< Romawa 6 >

1 Me kuwa zamu ce yanzu? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita?
What should we say then? Should we continue in sin, that grace may abound?
2 Ba zai taba faruwa ba. 'Yaya za'ace mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa?
Absolutely not. We who died to sin, how could we live in it any longer?
3 Ba ku san cewa duk wadanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba?
Or do you not know that all we who were baptized into Messiah Jesus were baptized into his death?
4 An kuwa binne mu tare da shi, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa. Haka kuma ya kasance ne domin kamar yadda Almasihu ya tashi daga matattu cikin daukakar Uba. Sakamakon haka muma zamu yi tafiya cikin sabuwar rayuwa.
We were buried therefore with him through baptism to death, that just like Messiah was raised from the dead through the glory of the Father, so we also might walk in newness of life.
5 Domin kuwa idan muna tare dashi cikin kamannin mutuwarsa zamu kuwa zauna tare dashi har ga kamannin tashinsa.
For if we have become united with him in the likeness of his death, we will also be part of his resurrection;
6 Mun kuma san cewa, an giciye wannan tsohon mutunmin nan namu tare dashi, domin a hallaka jikin zunubi. wanna kuwa ya kasance ne domin kada mu ci gaba da bautar zunubi.
knowing this, that our old self was crucified with him, that the body of sin might be done away with, so that we would no longer be in bondage to sin.
7 Duk kuma wanda ya mutu an ambace shi a matayin adali akan zunubi.
For he who has died has been freed from sin.
8 Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun bada gaskiya zamu yi rayuwa tare dashi.
But if we died with Messiah, we believe that we will also live with him;
9 Muna da sanen cewa an tada Almasihu daga matattu, don haka kuwa ba matacce yake ba. Mutuwa kuma bata da iko a kansa.
knowing that Messiah, being raised from the dead, dies no more. Death no more has dominion over him.
10 Game da mutuwar da yayi ga zunubi yayi sau daya kuma domin dukka. Rayuwar da yake yi kuma yana yi wa Allah ne.
For the death that he died, he died to sin one time; but the life that he lives, he lives to God.
11 Don haka ku ma sai ku dauki kanku a matsayin matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Almasihu Yesu.
In the same way, consider yourselves dead to sin, but alive to God in Messiah Jesus.
12 Sabili da haka kada ku bar zunubi yayi mulki a cikin jikinku, har ku yi biyayya ga sha'awarsa.
Therefore do not let sin reign in your mortal body, that you should obey it in its lusts.
13 Kada ku mika gabobin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin rashin adalci. Amma ku mika kanku ga Allah rayayyu daga mutuwa. Ku kuma mika gabobin jikinku ga Allah a matsayin kayan aiki na adalci.
Neither present your members to sin as instruments of unrighteousness, but present yourselves to God, as alive from the dead, and your members as instruments of righteousness to God.
14 kada ku ba zunubi dama yayi mulki a kanku, domin ba karkashin doka kuke ba, amma karkashin alheri kuke.
For sin will not have dominion over you. For you are not under law, but under grace.
15 To sai me? Sai mu yi zunubi wai don ba a karkashin doka muke ba amma alheri. ba zai taba faruwa ba.
What then? Should we sin because we are not under law, but under grace? Absolutely not.
16 Ba ku san cewa duk ga wanda kuka mika kanku a matsayin bayi, a gareshi ku bayi ne ba? Wannan fa gaskiya ne, ko dai ku bayi ne ga zunubi wanda kaiwa ga mutuwa ko kuma bayi ga biyayya wanda ke kaiwa ga adalci.
Do you not know that when you present yourselves to someone as obedient slaves, you are slaves of the one whom you obey, whether of sin, which leads to death, or of obedience, which leads to righteousness?
17 Amma godiya ta tabbata ga Allah! domin da ku bayin zunubi ne, amma kun yi biyayya daga zuciyarku irin salon koyarwar da aka baku.
But thanks be to God, that, whereas you were slaves of sin, you became obedient from the heart to that form of teaching to which you were entrusted.
18 An 'yantar daku daga bautar zunubi, an kuma maishe ku bayin adalci.
Being made free from sin, you became slaves of righteousness.
19 Ina magana da ku kamar mutum, domin kasawarku ta nama da jini. Kamar yadda kuka mika gabobin jikinku ga kazamta da miyagun ayyuka, haka ma yanzu ku mika gabobin jikinku a matsayin bayi na adalci.
I speak in human terms because of the weakness of your flesh, for as you presented your members as slaves to uncleanness and to wickedness upon wickedness, even so now present your members as slaves to righteousness for sanctification.
20 Domin a lokacin da kuke bayin zunubi, ku yantattu ne ga adalci.
For when you were slaves of sin, you were free in regard to righteousness.
21 A wannan lokacin wanne amfani kuka samu na ayyukan da yanzu kuke jin kunyarsu? Domin kuwa sakamakon wadannan ayyuka shine mutuwa.
What fruit then did you have at that time in the things of which you are now ashamed? For the end of those things is death.
22 Amma yanzu da da aka yantar daku daga zunubi aka mai da ku bayin Allah, amfaninsa ku kuwa shine tsarkakewarku. Sakamakon kuwa shine rai na har abada. (aiōnios g166)
But now, being made free from sin, and having become slaves of God, you have your fruit of sanctification, and the result of everlasting life. (aiōnios g166)
23 Don kuwa sakamakon zunubi mutuwa ne. Amma kyautar Allah itace rai madauwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. (aiōnios g166)
For the wages of sin is death, but the free gift of God is everlasting life in Messiah Jesus our Lord. (aiōnios g166)

< Romawa 6 >