< Romawa 10 >
1 'Yan'uwana, muradin zuciyata da dukkan addu'oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton.
Ἀδελφοί, ἡ μὲν εὐδοκία τῆς ἐμῆς καρδίας καὶ ἡ δέησις (ἡ *k*) πρὸς τὸν θεὸν ὑπὲρ (τοῦ *k*) (αὐτῶν *N(K)O*) (ἐστιν *k*) εἰς σωτηρίαν.
2 Domin na shaida game da su cewa suna da kwazo game da Allah, amma ba a kan sani ba.
μαρτυρῶ γὰρ αὐτοῖς ὅτι ζῆλον θεοῦ ἔχουσιν ἀλλ᾽ οὐ κατ᾽ ἐπίγνωσιν.
3 Don, ba su da sani akan adalcin Allah, suna kokarin tabbatar da adalcin kansu. Ba su bada kan su ga adalcin Allah ba.
ἀγνοοῦντες γὰρ τὴν τοῦ θεοῦ δικαιοσύνην καὶ τὴν ἰδίαν δικαιοσύνην ζητοῦντες στῆσαι τῇ δικαιοσύνῃ τοῦ θεοῦ οὐχ ὑπετάγησαν.
4 Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata.
Τέλος γὰρ νόμου Χριστὸς εἰς δικαιοσύνην παντὶ τῷ πιστεύοντι.
5 Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari'a: ''mutumin da ya aikata adalcin shari'a, zai rayu ta wurin wannan adalcin.''
Μωϋσῆς γὰρ γράφει τὴν δικαιοσύνην τὴν ἐκ τοῦ νόμου ὅτι ὁ ποιήσας αὐτὰ ἄνθρωπος ζήσεται ἐν (αὐτοῖς. *NK(O)*)
6 Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, ''Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?''(don ya sauko da Almasihu kasa).
Ἡ δὲ ἐκ πίστεως δικαιοσύνη οὕτως λέγει· μὴ εἴπῃς ἐν τῇ καρδίᾳ σου· τίς ἀναβήσεται εἰς τὸν οὐρανόν; τοῦτ᾽ ἔστιν Χριστὸν καταγαγεῖν·
7 Kada ku ce, ''Wa zai gangara zuwa kasa?'' (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu). (Abyssos )
ἢ τίς καταβήσεται εἰς τὴν ἄβυσσον; τοῦτ᾽ ἔστιν Χριστὸν ἐκ νεκρῶν ἀναγαγεῖν. (Abyssos )
8 Amma me yake cewa? “kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka.” Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa.
ἀλλὰ τί λέγει; ἐγγύς σου τὸ ῥῆμά ἐστιν ἐν τῷ στόματί σου καὶ ἐν τῇ καρδίᾳ σου· τοῦτ᾽ ἔστιν τὸ ῥῆμα τῆς πίστεως ὃ κηρύσσομεν·
9 Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.
ὅτι ἐὰν ὁμολογήσῃς (τὸ ῥῆμα *O*) ἐν τῷ στόματί σου (ὅτι *o*) (κύριον Ἰησοῦν *NK(o)*) καὶ πιστεύσῃς ἐν τῇ καρδίᾳ σου ὅτι ὁ θεὸς αὐτὸν ἤγειρεν ἐκ νεκρῶν, σωθήσῃ·
10 Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto.
καρδίᾳ γὰρ πιστεύεται εἰς δικαιοσύνην, στόματι δὲ ὁμολογεῖται εἰς σωτηρίαν.
11 Don nassi na cewa, ''Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba,''
Λέγει γὰρ ἡ γραφή· πᾶς ὁ πιστεύων ἐπ᾽ αὐτῷ οὐ καταισχυνθήσεται.
12 Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi.
οὐ γάρ ἐστιν διαστολὴ Ἰουδαίου τε καὶ Ἕλληνος· ὁ γὰρ αὐτὸς κύριος πάντων πλουτῶν εἰς πάντας τοὺς ἐπικαλουμένους αὐτόν.
13 Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto.
πᾶς γὰρ ὃς ἂν ἐπικαλέσηται τὸ ὄνομα κυρίου σωθήσεται.
14 To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba?
Πῶς οὖν (ἐπικαλέσωνται *N(k)O*) εἰς ὃν οὐκ ἐπίστευσαν; πῶς δὲ (πιστεύσωσιν *N(k)O*) οὗ οὐκ ἤκουσαν; πῶς δὲ (ἀκούσωσιν *N(k)O*) χωρὶς κηρύσσοντος;
15 Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa'azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa'azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, “Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!”
πῶς δὲ (κηρύξωσιν *N(k)O*) ἐὰν μὴ ἀποσταλῶσιν; (καθὼς *NK(o)*) γέγραπται· ὡς ὡραῖοι οἱ πόδες τῶν εὐαγγελιζομένων (εἰρήνην τῶν εὐαγγελιζομένων *K*) τὰ ἀγαθά.
16 Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, ''Ubangiji, wa ya gaskata da sakon?
ἀλλ᾽ οὐ πάντες ὑπήκουσαν τῷ εὐαγγελίῳ· Ἠσαΐας γὰρ λέγει· κύριε, τίς ἐπίστευσεν τῇ ἀκοῇ ἡμῶν;
17 Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu.
ἄρα ἡ πίστις ἐξ ἀκοῆς ἡ δὲ ἀκοὴ διὰ ῥήματος (Χριστοῦ. *N(K)O*)
18 Amma na ce, “ko basu ji ba ne? I, tabbas'' muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya.''
ἀλλὰ λέγω· μὴ οὐκ ἤκουσαν; μενοῦνγε εἰς πᾶσαν τὴν γῆν ἐξῆλθεν ὁ φθόγγος αὐτῶν καὶ εἰς τὰ πέρατα τῆς οἰκουμένης τὰ ῥήματα αὐτῶν.
19 yau, na ce, ''Ko Isra'ila basu sani ba ne?'' Da farko Musa ya ce, “Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al'umma ba. Abin da nake nufi nan shine al'ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali.''
ἀλλὰ λέγω· μὴ Ἰσραὴλ οὐκ ἔγνω; πρῶτος Μωϋσῆς λέγει· ἐγὼ παραζηλώσω ὑμᾶς ἐπ᾽ οὐκ ἔθνει ἐπ᾽ ἔθνει ἀσυνέτῳ παροργιῶ ὑμᾶς.
20 Amma Ishaya da karfin hali ya ce, ''Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba.
Ἠσαΐας δὲ ἀποτολμᾷ καὶ λέγει· εὑρέθην (ἐν *no*) τοῖς ἐμὲ μὴ ζητοῦσιν, ἐμφανὴς ἐγενόμην (ἐν *o*) τοῖς ἐμὲ μὴ ἐπερωτῶσιν.
21 ''Amma ga Isra'ila kam ya ce, '' na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai.''
πρὸς δὲ τὸν Ἰσραὴλ λέγει· ὅλην τὴν ἡμέραν ἐξεπέτασα τὰς χεῖράς μου πρὸς λαὸν ἀπειθοῦντα καὶ ἀντιλέγοντα.