< Romawa 13 >
1 Bari kowa yayi biyayya da hukuma, saboda babu wata hukuma sai dai in tazo daga Allah; mahukunta da suke nan kuwa daga Allah ne.
2 Saboda da haka duk wanda ya ja hukuma ya ja da dokar Allah; kuma dukan wadanda suka ki hukuma za su sha hukunci.
3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ne ga masu nagarta ba, amma ga masu aikata laifi. Kuna so ku zama marasa tsoron hukuma? Kuyi abu nagari, zaku sami yabo daga yin hakan.
4 Saboda shi bawan Allah ne a gare ku don nagarta. Amma in kun yi abu mara kyau, kuyi tsoro, saboda ba ya dauke da takobi ba tare da dalili ba. Don shi bawan Allah ne mai saka wa mugu da fushi.
5 Saboda haka dole kuyi biyayya, ba don fushi ba, amma saboda lamiri.
6 Saboda wannan ne kuke biyan haraji. Don masu mulki bayin Allah ne, wadanda suke yin haka kullum.
7 Ku bawa kowa hakkinsa; haraji ga mai haraji; kudin fito ga mai fito; tsoro ga wanda ya cancanci tsoro; girma ga wanda cancanci girmamawa.
8 Kada ku rike bashin kowa, sai dai ku kaunaci juna. Domin duk wanda ya kaunaci dan'uwansa ya cika doka.
9 To, “Kada kuyi zina, kada kuyi kisa, kada kuyi sata, kada kuyi kyashi, idan har akwai wata doka kuma, an takaita ta a wannan jimlar: “Ka kaunaci dan'uwanka kamar kanka.”
10 Kauna bata cutar da makwabci. Domin haka, kauna tace cikar shari'a.
11 Saboda wannan, kun san lokaci yayi, ku farka daga barci. Domin cetonmu yana kusa fiye da yadda muke tsammani.
12 Dare yayi nisa, gari ya kusan wayewa. Don haka, sai mu rabu da ayyukan duhu, mu yafa makaman haske.
13 Sai muyi tafiya yadda ya kamata, kamar da rana, ba a cikin shashanci ko buguwa ba. Kada kuma muyi tafiya cikin fasikanci da muguwar sha'awa, ba kuma cikin husuma ko kishi ba.
14 Amma ku yafa Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutumtaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.