< Ru’uya ta Yohanna 2 >
1 ''Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Afisus, ka rubuta: 'Wadannan sune kalmomin wanda ke rike da taurari bakwai a cikin hannun damarsa. wanda yake tafiya a tsakanin zankayen fitilun zinari bakwai,
Τῷ ἀγγέλῳ ⸀τῆςἐν Ἐφέσῳ ἐκκλησίας γράψον· Τάδε λέγει ὁ κρατῶν τοὺς ἑπτὰ ἀστέρας ἐν τῇ δεξιᾷ αὐτοῦ, ὁ περιπατῶν ἐν μέσῳ τῶν ἑπτὰ λυχνιῶν τῶν χρυσῶν·
2 ''Na san abubuwan da ka yi, da famar ka, da hakurinka da jimirinka. Na sani ba ka jimrewa miyagun mutane, na sani ka gwada wadanda suka ce da kansu, su manzanni ne, amma ba haka ba, ka tarar da su makaryata.
Οἶδα τὰ ἔργα σου, καὶ τὸν ⸀κόπονκαὶ τὴν ὑπομονήν σου, καὶ ὅτι οὐ δύνῃ βαστάσαι κακούς, καὶ ἐπείρασας τοὺς λέγοντας ἑαυτοὺς ⸀ἀποστόλους καὶ οὐκ εἰσίν, καὶ εὗρες αὐτοὺς ψευδεῖς·
3 Na san kana da tsawon jimrewa, kuma ka sha wahala sosai sabili da sunana, kuma baka gaji ba.
καὶ ὑπομονὴν ἔχεις, καὶ ἐβάστασας διὰ τὸ ὄνομά μου, καὶ ⸂οὐ κεκοπίακες.
4 Amma ga rashin jin dadi na da kai, ka bar kaunar ka ta fari.
ἀλλὰ ἔχω κατὰ σοῦ ὅτι τὴν ἀγάπην σου τὴν πρώτην ἀφῆκες.
5 Domin haka ka tuna daga inda ka fadi. Ka tuba ka yi abubuwan da ka yi da fari. Sai fa ka tuba, zan zo maka in kuma cire fitilar ka daga mazauninta.
μνημόνευε οὖν πόθεν ⸀πέπτωκας καὶ μετανόησον καὶ τὰ πρῶτα ἔργα ποίησον· εἰ δὲ μή, ἔρχομαί ⸀σοι καὶ κινήσω τὴν λυχνίαν σου ἐκ τοῦ τόπου αὐτῆς, ἐὰν μὴ μετανοήσῃς.
6 Amma kana da wannan: Ka tsani abubuwan da Nikolatawa suka yi, wanda nima na tsana.
ἀλλὰ τοῦτο ἔχεις ὅτι μισεῖς τὰ ἔργα τῶν Νικολαϊτῶν, ἃ κἀγὼ μισῶ.
7 wanda yake da kunnen ji ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bashi dama ya ci daga itacen rai, wanda ke cikin firdausin Allah.””
ὁ ἔχων οὖς ἀκουσάτω τί τὸ πνεῦμα λέγει ταῖς ἐκκλησίαις. τῷ νικῶντι δώσω αὐτῷ φαγεῖν ἐκ τοῦ ξύλου τῆς ζωῆς, ὅ ἐστιν ἐν τῷ παραδείσῳ τοῦ ⸀θεοῦ
8 Zuwa ga mala'ikan da ke Ikilisiliyar Samirna rubuta: 'Wadannan su ne kalmomin wanda yake shine farko shine karshe, wanda ya mutu ya sake rayuwa kuma.
Καὶ τῷ ἀγγέλῳ ⸀τῆςἐν Σμύρνῃ ἐκκλησίας γράψον· Τάδε λέγει ὁ πρῶτος καὶ ὁ ἔσχατος, ὃς ἐγένετο νεκρὸς καὶ ἔζησεν·
9 ''Na san wahalun ka da talaucin ka amma kana da arziki. Nasan masu bata suna wadanda suke cewa su Yahudawa ne, amma ba haka suke ba. Su majami'ar Shaidan ne.
Οἶδά ⸀σουτὴν θλῖψιν καὶ τὴν πτωχείαν, ἀλλὰ πλούσιος εἶ, καὶ τὴν βλασφημίαν ἐκ τῶν λεγόντων Ἰουδαίους εἶναι ἑαυτούς, καὶ οὐκ εἰσίν, ἀλλὰ συναγωγὴ τοῦ Σατανᾶ.
10 Kada ka ji tsoron wahalar da zaka fuskanta nan gaba. Duba! Shaidan yana gab da jefa wadansun ku cikin kurkuku, domin a gwada ku, kuma zaku sha wahala ta kwana goma. Kuyi aminci har ga mutuwa zan baku rawanin rai.
