< Ru’uya ta Yohanna 1 >
1 Wannan shine wahayin Yesu Almasihu da Allah ya bashi ya nuna wa bayinsa abinda zai faru ba da dadewa ba. Ya bayyana wannan ta wurin aiko da mala'ikansa ga bawansa Yahaya.
예수 그리스도의 계시라 이는 하나님이 그에게 주사 반드시 속히 될 일을 그 종들에게 보이시려고 그 천사를 그 종 요한에게 보내어 지시하신 것이라
2 Yahaya yayi shaida akan abinda ya gani game da maganar Allah da kuma shaidar da aka bayar game da Yesu Almasihu.
요한은 하나님의 말씀과 예수 그리스도의 증거 곧 자기의 본 것을 다 증거하였느니라
3 Mai albarka ne wanda ke karanta littafin nan da murya mai karfi, da kuma wadanda ke sauraron kalmomin wannan annabci kuma suke biyayya da abinda aka rubuta a ciki, domin kuwa lokaci ya kusato.
이 예언의 말씀을 읽는 자와 듣는 자들과 그 가운데 기록한 것을 지키는 자들이 복이 있나니 때가 가까움이라
4 Ni Yahaya, zuwa ga ikilisiyoyi bakwai na kasar Asiya: alheri zuwa gare ku da salama daga wanda ke yanzu, wanda ya kuma kasance a da, shi ne kuma mai zuwa nan gaba, kuma daga ruhohin nan bakwai da ke gaban kursiyinsa,
요한은 아시아에 있는 일곱 교회에 편지하노니 이제도 계시고 전에도 계시고 장차 오실 이와 그 보좌 앞에 일곱 영과
5 kuma daga Yesu Almasihu, wanda ke amintaccen mashaidi, dan fari na tashi daga cikin matattu, kuma mai mulkin sarakunan duniya. Ga wanda ya ke kaunar mu ya kuma kwance mu daga daurin zunubanmu ta wurin jininsa,
또 충성된 증인으로 죽은 자들 가운데서 먼저 나시고 땅의 임금들의 머리가 되신 예수 그리스도로 말미암아 은혜와 평강이 너희에게 있기를 원하노라 우리를 사랑하사 그의 피로 우리 죄에서 우리를 해방하시고
6 ya maishe mu masu mulki, firistoci na Allahnsa da Ubansa - daukaka da iko su tabbata gare shi har abada abadin, Amin. (aiōn )
그 아버지 하나님을 위하여 우리를 나라와 제사장으로 삼으신 그에게 영광과 능력이 세세토록 있기를 원하노라 아멘 (aiōn )
7 Duba yana zuwa tare da gizagizai, kowane ido zai gan shi, har ma da wadanda suka soke shi. Haka kuma dukkan kabilun duniya za su yi makoki saboda da shi. I, Amin.
볼지어다, 구름을 타고 오시리라 각인의 눈이 그를 보겠고 그를 찌른 자들도 볼 터이요 땅에 있는 모든 족속이 그를 인하여 애곡하리니 그러하리라 아멘
8 “Nine na farko da na karshe”, in ji Ubangiji Allah, “Wanda yake shine a yanzu, shine wanda ya kasance a da, kuma shi ne mai zuwa nan gaba, Mai iko duka.”
주 하나님이 가라사대 나는 알파와 오메가라 이제도 있고 전에도 있었고 장차 올 자요 전능한 자라 하시더라
9 Ni, Yahaya- dan'uwan ku da wanda ke tarayya daku cikin shan wahala, da mulki da tsawon jimrewa wadanda ke cikin Yesu - ina tsibirin da ake kira Batmusa saboda maganar Allah da kuma shaida game da Yesu.
나 요한은 너희 형제요 예수의 환난과 나라와 참음에 동참하는 자라 하나님의 말씀과 예수의 증거를 인하여 밧모라 하는 섬에 있었더니
10 Ina cikin Ruhu a ranar Ubangiji. Sai naji wata murya mai karfi a baya na kamar ta kaho.
주의 날에 내가 성령에 감동하여 내 뒤에서 나는 나팔소리 같은 큰 음성을 들으니
11 Ta ce, “Rubuta abinda ka gani a cikin littafi, ka kuma aika wa ikilisiyoyin nan bakwai - ga Afisus, ga Simirna, ga Birgamas, ga Tayatira, ga Sardisu, ga Filadalfiya, da kuma ga Laudikiya.”
가로되 너 보는 것을 책에 써서 에베소, 서머나, 버가모, 두아디라, 사데, 빌라델비아, 라오디게아 일곱 교회에 보내라 하시기로
12 Na juya don in ga wanda muryarsa ke magana da ni, da na juya sai na ga fitilu bakwai akan madorin su
몸을 돌이켜 나더러 말한 음성을 알아 보려고 하여 돌이킬 때에 일곱 금촛대를 보았는데
13 A tsakiyar fitilun akwai wani mai kama da dan mutum, yana sanye da doguwar tufa har tafin sawunsa, da damara ta zinariya kewaye a kirjinsa.
촛대 사이에 인자 같은 이가 발에 끌리는 옷을 입고 가슴에 금띠를 띠고
14 Kansa da gashinsa fari fat kamar auduga - kamar dusar kankara, kuma idanun sa kamar harshen wuta.
그 머리와 털의 희기가 흰 양털같고 눈 같으며 그의 눈은 불꽃 같고
15 Kafaffunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar tagullar da aka tace da wutar makera, muryar sa kuma kamar kugin ambaliyar ruwan teku ne.
그의 발은 풀무에 단련한 빛난 주석 같고 그의 음성은 많은 물소리와 같으며
16 A hannunsa na dama yana rike da taurari bakwai, daga bakinsa kuma kakkaifan takobi mai kaifi biyu ke fitowa. Fuskarsa tana haskakawa kamar sa'adda rana ke haskakawa kwarai.
그 오른손에 일곱 별이 있고 그 입에서 좌우에 날선 검이 나오고 그 얼굴은 해가 힘있게 비취는 것 같더라
17 Lokacin da na gan shi, na fadi kamar mataccen mutum a kafaffunsa. Ya dora hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Nine na farko da na karshe,
내가 볼 때에 그 발 앞에 엎드러져 죽은 자같이 되매 그가 오른손을 내게 얹고 가라사대 두려워 말라 나는 처음이요 나중이니
18 da kuma wanda ke raye. Na mutu, amma duba ina raye har abada! Kuma ina da mabudin mutuwa da na hades. (aiōn , Hadēs )
곧 산 자라 내가 전에 죽었었노라 볼지어다 이제 세세토록 살아 있어 사망과 음부의 열쇠를 가졌노니 (aiōn , Hadēs )
19 Domin haka ka rubuta abinda ka gani, abin da ke yanzu, da abin da zai faru bayan wanan.
그러므로 네 본 것과 이제 있는 일과 장차 될 일을 기록하라
20 Akan boyayyar ma'ana game da taurari bakwai da ka gani a hannun dama na, da madorin fitilu bakwai na zinariya: Taurarin nan bakwai mala'iku ne na ikilisiyoyi bakwai, kuma madorin fitilun nan bakwai ikilisiyoyi ne bakwai.
네 본 것은 내 오른손에 일곱 별의 비밀과 일곱 금 촛대라 일곱 별은 일곱 교회의 사자요 일곱 촛대는 일곱 교회니라