< Romawa 7 >
1 'Yan'uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari'a), cewar shari'a na mulkin mutum muddin ransa?
Zdaliž nevíte, bratří, (nebo povědomým Zákona mluvím) že Zákon panuje nad člověkem, dokudž živ jest člověk?
2 Domin ta wurin shari'a matar aure a daure take muddin mijinta nada rai, amma idan mijinta ya mutu, ta kubuta daga shari'ar aure.
Nebo žena, kteráž za mužem jest, živému muži přivázána jest zákonem; pakli by umřel muž její, rozvázána jest od zákona muže.
3 To don haka idan, mijinta na da rai, sai ta tafi ta zauna da wani mutumin, za'a kirata mazinaciya. Amma idan mijin ya mutu, ''yantarciya ce daga shari'a, domin kada ta kasance mazinaciya idan ta auri wani mutum.
A protož dokudž jest živ muž její, slouti bude cizoložnice, bude-li s jiným mužem; pakliť by muž její umřel, jižť jest svobodna od zákona toho, takže již nebude cizoložnice, bude-li s jiným mužem.
4 Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya.
Takž, bratří moji, i vy umrtveni jste Zákonu skrze tělo Kristovo, abyste byli jiného, totiž toho, kterýž z mrtvých vstal, abychom ovoce nesli Bohu.
5 Domin sa'adda muke cikin jiki, ana motsa dabi'armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari'a domin mu haifi 'ya'ya zuwa mutuwa.
Nebo když jsme byli v těle, žádosti hříchů příčinou Zákona vzbuzené moc svou provodily v údech našich k nesení ovoce ne Bohu, ale smrti.
6 Amma yanzu an kubutar damu daga shari'a, mun mutu daga abin da ya daure mu, domin mu yi bauta cikin sabuntuwar Ruhu, ba cikin tsohon rubutun shari'a ba.
Nyní pak osvobozeni jsme od Zákona, když umřel ten, v němž jsme držáni byli, tak abychom již sloužili v novotě ducha, a ne v vetchosti litery.
7 To me zamu ce kenan? ita shari'ar kanta zunubi ce? ba zai taba faruwa ba. Duk da haka. Idan ba ta wurin shari'a ba, ba zan taba sanin zunubi ba, in ba ta wurin shari'a ba. Ba zan taba kyashin abin wani ba, har sai da shari'a tace, “Kada kayi kyashi.”
Což tedy díme? Že Zákon jest hříchem? Nikoli; nýbrž hříchu jsem nepoznal, než skrze Zákon. Nebo i o žádosti byl bych nevěděl, aby hříchem byla, by byl Zákon neřekl: Nepožádáš.
8 Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha'awa dake cikina. Domin in da babu shari'a, zunubi matacce ne.
Ale příčinu vzav hřích skrze přikázaní, zplodil ve mně všelikou žádost. Bez Zákona zajisté hřích mrtev jest.
9 Ada na rayu sau daya ba tare da shari'a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu.
Jáť pak byl jsem živ někdy bez Zákona, ale když přišlo přikázání, hřích ožil,
10 Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya.
a já umřel. I shledáno jest, že to přikázání, kteréž mělo mi býti k životu, že jest mi k smrti.
11 Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni.
Nebo hřích, vzav příčinu skrze to přikázání, podvedl mne, a skrze ně i zabil.
12 Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau.
A tak Zákon zajisté svatý, a přikázání svaté i spravedlivé a dobré jest.
13 To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi.
Tedy to dobré učiněno jest mi smrt? Nikoli, ale hřích, kterýž aby se okázal býti hříchem, skrze to dobré zplodil mi smrt, aby tak byl příliš velmi hřešící hřích skrze přikázání.
14 Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi.
Víme zajisté, že Zákon jest duchovní, ale já jsem tělesný, prodaný hříchu.
15 Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa.
Nebo toho, což činím, neoblibuji; nebo ne, což chci, to činím, ale, což v nenávisti mám, to činím.
16 Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau.
Jestližeť pak, což nechci, to činím, tedy povoluji Zákonu, že jest dobrý.
17 Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina.
A tak již ne já to činím, ale ten, kterýž přebývá ve mně, hřích.
18 Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa.
Vímť zajisté, že nepřebývá ve mně, (to jest v těle mém), dobré. Nebo chtění hotové mám, ale vykonati dobrého, tohoť nenalézám.
19 Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa.
Nebo nečiním toho dobrého, což chci, ale činím to zlé, čehož nechci.
20 To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina.
A poněvadž pak, čehož já nechci, to činím, tedyť již ne já činím to, ale ten, kterýž přebývá ve mně, hřích.
21 Don haka, sai na iske, akwai ka'ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani.
Nalézám tedy takový při sobě zákon, když chci činiti dobré, že se mne přídrží zlé.
22 Domin a cikina ina murna da shari'ar Allah.
Nebo zvláštní libost mám v Zákoně Božím podle vnitřního člověka;
23 Amma ina ganin wasu ka'idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka'idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka'idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina.
Ale vidím jiný zákon v údech svých, odporující zákonu mysli mé a jímající mne, tak abych byl vězeň zákona hřícha, kterýž jest v údech mých.
24 Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa?
Bídný já člověk! Kdo mne vysvobodí z toho těla smrti?
25 Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari'ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka'idar zunubi da ke tare da jikina.
Ale děkujiť Bohu skrze Jezukrista Pána našeho. A takžť já sloužím myslí Zákonu Božímu, ale tělem zákonu hřícha.