⸀μηδὲνφοβοῦ ἃ μέλλεις ⸀πάσχειν ⸀ἰδοὺμέλλει ⸀βάλλεινὁ διάβολος ἐξ ὑμῶν εἰς φυλακὴν ἵνα πειρασθῆτε, καὶ ⸀ἕξετεθλῖψιν ἡμερῶν δέκα. γίνου πιστὸς ἄχρι θανάτου, καὶ δώσω σοι τὸν στέφανον τῆς ζωῆς.
11 wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Shi wanda yayi nasara ba zai cutu a mutuwa ta biyu ba.””
ὁ ἔχων οὖς ἀκουσάτω τί τὸ πνεῦμα λέγει ταῖς ἐκκλησίαις. ὁ νικῶν οὐ μὴ ἀδικηθῇ ἐκ τοῦ θανάτου τοῦ δευτέρου.
12 ''Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Burgamas rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda ya ke da takobi mai kaifi biyu;
Καὶ τῷ ἀγγέλῳ τῆς ἐν Περγάμῳ ἐκκλησίας γράψον· Τάδε λέγει ὁ ἔχων τὴν ῥομφαίαν τὴν δίστομον τὴν ὀξεῖαν·
13 ''Na san inda kake zama can inda kursiyin shaidan yake. Duk da haka ka rike sunana da karfi, na sani baka yi musun bangaskiyar ka da ni ba, ko a lokacin Antifas mashaidina, amintaccena, wanda aka kashe a tsakaninku, can inda shaidan yake zama.
⸀Οἶδαποῦ κατοικεῖς, ὅπου ὁ θρόνος τοῦ Σατανᾶ, καὶκρατεῖς τὸ ὄνομά μου, καὶ οὐκ ἠρνήσω τὴν πίστιν μου ⸀καὶ ἐν ταῖς ⸀ἡμέραιςἈντιπᾶς, ὁ μάρτυς μου ὁ πιστός ⸀μου, ὃς ἀπεκτάνθη παρʼ ὑμῖν, ὅπου ὁ Σατανᾶς κατοικεῖ.
14 Amma ga rashin jin dadi na kadan da kai: Kana da wadansu da suke rike da koyarwar Bil'amu kamkam, wanda ya koya wa Balak ya sa abin tuntubi gaban 'ya'yan Isra'ila, domin su ci abincin da aka mika wa gumaka kuma suyi fasikanci.
ἀλλὰ ἔχω κατὰ σοῦ ὀλίγα, ὅτι ἔχεις ἐκεῖ κρατοῦντας τὴν διδαχὴν Βαλαάμ, ὃς ⸂ἐδίδασκεν τῷ Βαλὰκ βαλεῖν σκάνδαλον ἐνώπιον τῶν υἱῶν Ἰσραήλ, ⸀φαγεῖνεἰδωλόθυτα καὶ πορνεῦσαι·
15 Hakannan kuma wasunku sun rike koyarwar Nikolatawa kamkam.
οὕτως ἔχεις καὶ σὺ κρατοῦντας τὴν ⸀διδαχὴνΝικολαϊτῶν ὁμοίως.
16 Sabili da haka ka tuba! Idan ka ki zan zo gare ka da sauri, kuma in yi yaki gaba da su da takobi dake cikin bakina.
μετανόησον οὖν· εἰ δὲ μή, ἔρχομαί σοι ταχύ, καὶ πολεμήσω μετʼ αὐτῶν ἐν τῇ ῥομφαίᾳ τοῦ στόματός μου.
17 Bari wanda yake da kunne ya sauriri abin da Ruhu yake fadawa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bada wata boyayyar manna, kuma zan bashi farin dutse da sabon suna a rubuce a kan dutsen, suna wanda ba wanda ya sani, sai shi wanda ya karbe shi.””
ὁ ἔχων οὖς ἀκουσάτω τί τὸ πνεῦμα λέγει ταῖς ἐκκλησίαις. τῷ νικῶντι δώσω ⸀αὐτῷτοῦ μάννα τοῦ κεκρυμμένου, καὶ δώσω αὐτῷ ψῆφον λευκήν, καὶ ἐπὶ τὴν ψῆφον ὄνομα καινὸν γεγραμμένον ὃ οὐδεὶς οἶδεν εἰ μὴ ὁ λαμβάνων.
18 Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Tiyatira rubuta: 'Wadannan sune kalamomin Dan Allah, wanda yake da idanu kamar harshen wuta; sawayen kamar gogaggiyar tagulla:
Καὶ τῷ ἀγγέλῳ ