< Ru’uya ta Yohanna 4 >
1 Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga budaddiyar kofa a sama. Muryar fari da na ji kamar kakaki, na cewa hauro in nuna maka abubuwan da dole za su faru bayan wadannan al'amura.”
Μετὰ ταῦτα εἶδον, καὶ ἰδοὺ θύρα ἠνεῳγμένη ἐν τῷ οὐρανῷ, καὶ ἡ φωνὴ ἡ πρώτη ἣν ἤκουσα ὡς σάλπιγγος λαλούσης μετʼ ἐμοῦ, λέγων· Ἀνάβα ὧδε, καὶ δείξω σοι ἃ δεῖ γενέσθαι. μετὰ ταῦτα
2 Nan da nan ina cikin Ruhu, sai na ga wani kursiyin da aka ajiye shi a sama, da wani zaune bisansa.
⸀εὐθέωςἐγενόμην ἐν πνεύματι· καὶ ἰδοὺ θρόνος ἔκειτο ἐν τῷ οὐρανῷ, καὶ ἐπὶ τὸν θρόνον καθήμενος,
3 Shi da ke zaune a kan tana da kamanin yasfa da yakutu. Akwai Bakangizo kewaye da kursiyin kamanin bakangizon kuwa zumurudu.
⸂καὶ ὁ καθήμενος ὅμοιος ὁράσει λίθῳ ἰάσπιδι καὶ σαρδίῳ, καὶ ἶρις κυκλόθεν τοῦ θρόνου ⸂ὅμοιος ὁράσει σμαραγδίνῳ.
4 A kewaye da kursiyin kuwa akwai kursiyoyi ashirin da hudu, masu zama bisa kursiyoyin nan kuwa dattawa ne ashirin da hudu, sanye da fararen tufafi, da kambunan zinariya bisa kawunansu.
καὶ κυκλόθεν τοῦ θρόνου ⸀θρόνοιεἴκοσι τέσσαρες, καὶ ἐπὶ τοὺς ⸀θρόνουςεἴκοσι τέσσαρας πρεσβυτέρους καθημένους περιβεβλημένους ⸀ἐνἱματίοις λευκοῖς, καὶ ἐπὶ τὰς κεφαλὰς αὐτῶν στεφάνους χρυσοῦς.
5 Daga kursiyin walkiya na ta fitowa, cida, da karar aradu. Fitilu bakwai na ci a gaban kursiyin, fitilun sune ruhohin Allah guda bakwai.
καὶ ἐκ τοῦ θρόνου ἐκπορεύονται ἀστραπαὶ καὶ φωναὶ καὶ βρονταί· καὶ ἑπτὰ λαμπάδες πυρὸς καιόμεναι ἐνώπιον τοῦ θρόνου, ⸀ἅεἰσιν ⸀τὰἑπτὰ πνεύματα τοῦ θεοῦ,
6 Gaban kursiyin akwai tekun gilashi, mai haske kamar karau. A tsakiyar kursiyin da kewayen kursiyin akwai rayayyun hallitu guda hudu cike da idanu gaba da baya.
καὶ ἐνώπιον τοῦ θρόνου ὡς θάλασσα ὑαλίνη ὁμοία κρυστάλλῳ. Καὶ ἐν μέσῳ τοῦ θρόνου καὶ κύκλῳ τοῦ θρόνου τέσσαρα ζῷα γέμοντα ὀφθαλμῶν ἔμπροσθεν καὶ ὄπισθεν·
7 Rayayyen hallitta na farko na da kamanin zaki, rayayyen hallitta na biyun kamanin dan maraki ne, rayayyen hailitta na uku fuskar sa kamar dan adam, kuma rayayyen hallitta ta hudu na da kamanin gaggafa mai tashi.
καὶ τὸ ζῷον τὸ πρῶτον ὅμοιον λέοντι, καὶ τὸ δεύτερον ζῷον ὅμοιον μόσχῳ, καὶ τὸ τρίτον ζῷον ⸀ἔχων⸂τὸ πρόσωπον ὡς ἀνθρώπου, καὶ τὸ τέταρτον ζῷον ὅμοιον ἀετῷ πετομένῳ·
8 Dukan rayayyun hallittan nan hudu na da fukafukai shida shida, cike da idanu a bisa da karkashin fukafukan. Dare da rana ba sa daina cewa, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne Ubangiji Allah, mai iko duka, shine da shine yanzu shine mai zuwa.”
καὶ τὰ τέσσαρα ζῷα, ἓν ⸂καθʼ ἓν ⸀αὐτῶν⸀ἔχωνἀνὰ πτέρυγας ἕξ, κυκλόθεν καὶ ἔσωθεν γέμουσιν ὀφθαλμῶν· καὶ ἀνάπαυσιν οὐκ ἔχουσιν ἡμέρας καὶ νυκτὸς λέγοντες· Ἅγιος ἅγιος ἅγιος κύριος, ὁ θεός, ὁ παντοκράτωρ, ὁ ἦν καὶ ὁ ὢν καὶ ὁ ἐρχόμενος.
9 A dukan lokacin da rayayyun hallittun nan suke ba da girma, daukaka, da godiya ga shi da ke zaune bisa kursiyin, wanda ke raye har abada abadin, (aiōn )
καὶ ὅταν ⸀δώσουσιντὰ ζῷα δόξαν καὶ τιμὴν καὶ εὐχαριστίαν τῷ καθημένῳ ἐπὶ ⸂τῷ θρόνῳ, τῷ ζῶντι εἰς τοὺς αἰῶνας τῶν αἰώνων, (aiōn )
10 sai dattawan nan ashirin da hudu suka fadi da fuskokinsu a kasa gaban shi da ke zaune bisa kursiyin. Suka yi sujada ga shi da ke rayuwa har abada abadin, suna jefar da kambinsu a gaban kursiyin, suna cewa, (aiōn )
πεσοῦνται οἱ εἴκοσι τέσσαρες πρεσβύτεροι ἐνώπιον τοῦ καθημένου ἐπὶ τοῦ θρόνου, καὶ προσκυνήσουσιν τῷ ζῶντι εἰς τοὺς αἰῶνας τῶν αἰώνων, καὶ βαλοῦσιν τοὺς στεφάνους αὐτῶν ἐνώπιον τοῦ θρόνου, λέγοντες· (aiōn )
11 “Ka cancanta, ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka karbi yabo da daukaka da iko. Domin kai ka hallicci dukan komai, da kuma nufinka ne, suka kasance aka kuma hallicce su.
Ἄξιος εἶ, ὁ κύριος καὶ ὁ θεὸς ⸀ἡμῶν λαβεῖν τὴν δόξαν καὶ τὴν τιμὴν καὶ τὴν δύναμιν, ὅτι σὺ ἔκτισας ⸀τὰπάντα, καὶ διὰ τὸ θέλημά σου ἦσαν καὶ ἐκτίσθησαν.