< Romawa 2 >

1 Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa.
Зато се не можеш изговорити, о човече који год судиш! Јер којим судом судиш другом, себе осуђујеш; јер то чиниш судећи.
2 Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa.
А знамо да је суд Божји прав на оне који то чине.
3 Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah?
Него помишљаш ли, о човече који судиш онима који то чине, и сам чиниш то! Да ћеш ти побећи од суда Божијег?
4 Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane?
Или не мариш за богатство Његове доброте и кротости и трпљења, не знајући да те доброта Божија на покајање води?
5 Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah.
Него својом дрвености и непокајаним срцем сабираш себи гнев за дан гнева у који ће се показати праведни суд Бога,
6 Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa:
Који ће дати свакоме по делима његовим:
7 Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada. (aiōnios g166)
Онима, дакле, који су трпљењем дела доброг тражили славу и част и нераспадљивост, живот вечни; (aiōnios g166)
8 Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu.
А онима који се уз пркос супроте истини, а покоравају се неправди, немилост и гнев.
9 Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa.
Невоља и туга на сваку душу човека који чини зло, а најпре Јеврејина и Грка;
10 Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa.
А слава и част и мир свакоме који чини добро, а најпре Јеврејину и Грку;
11 Domin kuwa Allah ba mai tara bane.
Јер Бог не гледа ко је ко.
12 Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a.
Јер који без закона сагрешише, без закона ће и изгинути; и који у закону сагрешише, по закону ће се осудити
13 Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata.
(Јер пред Богом нису праведни они који слушају закон, него ће се они оправдати који га творе;
14 Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar.
Јер кад незнабошци не имајући закон сами од себе чине шта је по закону, они закон не имајући сами су себи закон:
15 Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu.
Они доказују да је оно написано у срцима њиховим што се чини по закону, будући да им савест сведочи, и мисли међу собом туже се или правдају)
16 hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu.
На дан када Бог узасуди тајне људске по јеванђељу мом преко Исуса Христа.
17 Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah,
Гле, ти се зовеш Јеврејин, а ослањаш се на закон и хвалиш се Богом,
18 ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar.
И познајеш вољу, и избираш шта је боље, јер си научен од закона;
19 Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu,
И мислиш да си вођ слепима, видело онима који су у мраку,
20 mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya.
Наказатељ безумнима, учитељ деци, који имаш углед разума и истине у закону.
21 ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata?
Учећи, дакле, другог себе не учиш;
22 Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali?
Проповедајући да се не краде, крадеш; говорећи: Не чини прељубе, чиниш прељубу: гадећи се на идоле, крадеш светињу;
23 ku masu murna da tinkaho cikin shari'ar, ba kwa wulakanta Allah cikin kurakuranku na rashin bin shari'a?
Који се хвалиш законом, а преступом закона срамотиш Бога.
24 ''Domin kuwa an wulakanta sunan Allah cikin Al'umai sabili da ku,'' kamar yadda aka riga aka rubuta.
Јер се име Божије због вас хули у незнабошцима, као што стоји написано.
25 Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya.
Обрезање помаже ако закон држиш; ако ли си преступник закона, обрезање је твоје необрезање постало.
26 domin kuwa idan mutum marar kaciya zai kiyaye dukkan bukatun doka, baza'a iya daukan rashin kaciyarsa a matsayin mai kaciya ba?
Ако, дакле, необрезање правду закона држи, зашто се не би његово необрезање за обрезање узело?
27 Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka!
И онај који је од рода необрезан и извршује закон, осудиће тебе који си са словима и обрезањем преступник закона.
28 Domin shi kuwa ba Bayahude bane a waje; ba kuwa mai kaciyar da aka tsaga fata ba.
Јер оно није Јеврејин који је споља Јеврејин, нити је оно обрезање које је споља, на телу;
29 Amma Bayahude ne ta ciki, sanna kuma mai kaciyar zuciya da kuma ruhu ba wasika ba, irin wanna mutumin yabonsa ba daga wurin mutane yake zuwa ba, amma daga Allah.
Него је оно Јеврејин који је изнутра и обрезање срца духом а не словима, то је обрезање; коме је хвала не од људи него од Бога.

< Romawa 2 >