< Ru’uya ta Yohanna 6 >

1 Na duba lokacin da Dan Ragon ya bude daya daga cikin hatiman bakwai, sai na ji daya daga cikin rayayyun halittattun hudu ya fada da murya kamar tsawa, ''Zo!”
Then I saw the Lamb open one of the seven seals, and I heard one of the four living creatures say with a voice like thunder, “Come and see.”
2 Sai Na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa na rike da baka, kuma an bashi rawani. Ya fito a matsayin mai nasara domin ya yi nasara.
And behold, there was a white horse! Its rider had a bow, and he was given a crown and went out conquering and to conquer.
3 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na biyu, sai na ji rayayyen halitta na biyu ya ce, ''Zo!''
When the Lamb opened the second seal, I heard the second living creature say, “Come.”
4 Sai wani doki ya fito waje - jawur. Ga mahayin aka bashi dama ya dauke salama daga duniya, domin mutanen ta su karkashe juna. Wannan mahayin an bashi babbar takobi.
Then another horse came out, a fiery red one. Its rider was permitted to take peace from the earth, so that people would slay one another, and he was given a great sword.
5 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na uku, sai na ji rayayyen halita na uku ya ce, ''Zo!'' Na ga bakin doki, mai hawanta na rike da ma'auni a cikin hannunsa.
When the Lamb opened the third seal, I heard the third living creature say, “Come and see.” And behold, there was a black horse! Its rider had a balance scale in his hand.
6 Sai na ji kamar wata murya daga cikin rayayyun halittattun nan hudu ta ce, “Mudun alkama guda a kan albashin yini, kuma mudun sha'ir uku. Amma kar ka bata mai da kuma ruwan inabi.”
Then I heard a voice from among the four living creatures saying, “A measure of wheat for a denarius, and three measures of barley for a denarius, and do not damage the oil and wine.”
7 Da Dan Ragon ya bude hatimi na hudu, na ji muryar rayayyen halitta na hudu ya ce, ''Zo!''
When the Lamb opened the fourth seal, I heard the fourth living creature say, “Come and see.”
8 Sai na ga wani doki ruwan toka. Mai hawansa an bashi suna mutuwa, hades kuma tana biye da shi. An basu iko bisa kashi hudu na duniya su kashe da takobi, yunwa, cututtuka, da kuma namomin jeji na duniya. (Hadēs g86)
And behold, there was a pale green horse! The name of its rider was Death, and Hades followed him. He was given authority over a fourth of the earth to kill by the sword, by famine and pestilence, and by the wild beasts of the earth. (Hadēs g86)
9 Da Dan Ragon ya bude hatimi na biyar, a karkashin bagadi sai na ga rayukan wadanda aka kashe saboda maganar Allah, da kuma shaidar da suka rike.
When the Lamb opened the fifth seal, I saw under the altar the souls of those who had been slain because of the word of God and because of the testimony of the Lamb which they had upheld.
10 Suka yi kuka da babban murya, ''Sai yaushe ya mai iko duka, Mai Tsarki da gaskiya, zaka shari'anta mazaunan duniya, ka kuma dauki fansar jininmu?
They cried out with a loud voice, “How long, O Master, Holy and True, will yoʋ not judge and avenge our blood on those who dwell on the earth?”
11 Sai kowanne dayan su aka bashi farar tufa aka kuma fada masu su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su da kuma 'yan'uwansu maza da mata wadanda aka kashe ya cika, kamar yadda aka kashe su.
They were each given a white robe and told to rest a while longer, until their fellow servants and their brothers, who were about to be killed just as they had been, should complete their course.
12 Da Dan Ragon ya bude hatimi na shidan, ina kallo sai ga babbar girgizar kasa. Rana ta zama baki kirin kamar bakar tufa, wata kuma ya zama kamar jini.
Then I watched as the Lamb opened the sixth seal, and there was a great earthquake. The sun became as black as sackcloth made of goat hair, the entire moon became like blood,
13 Taurarin sama suka fado kasa, kamar yadda itacen baure ke karkade 'ya'yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ta kada.
and the stars of the sky fell to the earth like a fig tree dropping its unripe figs when it is shaken by a strong wind.
14 Sama kuma ta bace kamar takardar da aka nannade. Kowanne dutse da tsibiri aka kau da shi daga wurinsa.
The sky was split apart like a scroll being rolled up, and every mountain and island was removed from its place.
15 Sai sarakan duniya da muhimman mutane da sarakunan yaki, attajirai, da masu iko, tare da kowanne mutum, bawa da 'yantacce suka boye cikin duwatsu da tsaunuka.
Then the kings of the earth, the magnates, the commanders, the rich, the mighty, and every slave and free man hid themselves in the caves and among the rocks of the mountains.
16 Suka ce wa tsaunuka da duwatsu, “Ku fado bisan mu! Ku boye mu daga fuskar wanda yake zaune bisa kursiyin da kuma fushin Dan Ragon.
And they said to the mountains and rocks, “Fall on us, and hide us from the face of him who sits on the throne and from the wrath of the Lamb,
17 Domin babban ranar fushin sa ta zo. Wa zai iya tsayawa?''
for the great day of his wrath has come, and who can withstand it?”

< Ru’uya ta Yohanna 6 >