodighed tålte Vredes-Kar, som vare beredte til Fortabelse,
23 To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko?
også for at kundgøre sin Herligheds Rigdom over Barmhjertigheds-Kar, som han forud havde beredt til Herlighed?
24 Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al'ummai?
Og hertil kaldte han også os, ikke alene af Jøder, men også af Hedninger,
25 Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha'u: ''zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba.
som han også siger hos Hoseas: "Det, som ikke var mit Folk, vil jeg kalde mit Folk, og hende, som ikke var den elskede; den elskede;
26 Zai zama kuma a inda aka ce da su, “ku ba mutanena bane, za a kisa su 'ya'yan Allah mai rai.”'
og det skal ske, at på det Sted, hvor der blev sagt til dem: I ere ikke mit Folk, der skulle de kaldes den levende Guds Børn."
27 Ishaya ya yi kira game da Isra'ila, ''in a ce yawan 'ya'yan Isra'ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto.
Men Esajas udråber over Israel: "Om end Israels Børns Tal var som Havets Sand, så skal kun Levningen frelses.
28 Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba.
Thi idet Herren opgør Regnskab og afslutter det i Hast, vil han fuldbyrde det på Jorden."
29 Yadda Ishaya ya rubuta ada, ''In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata.
Og som Esajas forud har sagt: "Dersom den Herre Zebaoth ikke havde levnet os en Sæd, da vare vi blevne som Sodoma og gjorte lige med Gomorra."
30 To me za mu ce kenan? Ko al'ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya.
Hvad skulle vi da sige? At Hedninger, som ikke jagede efter Retfærdighed, fik Retfærdighed; nemlig Retfærdigheden af Tro;
31 Amma Isra'ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari'a, ba su kai ga gaci ba.
men Israel, som jagede efter en Retfærdigheds Lov, nåede ikke til en sådan Lov.
32 To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi.
Hvorfor? fordi de ikke søgte den af Tro, men som af Geringer. De stødte an på Anstødsstenen,
33 Kamar yadda aka rubuta, “Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba.”
som der er skrevet: "Se, jeg sætter i Zion en Anstødssten og en Forargelses Klippe; og den, som tror på ham, skal ikke blive til Skamme."