< Romawa 14 >

1 Ku karbi duk wanda yake da rarraunar bangaskiya, ba tare da sukar ra'ayinsa ba.
Τὸν δὲ ἀσθενοῦντα τῇ πίστει προσλαμβάνεσθε, μὴ εἰς διακρίσεις διαλογισμῶν.
2 Wani yana da bangaskiyar yaci komai, wani wanda yake da rauni yakanci ganye ne kawai.
ὃς μὲν πιστεύει φαγεῖν πάντα, ὁ δὲ ἀσθενῶν λάχανα ἐσθίει.
3 Kada wanda yake cin komai ya raina wanda baya cin kowanne abu. Kada kuma wanda baya cin kowanne abu ya shara'anta sauran da suke cin komai. Saboda Allah ya karbe shi.
ὁ ἐσθίων τὸν μὴ ἐσθίοντα μὴ ἐξουθενείτω, καὶ ὁ μὴ ἐσθίων τὸν ἐσθίοντα μὴ κρινέτω· ὁ Θεὸς γὰρ αὐτὸν προσελάβετο.
4 Kai wanene, kai wanene da kake ganin laifin bawan wani? Tsayawarsa ko faduwarsa ai hakin maigidansa ne, amma Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
σὺ τίς εἶ ὁ κρίνων ἀλλότριον οἰκέτην; τῷ ἰδίῳ Κυρίῳ στήκει ἢ πίπτει· σταθήσεται δέ· δυνατὸς γάρ ἐστιν ὁ Θεὸς στῆσαι αὐτόν.
5 Wani yakan daukaka wata rana fiye da sauran. Wani kuma yana daukan ranakun daidai. Kowa ya zauna a cikin hakakkewa akan ra'ayinsa.
ὃς μὲν κρίνει ἡμέραν παρ᾽ ἡμέραν, ὃς δὲ κρίνει πᾶσαν ἡμέραν. ἕκαστος ἐν τῷ ἰδίῳ νοῒ πληροφορείσθω.
6 Shi wanda ya kula da wata rana, ya kula da ita don Ubangiji. Kuma wanda yaci, yaci ne domin Ubangiji, domin yana yi wa Allah godiya. Shi wanda bai ci ba, yaki ci ne domin Ubangiji. Shima yana yi wa Allah godiya.
ὁ φρονῶν τὴν ἡμέραν Κυρίῳ φρονεῖ, καὶ ὁ μὴ φρονῶν τὴν ἡμέραν Κυρίῳ οὐ φρονεῖ. καὶ ὁ ἐσθίων Κυρίῳ ἐσθίει· εὐχαριστεῖ γὰρ τῷ Θεῷ· καὶ ὁ μὴ ἐσθίων Κυρίῳ οὐκ ἐσθίει, καὶ εὐχαριστεῖ τῷ Θεῷ.
7 Domin babu wanda yake rayuwa don kansa a cikinmu, kuma babu mai mutuwa don kansa.
οὐδεὶς γὰρ ἡμῶν ἑαυτῷ ζῇ καὶ οὐδεὶς ἑαυτῷ ἀποθνήσκει·
8 Domin in muna raye, muna raye don Ubangiji. Kuma in mun mutu, mun mutu ne don Ubangiji. Ashe, ko muna raye, ko a mace mu na Ubangiji ne.
ἐάν τε γὰρ ζῶμεν, τῷ Κυρίῳ ζῶμεν, ἐάν τε ἀποθνήσκωμεν, τῷ Κυρίῳ ἀποθνήσκομεν. ἐάν τε οὖν ζῶμεν ἐάν τε ἀποθνήσκωμεν, τοῦ Κυρίου ἐσμέν.
9 Domin wannan dalilin Almasihu ya mutu ya kuma tashi, saboda ya zama Ubangiji ga matattu da rayayyu.
εἰς τοῦτο γὰρ Χριστὸς καὶ ἀπέθανε καὶ ἀνέστη καὶ ἔζησεν, ἵνα καὶ νεκρῶν καὶ ζώντων κυριεύσῃ.
10 Amma ku don me kuke shara'anta yan'uwanku? kai kuma don me kake raina dan'uwanka? Dukan mu zamu tsaya gaban kursiyin shari'ar Allah.
Σὺ δὲ τί κρίνεις τὸν ἀδελφόν σου; ἢ καὶ σὺ τί ἐξουθενεῖς τὸν ἀδελφόν σου; πάντες γὰρ παραστησόμεθα τῷ βήματι τοῦ Χριστοῦ.
