< Romawa 1 >
1 Bulus, bawan Yesu Almasihu, kirayayye ya zama manzo, kuma kebabbe domin bisharar Allah.
2 Wannan itace bisharar da ya alkawarta tuntuni ta wurin annabawansa ta wurin tsarkakakkun littattafan sa.
3 Game da Dansa ne, haifaffe daga zuriyar Dauda ga zancen jiki.
4 Ta wurin tashinsa daga mattatu aka aiyana shi ya zama Dan Allah ta wurin ikon Ruhu na tsarkakewa. Yesu Almasihu Ubangijimu.
5 Ta wurinsa muka karbi alheri da manzanci sabo da biyayyar imani a cikin dukkan al'ummai, domin darajar sunansa.
6 cikin wadannan al'ummai kwa, ku ma an kiraku ku zama na Yesu Almasihu.
7 Wannan wasika ga dukkanku ne da kuke cikin Roma, kaunatattu na Allah, kirayayyun mutane tsarkakakku. Bari alheri ya kasance tare daku, da salama daga Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
8 Abu na farko dai ina yi wa Allah na godiya ta wurin Yesu Almasihu domin ku duka, domin kuwa ana labarta bangaskiyarku ko ina a cikin dukkan duniya.
9 Domin kuwa Allah shi ne shaida ta, wanda nake bautawa a cikin ruhuna a cikin bisharar Dansa, yadda a koyaushe na ke ambaton ku.
10 A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah.
11 Gama ina marmarin ganin ku, domin in baku wata baiwa ta ruhaniya, domin in karfafa ku.
12 Wato ina dokin in sami cikakkiyar karfafawa a cikin ku, ta wurin bangaskiyar junanmu, wato tawa da taku.
13 Yanzu fa bana so ku rasa sani, yan'uwa, sau da yawa nake yin niyyar zuwa wurinku, amma har yanzu hakan din bata samu ba. Na so yin hakan din ne don in sami 'ya'ya na ruhu a cikinku kamar dai yadda ya ke a sauran Al'ummai.
14 Ina dauke da nawayar Hellinawa da ta sauran jama'a, masu hikima da marasa hikima.
15 Don a shirye na ke in sanar da bishara a gare ku, ku da kuke cikin Roma.
16 Don kuwa ni ba na jin kunyar yin bishara, don ita ce ikon Allah don samun ceto ga duk wanda ya gaskata, da farko dai Yahudawa kana kuma Hellinawa,
17 Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, “Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya.”
18 Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su.
19 Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri.
20 Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja. (aïdios )
21 Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta.
22 Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye.
23 Sun musanya daukakar Allah madawwami da ta kamannin abubuwan da basa dawwama, kamar mutum, da tsuntsaye, da dabbobi masu kafafu hurhudu, da masu jan ciki.
24 Saboda haka Allah ya bashe su ga sha'awoyin kazantar zukatansu, su wulakantar da jukunansu a junansu.
25 Sune suka musanya gaskiyar Allah da karya, Kuma suke sujada da bauta ga halittaccen abu, maimakon Mahaliccin, Wanda yake abin yabo har abada. Amin. (aiōn )
26 Saboda haka Allah ya bashe su, ga sha'awowin su na lalata da wulakanci, har matansu suka canza ka'idar jima'i da aka saba zuwa madigo mace da mace.
27 Mazajensu ma suka sauya ka'idar jima'i tsakanin mace da miji zuwa namiji da namiji suna yin aikin lalata. Maza su na kwana da maza suna aikata aikin ban kyama, suna kuwa girbe sakamakon aiknsu na ban kyama.
28 Tunda shike ba su amince da Allah a cikkin al'amuransu ba, Allah ya bashe su ga bataccen hankalinsu, su aikata wadannan munanan abubuwa.
29 Suna cike da dukkan rashin adalci, mugunta, kyashi, keta, kuma cike da kishi, kisan kai, tarzoma, makirci, da kuma munanan manufafofi.
30 Masu gulma da kage, makiyan Allah. Masu tada zaune tsaye, masu taurin kai, da ruba, masu kaga kowadanne miyagun abubuwa, kuma masu kin yin biyayya ga iyayensu.
31 Masu duhun zuciya; masu cin amana, marasa soyayya, da kuma rashin tausayi.
32 Suna sane da tsarin Allah cewa masu yin irin wadannan al'amura sun cancanci hukuncin mutuwa. Ba kuwa yin wadannan abubuwan ka dai suke yi ba, harma goyon bayan masu yinsu suke yi.