< Romawa 4 >
1 Me kenan zamu ce game da Ibrahim, kakanmu a jiki, me ya samu?
What then shall we say that our father Abraham discovered, as a man?
2 Domin idan Ibrahim ya sami kubutarwa ta wurin ayuka, ai da ya sami dalilin fahariya, amma ba a gaban Allah ba.
If Abraham was really justified by works, he has a boast—but not before God.
3 Kuma fa me nassi ke fadi? “Ibrahim ya bada gaskiya ga Allah, sai aka lisafta ta adalci gare shi.”
So what does the Scripture say? “Abraham believed God, and it was credited to him as righteousness.”
4 Yanzu fa shi dake yin ayyuka, ladansa ba a lisafta shi alheri ba ne, amma abun da ke nasa.
Now to him who works, the pay is not counted as a gift but as an obligation.
5 Amma kuma shi da bai da ayyuka kuma maimakon haka ya gaskanta ga wanda ke kubutar da masu zunubai, bangaskiyarsa an lisafta ta a misalin adalci.
But to him who does not work but believes on Him who justifies the ungodly, his faith is credited as righteousness.
6 Dauda ya yi furcin albarka bisa mutumin da Allah ya lisafta mai adalci da rashin ayyuka.
Just as David speaks of the blessing of the man to whom God credits righteousness apart from works:
7 Sai ya ce, “Masu albarka ne wadanda aka yafe laifofinsu, kuma wadanda zunubansu a rufe suke.
“Blessed are they whose lawless deeds have been forgiven, and whose sins have been covered up.
8 Mai albarka ne mutumin da ko kadan Ubangiji ba zaya lisafta zunubin sa ba.”
Blessed is the man to whom the Lord will not impute sin!”
9 To albarkar da aka fadi ko a bisansu wadanda aka yi wa kaciya ne kadai, ko kuwa a bisan su ma marasa kaciya? Domin mun yi furcin, “Bangaskiyar Ibrahim an lisafta ta adalci ce agare shi.”
Is this blessing then only for the circumcised, or also for the uncircumcised? Since we say that faith was credited to Abraham as righteousness,
10 Yaya aka lisafta ta? Bayan Ibrahim ya yi kaciya, ko kuwa a rashin kaciya? Ba a cikin kaciya ba, amma a rashin kaciya.
how then was it credited? After he was circumcised or while still uncircumcised? Not circumcised, but uncircumcised!
11 Ibrahim ya amshi alamar kaciya. Wannan shi ne hatimin adalcin bangaskiyar da ya ke da ita tun cikin rashin kaciyarsa. Albarkacin wannan alama ce, ta sa shi ya zama uban dukkan wadanda suka badagaskiya, ko da shike ba su da kaciya. Wato ma'ana, adalci za a lisafta masu.
And he received the sign of circumcision, a seal of the righteousness from his faith while still uncircumcised, so that he might be the father of all those who believe while uncircumcised, in order that this righteousness may be credited to them also,
12 Wannan kuma yana da ma'anar cewa Ibrahim ya zama uban kaciya ga wadanda suka fito ba domin masu kaciya kadai ba, amma kuma domin wadanda ke biyo matakin ubanmu Ibrahim. Kuma wannan itace bangaskiyar da ya ke da ita a rashin kaciya.
and the father of the circumcised—not only those who are circumcised, but especially those who follow in the footsteps of the faith of our father Abraham while still uncircumcised.
13 Domin ba ta wurin shari'a aka bada alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa ba, wannan alkawarin da ya ce zasu gaji duniya. Maimako, a ta wurin adalcin bangaskiya ne.
Now the promise that he would be the heir of the world was not to Abraham, or his seed, through law, but through the righteousness of faith.
14 Domin idan su da ke na shari'a magada ne, bangaskiya bata da komai, kuma alkawarin an wofintar da shi kenan.
For if those who are of law are heirs, the faith is made empty and the promise has been invalidated;
15 Domin shari'a ta kan jawo fushi, amma ta wurin rashin shari'a, babu karya umarni.
because the law produces wrath, since where there is no law neither is there transgression.
16 Saboda wannan dalili haka ta faru ta wurin bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri. Kamar haka, alkawarin ya tabbata ga dukkan zuriya. Kuma wannan zuriya ba zata kunshi wadanda suke da sanin shari'a ba kadai, har ma da wadanda ke daga bangaskiyar Ibrahim. Saboda shi ne uban dukkan kowa,
For this reason it is of faith so that it may be according to grace, in order that the promise be guaranteed to all the seed—not only to those of law, but also to those of the faith of Abraham, who is the father of us all;
17 kamar yadda aka rubuta, “Na maishe ka uba ga kasashe masu yawa.” Ibrahim na gaban aminin sa, wato, Allah, mai bada rai ga mattatu kuma ya kan kira abubuwan da basu da rai su kuma kasance.
just as it is written: “I have made you a father of many ethnic nations”—in the presence of Him whom he believed: God, who gives life to the dead and calls the nonexistent things as though they did exist.
18 Duk da halin da ke a bayyane, Ibrahim ya gaskata ga Allah kai tsaye game da abubuwan da ke nan gaba. Sai ya zama uba ga kasashe masu yawa, kamar yadda aka ambata, “... Haka zuriyarka zata kasance.”
Contrary to hope, Abraham in hope believed, so as to become a father of many ethnic nations, according to what had been spoken: “So shall your seed be.”
19 Ba ya karaya a bangaskiya ba. Ibrahim ya yarda da cewa jikinsa ya rigaya ya tsufa (shekarun sa na misalin dari). Ya kuma yarda da cewa mahaifar Saratu bata iya bada 'ya'ya ba.
And not being weak in faith, he did not consider his own body, already dead (being about a hundred years old), or the deadness of Sarah's womb.
20 Amma domin alkawarin Allah, Ibrahim bai ji nauyin rashin bangaskiya ba. Maimakon haka, ya sami karfafawa a bangaskiyarsa sai ya daukaka Allah.
He did not waver at God's promise in unbelief; rather, he was strengthened by the faith, giving glory to God,
21 Ya na da cikakkiyar gamsuwa cewa idan Allah ya yi alkawari, shi mai iya kammalawa ne.
being fully convinced that what He had promised He was also able to perform
22 Haka nan ne kuma aka lisafta masa wannan a matsayin adalci.
—that is why it was credited to him as righteousness.
23 To ba'a rubuta kawai damin amfaninsa kadai ba, da aka lisafta dominsa.
Now it was not only for his sake that it was written that it was credited to him,
24 A rubuce yake domin mu, domin wadanda za'a lisafta su, mu da muka bada gaskiya gare shi wanda ya tada Yesu Ubangijinmu daga matattu.
but for our sake also, to whom it will be credited, we who believe on Him who raised Jesus our Lord from the dead,
25 Wannan shi ne wanda aka bashe shi domin zunubanmu kuma an tada shi saboda fasar mu.
who was delivered up because of our transgressions, and was raised because of our justification.