11 Domin a rubuce yake, “Na rantse, “inji Ubangiji”, kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah.”
γέγραπται γάρ· ζῶ ἐγώ, λέγει Κύριος, ὅτι ἐμοὶ κάμψει πᾶν γόνυ, καὶ πᾶσα γλῶσσα ἐξομολογήσεται τῷ Θεῷ.
12 Domin kowannenmu zai fadi abin da shi yayi da bakinsa a gaban Allah.
ἄρα οὖν ἕκαστος ἡμῶν περὶ ἑαυτοῦ λόγον δώσει τῷ Θεῷ.
13 Saboda da haka kada muyi wa juna shari'a, amma maimakon haka ku dauki wannan kudduri, don kada kowa ya zama sanadin tuntunbe ko faduwa ga dan'uwansa.
Μηκέτι οὖν ἀλλήλους κρίνωμεν, ἀλλὰ τοῦτο κρίνατε μᾶλλον, τὸ μὴ τιθέναι πρόσκομμα τῷ ἀδελφῷ ἢ σκάνδαλον.
14 Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki.
οἶδα καὶ πέπεισμαι ἐν Κυρίῳ Ἰησοῦ ὅτι οὐδὲν κοινὸν δι᾽ αὐτοῦ· εἰ μὴ τῷ λογιζομένῳ τι κοινὸν εἶναι, ἐκείνῳ κοινόν.
15 Idan har abincinka na cutar da dan'uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka.
εἰ δὲ διὰ βρῶμα ὁ ἀδελφός σου λυπεῖται, οὐκέτι κατὰ ἀγάπην περιπατεῖς. μὴ τῷ βρώματί σου ἐκεῖνον ἀπόλλυε, ὑπὲρ οὗ Χριστὸς ἀπέθανε.
16 Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu.
μὴ βλασφημείσθω οὖν ὑμῶν τὸ ἀγαθόν.
17 Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki.
οὐ γάρ ἐστιν ἡ βασιλεία τοῦ Θεοῦ βρῶσις καὶ πόσις, ἀλλὰ δικαιοσύνη καὶ εἰρήνη καὶ χαρὰ ἐν Πνεύματι Ἁγίῳ·
18 Domin wanda yake bautar Almasihu a wannan hanya, karbabbe ne ga Allah, kuma jama'a sun yarda da shi.
ὁ γὰρ ἐν τούτοις δουλεύων τῷ Χριστῷ εὐάρεστος τῷ Θεῷ καὶ δόκιμος τοῖς ἀνθρώποις.
19 Don haka, mu nemi abubuwa na salama da abubuwan da zasu gina juna.
ἄρα οὖν τὰ τῆς εἰρήνης διώκωμεν καὶ τὰ τῆς οἰκοδομῆς τῆς εἰς ἀλλήλους.
20 Kada ku lalata aikin Allah don abinci. Komai yana da tsarki, amma kaiton mutumin da yake cin abin da zai sa shi ya fadi.
μὴ ἕνεκεν βρώματος κατάλυε τὸ ἔργον τοῦ Θεοῦ. πάντα μὲν καθαρά, ἀλλὰ κακὸν τῷ ἀνθρώπῳ τῷ διὰ προσκόμματος ἐσθίοντι.
21 Bashi da kyau a ci nama ko a sha ruwan inabi, ko duk abin da zai jawo faduwar dan'uwanka.
καλὸν τὸ μὴ φαγεῖν κρέα μηδὲ πιεῖν οἶνον μηδὲ ἐν ᾧ ὁ ἀδελφός σου προσκόπτει ἢ σκανδαλίζεται ἢ ἀσθενεῖ.
22 Wannan bangaskiyar da kuke da ita, ku adana ta tsakaninku da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa bata da laifi akan abin da hankalinsa ya ga daidai ne.
σὺ πίστιν ἔχεις; κατὰ σεαυτὸν ἔχε ἐνώπιον τοῦ Θεοῦ. μακάριος ὁ μὴ κρίνων ἑαυτὸν ἐν ᾧ δοκιμάζει.
23 Duk wanda yayi shakka amma kuma yaci, ya sani yayi laifi kenan, domin ba tare da bangaskiya bane. Duk abin da ba na bangaskya bane zunubi ne.
ὁ δὲ διακρινόμενος ἐὰν φάγῃ, κατακέκριται, ὅτι οὐκ ἐκ πίστεως· πᾶν δὲ ὃ οὐκ ἐκ πίστεως, ἁμαρτία ἐστίν.

< Romawa 14 >