< Romawa 3 >

1 To ina fifikon da bayahude yake dashi? Kuma ina ribar kaciya?
Quid ergo amplius Iudæo est? Aut quæ utilitas circumcisionis?
2 Akwai muhimmancinsu ta kowacce hanya. Tun farko dai, yahudawa ne aka dankawa wahayi daga Allah.
Multum per omnem modum. Primum quidem quia credita sunt illis eloquia Dei.
3 Idan wasu yahudawa basu bada gaskiya ba fa? Rashin bangaskiyarsu zai hana amincin Allah aiki?
Quid enim si quidam illorum non crediderunt? Numquid incredulitas illorum fidem Dei evacuabit? Absit.
4 Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, “Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a.”
Est autem Deus verax: omnis autem homo mendax, sicut scriptum est: Ut iustificeris in sermonibus tuis: et vincas cum iudicaris.
5 Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka.
Si autem iniquitas nostra iustitiam Dei commendat, quid dicemus? Numquid iniquus est Deus, qui infert iram?
6 Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya?
(Secundum hominem dico.) Absit. Alioquin quomodo iudicabit Deus hunc mundum?
7 Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi?
Si enim veritas Dei in meo mendacio abundavit in gloriam ipsius: quid adhuc et ego tamquam peccator iudicor?
8 To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, “Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?” Hukuncin su halal ne.
Et non (sicut blasphemamur, et sicut aiunt quidam nos dicere) faciamus mala ut veniant bona: quorum damnatio iusta est.
9 To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi.
Quid ergo? Præcellimus eos? Nequaquam. Causati enim sumus Iudæos, et Græcos omnes sub peccato esse,
10 Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya.
sicut scriptum est: Quia non est iustus quisquam:
11 Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah.
non est intelligens, non est requirens Deum.
12 Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya.
Omnes declinaverunt, simul inutiles facti sunt, non est qui faciat bonum, non est usque ad unum.
13 Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu.
Sepulchrum patens est guttur eorum, linguis suis dolose agebant: Venenum aspidum sub labiis eorum:
14 Bakunansu cike suke da la'ana da daci.
Quorum os maledictione, et amaritudine plenum est:
15 Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini.
Veloces pedes eorum ad effundendum sanguinem:
16 Tafarkinsu wahala ce da lalacewa.
Contritio, et infelicitas in viis eorum:
17 Wadannan mutane basu san hanyar salama ba.
et viam pacis non cognoverunt:
18 Babu tsoron Allah a idanunsu.”
Non est timor Dei ante oculos eorum.
19 To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah.
Scimus autem quoniam quæcumque lex loquitur, iis, qui in lege sunt, loquitur: ut omne os obstruatur, et subditus fiat omnis mundus Deo:
20 Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo.
quia ex operibus legis non iustificabitur omnis caro coram illo. Per legem enim cognitio peccati.
21 Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa.
Nunc autem sine lege iustitia Dei manifestata est: testificata a lege et Prophetis.
22 Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci:
Iustitia autem Dei per fidem Iesu Christi in omnes, et super omnes, qui credunt in eum: non enim est distinctio:
23 Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah,
Omnes enim peccaverunt, et egent gloria Dei.
24 Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu.
Iustificati gratis per gratiam ipsius, per redemptionem, quæ est in Christo Iesu,
25 Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya
quem proposuit Deus propitiationem per fidem in sanguine ipsius, ad ostensionem iustitiæ suæ propter remissionem præcedentium delictorum
26 cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu.
in sustentatione Dei, ad ostensionem iustitiæ eius in hoc tempore: ut sit ipse iustus, et iustificans eum, qui est ex fide Iesu Christi.
27 To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya.
Ubi est ergo gloriatio tua? Exclusa est. Per quam legem? Factorum? Non: sed per legem fidei.
28 Domin wannan muka kammala cewar ana baratar da mutum ta wurin bangaskiya ba tare da ayyukan shari'a ba.
Arbitramur enim iustificari hominem per fidem sine operibus legis.
29 Ko kuwa Allah Allahn yahudawa ne kadai? Shi ba Allahn al'ummai bane? I, na al'ummai ne kuma.
An Iudæorum Deus tantum? Nonne et Gentium? Immo et Gentium.
30 Idan dai lallai Allah daya ne, zai baratar da mai kaciya ta wurin bangaskiya, da marar kaciya kuma ta wurin bangaskiya.
Quoniam quidem unus est Deus, qui iustificat circumcisionem ex fide, et præputium per fidem.
31 Mun kawar da shari'a kenan ta wurin bangaskiya? ba zai taba kasancewa haka ba. Maimako ma, muna inganta shari'a kenan.
Legem ergo destruimus per fidem? Absit: sed legem statuimus.

< Romawa 3 >