< Ru’uya ta Yohanna 9 >
1 Sa'annan mala'ika na biyar ya busa kahonsa. Na ga tauraro daga sama da ya fado zuwa duniya. An ba tauraron nan mabudin hanyar rami marar iyaka. (Abyssos )
And the fifth angel sounded; and I saw a star fall from heaven to the earth; and there was given to him the key of the pit of the abyss; (Abyssos )
2 Ya bude hanyar rami marar iyaka, sai hayaki ya fito daga kofar kamar hayaki daga babban ramin wuta. Rana da iska suka juya duhu, sabili da hayakin da ke fitowa daga kofar ramin. (Abyssos )
and he opened the pit of the abyss; and there arose a smoke out of the pit, like the smoke of a great furnace; and the sun and the air were darkened by the smoke of the pit. (Abyssos )
3 Daga cikin hayakin kuwa sai ga fari sun fito zuwa duniya, aka ba su iko kamar na kunamai cikin duniya.
And out of the smoke there came locusts upon the earth; and power was given to them, as the scorpions of the earth have power.
4 Aka gaya masu kada su yi wa ciyayi da kowanne koren ganye ko itace illa, sai dai mutanen da basu da hatimin Allah a goshinsu.
And they were commanded not to hurt the grass of the earth, nor any green thing, nor any tree, but the men who have not the seal of God in their foreheads.
5 Ba a basu izini su kashe wadannan mutane ba, sai dai su azabtar da su na watani biyar. Zafinsu kuwa zai zama kamar na cizon kunama idan ta harbi mutum.
And they were permitted, not to kill them, but to torment them five months; and the torment inflicted by them was like the torment inflicted by a scorpion, when he stings a man.
6 A kwanakin nan mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba. Za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za ta guje su.
And in those days men will seek for death, and shall not find it; and they will desire to die, and death shall flee from them.
7 Farin kuwa suna kama da dawakai da aka shirya domin yaki. A bisa kansu akwai wani abu kamar rawanan zinariya, fuskokinsu kuma kamar na 'yan adam.
And the shapes of the locusts were like horses prepared for battle; and on their heads were, as it were, crowns of gold; and their faces were like the faces of men.
8 Gashinsu kuma kamar na mata yake, hakoransu kamar hakoran zaki.
And they had hair like the hair of women; and their teeth were like the teeth of lions.
9 Sulkunansu kuma kamar na karfe, karar fikafikansu kuma kamar karar kekunan dawakin yaki masu yawa da dawakai da aka shirya domin zuwa yaki.
And they had breastplates like breastplates of iron; and the sound of their wings was like the sound of chariots of many horses running to battle.
10 Suna da wutsiya da kari kamar kunamai; A wutsiyar su kuma suna da ikon da zai azabtar da mutane na tsawon wata biyar.
And they had tails like scorpions, and there were stings in their tails; and they had power to hurt men five months.
11 Suna da wani kamar sarki a kansu, mala'ikan rami marar iyaka. Sunansa da Ibraniyanci Abadon, da Helenanci kuma Afoliyon. (Abyssos )
And they had over them a king, the angel of the abyss: his name, in Hebrew, is Abaddon, and, in Greek, he has the name Apollyon. (Abyssos )
12 Bala'i na fari ya wuce. Duba! Bayan wannan akwai masifu guda biyu masu zuwa.
The first woe is past: behold, there are coming, after this, two woes more.
13 Mala'ika na shida ya busa kahonsa, sai na ji murya daga kahonin bagadin zinariya da ke gaban Allah.
And the sixth angel sounded: and I heard a voice from the four horns of the golden altar that is before God,
14 Muryar ta ce wa mala'ika na shida da ke rike da kahon, “Kwance mala'ikun nan hudu da ke daure a babban kogin Yufiretis,''
saying to the sixth angel, who had the trumpet: Loose the four angels that are bound at the great river Euphrates.
15 Mala'iku hudun da aka shirya domin wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da kuma wannan shekara, aka sake su su kashe daya bisa uku na 'yan adam.
And the four angels were loosed, who were prepared for an hour, and a day, and a month, and a year, to slay the third part of men.
16 Yawan sojoji da ke kan dawakai shine 200, 000, 000. Na ji adadin su.
And the number of the armies of horsemen was two myriads of myriads: I heard the number of them.
17 Haka na ga dawakan a cikin wahayina da mahayansu: Sulkunansu jawur kamar wuta, bakin shudi, da kuma ruwan doruwa. Kawunan dawakan suna kama da na zakuna, daga bakunansu kuma wuta, da hayaki da farar wuta suka fito.
And thus I saw the horses in the vision, and those who sat on them; they had breastplates, fiery, and hyacinthine, and sulphurous: and the heads of the horses were like the heads of lions, and out of their mouths issued fire and smoke and brimstone.
18 Aka kashe daya bisa uku na mutane ta annoban nan uku: wuta, hayaki da farar wuta da suka fito daka bakunansu.
By these three plagues was the third part of men killed, by the fire, and the smoke, and the brimstone that issued out of their mouths.
19 Domin iko na dawakan na bakunansu da wutsiyoyinsu - domin wutsiyoyinsu suna kama da macizai, kuma suna da kawuna wadanda dasu suke ji wa mutane rauni.
For their power was in their mouth and in their tails; for their tails were like serpents, and had heads, and with them they do injury.
20 Sauran 'yan adam, da ba a kashe su ta wannan annoba ba, basu tuba daga ayyukan da suka yi ba. Basu kuma daina bautar aljanu da gumakan zinariya, da azurfa, da tagulla, da dutse, da itace ba - abubuwan da ba su gani, ji, ko tafiya.
And the rest of men that were not killed by these plagues, repented not of the works of their hands, that they might not worship demons, and idols of gold, and of silver, and of brass, and of stone, and of wood, which can neither see, nor hear, nor walk;
21 Basu kuma tuba ba daga kisan kai, sihiri, fasikanci, ko kuma ayyukansu na sata ba.
and they repented not of their murders, nor of their sorceries, nor of their lewdness, nor of their thefts.