< Romawa 15 >
1 Yanzu mu da muke da karfi ya kamata mu dau nauyi raunana, kuma bai dace mu nuna son kai ba.
Дужни смо, дакле, ми јаки слабости слабих носити, и не себи угађати.
2 Bari kowannenmu ya faranta wa makwabcinsa rai, domin wannan yana da kyau, don a gina shi.
И сваки од вас да угађа ближњему на добро за добар углед.
3 Domin Almasihu bai faranta wa kansa rai ba. Kamar yadda aka rubuta, “zagin da wadansu suka yi masa ya sauka a kaina.”
Јер и Христос не угоди себи, него као што је писано: Ружења оних који Тебе руже падоше на ме.
4 Don abin da aka rubuta a baya an rubuta ne domin a gargade mu, domin ta hakuri da karfafawar litattafai mu sami karfi.
Јер шта се напред написа, за нашу се науку написа, да трпљењем и утехом писма наду имамо.
5 Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu.
А Бог трпљења и утехе да вам да да сложно мислите међу собом по Христу Исусу,
6 Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya.
Да једнодушно једним устима славите Бога и Оца Господа нашег Исуса Христа.
7 Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah.
Зато примајте један другог као што и Христос прими вас на славу Божију.
8 Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu.
Али кажем да је Исус Христос био слуга обрезања истине ради Божије, да утврди обећање очевима,
9 Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, “Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka.”
А незнабошци по милости да прославе Бога, као што стоји написано: Зато ћу Те хвалити међу незнабошцима, Господе, и певаћу име Твоје.
10 Kuma an ce. “Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa.”
И опет говори: Веселите се незнабошци с народом Његовим.
11 Kuma.” Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi.”
И опет: Хвалите Господа сви незнабошци, и славите Га сви народи.
12 Kuma, Ishaya ya ce “Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa.”
И опет Исаија говори: Биће корен Јесејев, и који устане да влада над незнабошцима у Оног ће се уздати незнабошци.
13 Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
А Бог наде да испуни вас сваке радости и мира у вери, да имате изобиље у нади силом Духа Светог.
14 Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna.
А ја сам и сам уверен за вас, браћо, да сте и ви сами пуни благодати, напуњени сваког разума, да можете друге научити.
15 Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah.
Али вам опет, браћо, слободно писах неколико да вам напоменем ради благодати која ми је дана од Бога,
16 Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
Да будем слуга Исуса Христа у незнабошцима, да служим јеванђељу Божијем, да буду незнабошци принос повољан и освећен Духом Светим.
17 Don haka ina jin dadi cikin Yesu Almasihu da abubuwa na Allah.
Имам, дакле, хвалу у Христу Исусу код Бога.
18 Domin ba ni da abin da zan ce, sai abin da Yesu ya aikata ta wurina, domin Al'ummai su yi biyayya ta magana da aiki.
Јер не смем говорити шта које Христос не учини кроза ме за послушање незнабожаца речју и делом,
19 Ta wurin alamu, da al'jibai, da ikon Ruhu Mai Tsarki. Daga Urushalima, da kewaye har zuwa Ilirikum, an kai bisharar Almasihu ko'ina dukka.
У сили знака и чудеса силом Духа Божијег; тако да од Јерусалима и наоколо тја до Илирика напуних јеванђељем Христовим.
20 A cikin hanyar nan, burina in sanar da bishara, amma a inda ba a san Yesu ta wurin sunansa ba, don kada in sa gini akan harshashi wani.
И тако се трудих да проповедим јеванђеље не где се спомињаше Христос, да на туђој закопини не зидам;
21 Kamar yadda yake a rubuce.”Wadanda ba a taba fada wa labarinsa ba, su gane. Wadanda ba su taba jin labarinsa ba su fahimta.”
Него као што је писано: Којима се не јави за Њега, видеће; и који не чуше разумеће.
22 Saboda an hana ni zuwa wurin ku a lokatai da dama.
То ме задржа много пута да не дођем к вама.
23 Amma yanzu bani da sauran wani wuri a lardin nan, kuma cikin shekaru masu yawa ina da marmarin in zo wurin ku.
А сад више не имајући места у овим земљама, а имајући жељу од много година да дођем к вама,
24 Duk lokacin da zan tafi Asbaniya ina begen ganin ku yayin wucewa, don ku raka ni bayan na ji dadin zama da ku na dan lokaci.
Ако пођем у Шпањолску, доћи ћу вам; јер се надам да ћу туда проћи и вас видети, и ви ћете ме отпратити онамо кад се најпре неколико наситим вас.
25 Amma yanzu ina tafiya Urushalima don in yi wa tsarkaka hidima.
А сад идем у Јерусалим служећи светима.
26 Domin abin farinciki ne ga mutanen Makidoniya da Akaya su yi bayarwa domin gajiyayyu masu bada gaskiya wadanda suke a Urushalima.
Јер Македонија и Ахаја учинише драговољно неки порез за сиромахе свете који живе у Јерусалиму.
27 Suna jin dadi domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin Al'ummai sun yi tarayya da su cikin ayyukan ruhaniya, ya zama hakki a kansu su ma su taimake su da abubuwa.
Они учинише драговољно, а и дужни су им; јер кад незнабошци добише део у њиховим духовним имањима, дужни су и они њима у телесним послужити.
28 Domin lokacin da na gama basu kudin, zan zo gareku a hanyata ta zuwa Asbaniya.
Кад ово, дакле, свршим, и овај им плод запечатим, поћи ћу преко вас у Шпањолску.
29 Na san cewa lokacin da na zo gareku, zan zo da cikakkun albarku na Almasihu.
А знам да кад дођем к вама, доћи ћу с обилним благословом јеванђеља Христовог.
30 Yanzu ina rokonku, yan'uwa, ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Ruhu Mai Tsarki, ku yi ta fama tare da ni a cikin yin addu'o, inku ga Allah saboda ni.
Али вас молим, браћо, заради Господа нашег Исуса Христа, и заради љубави Духа, помозите ми у молитвама за ме к Богу;
31 Kuyi haka saboda in tsira daga wadanda suke masu biyayya ga Yahudiya, domin kuma hidimata saboda Urushalima ta zama karbabbiya.
Да се избавим од оних који се противе у Јудеји, и да служба моја за Јерусалим буде по вољи светима;
32 Ku yi addu'a cewa in zo wurinku da farinciki ta wurin nufin Allah, cewa tare da ni da ku, mu sami hutu.
Да с радошћу дођем к вама, с вољом Божијом, и да се развеселим с вама.
33 Allah na salama ya kasance tare da ku duka. Amin.
А Бог мира са свима вама. Амин.