< Romawa 16 >

1 Ina gabatar muku da fibi 'yar'uwarmu, wanda take hidima a Ikilisiya dake cikin Kankiriya.
I commend to you Phebe our sister, who is a servant of the church which is at Cenchrea:
2 Domin ku karbe ta cikin Ubangij. A hanyar da ta dace ga masu bada gaskiya, ku tsaya tare da ita cikin kowacce bukata. Domin ita da kanta ta zama da taimako ga masu yawa, har da ni ma.
That ye receive her in the Lord, as it becometh saints, and that ye assist her in whatever business she hath need of you: for she hath been a succorer of many, and of myself also.
3 Ku gai da Bilkisu da Akila abokan aiki cikin Yesu Almasihu.
Greet Priscilla and Aquila my helpers in Christ Jesus:
4 Wadanda sabo da ni suka sadaukar da ransu. Ina godiya garesu, ba ni kadai ba, amma kuma da dukan Ikilisiyoyin Al 'mmai.
Who have for my life laid down their own necks: to whom not only I give thanks, but also all the churches of the Gentiles.
5 Gaida Ikilisiya da ke gidansu. Ku gai da Abainitas kaunataccena. Wanda shi ya fara bada gaskiya ga Almasihu a Asiya.
Likewise [greet] the church that is in their house. Salute my well-beloved Epenetus, who is the first-fruits of Achaia to Christ.
6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi maku aiki tukuru.
Greet Mary, who bestowed much labor on us.
7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, yan'uwana da abokan kurkukuna. Su sanannu ne cikin manzani, wadanda suke cikin Almasihu kafin ni.
Salute Andronicus and Junia my kinsmen, and my fellow-prisoners, who are of note among the apostles, who also were in Christ before me.
8 Ku gai da Amfiliyas kaunatace na cikin Ubangiji.
Greet Amplias my beloved in the Lord.
9 Ku gai da Urbanas abokin aikinmu cikin Almasihu, da Istakis kaunataccena.
Salute Urbane, our helper in Christ, and Stachys my beloved.
10 Ku gai da Abalis amintacce cikin Almasihu. Ku gai da wadanda su ke gidan Aristobulus.
Salute Apelles approved in Christ. Salute them who are of Aristobulus' [household].
11 Ku gai da Hirudiya, dan'uwa na, da wadanda ke gidan Narkissa, wadanda ke cikin Ubangiji.
Salute Herodion my kinsman. Greet them that are of the [household] of Narcissus, who are in the Lord.
12 Ku gai da Tarafina daTarafusa, masu aikin Ubangiji.
Salute Tryphena and Tryphosa, who labor in the Lord. Salute the beloved Persis, who labored much in the Lord.
13 Ku gai da Barsisa kaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji da yawa. Ku gai da Rufas zababbe cikin Ubangiji da mamarsa da ni.
Salute Rufus chosen in the Lord, and his mother and mine.
14 Ku gai da Asinkiritas da Filiguna da Hamis da Baturobas da Hamisu da kuma yan'uwa da ke tare da su.
Salute Asyncritus, Phlegon, Hermas, Patrobas, Hermes, and the brethren who are with them.
15 Ku gai da Filolugus daYuliya da Niriyas da yan'uwansa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkaka da ke tare su.
Salute Philologus, and Julia, Nereus, and his sister, and Olympas, and all the saints who are with them.
16 Ku gaggai da juna da tsatsarkar sumba. Dukan Ikilisiyoyin Almasihu na gaishe ku.
Salute one another with a holy kiss. The churches of Christ salute you.
17 Yanzu ina rokon ku, yan'wa, ku yi tunani fa game da masu kawo rabuwa da tuntube. Sabanin koyarwar da ku ka koya. Ku yi nesa da su.
Now I beseech you, brethren, mark them who cause divisions and offenses, contrary to the doctrine which ye have learned; and avoid them.
18 Domin irin mutanen nan ba sa bauta wa Ubangiji Yesu, sai dai tumbinsu. Ta dadin bakinsu suke rudin zuciyar marasa laifi.
For they that are such serve not our Lord Jesus Christ, but their own belly; and by good words and fair speeches deceive the hearts of the simple.
19 Domin rayuwar biyayyarku takai ga kunnen kowa, na yi farin ciki da ku, amma ina so ku zama da hikima game da abin ya ke mai kyau, ku zama marasa laifi ga abin da ke na mugunta.
For your obedience is come abroad to all [men]. I am glad therefore on your behalf: but yet I would have you wise to that which is good, and simple concerning evil.
20 Allah na salama zai sa ku tattake Shaidan da sauri kalkashin sawayen ku. Alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku.
And the God of peace will soon bruise Satan under your feet. The grace of our Lord Jesus Christ [be] with you. Amen.
21 Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana.
Timothy my work-fellow, and Lucius, and Jason, and Sosipater my kinsmen, salute you.
22 Ni Tartiyas wanda ya rubuta wasikan nan, na gaisheku cikin Ubangiji.
I Tertius, who wrote [this] epistle, salute you in the Lord.
23 Gayus mai masaukina da kuma dukan Ikilisiya, suna gaishe ku. Arastas ma'ajin birni na gaishe ku, da Kwartus dan'uwanmu.
Gaius my host, and of the whole church, saluteth you. Erastus the chamberlain of the city saluteth you, and Quartus a brother.
24 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku dukka. Amin.
The grace of our Lord Jesus Christ [be] with you all. Amen.
25 Yanzu ga wanda ke da Ikon karfafa ku bisa ga bisharata da wa'azin Yesu Almasihu, wanda ta gare shi ne aka bayyana asiran nan da suke boye tun da dadewa, (aiōnios g166)
Now to him that is able to establish you according to my gospel, and the preaching of Jesus Christ, according to the revelation of the mystery, which hath been kept secret since the world began, (aiōnios g166)
26 amma yanzu sanannu ne ta wurin litattafan Annabawa bisa umarnin Allah madauwami, domin biyayyar bangaskiya cikin Al'ummai dukka. (aiōnios g166)
But now is made manifest, and by the scriptures of the prophets, according to the commandment of the everlasting God, made known to all nations for the obedience of faith: (aiōnios g166)
27 Ga Allah mai hikima kadai, ta wurin Yesu Almasihu daukaka ta tabbata har abada. Amin. (aiōn g165)
To God the only wise, [be] glory through Jesus Christ for ever. Amen. (aiōn g165)

< Romawa 16 >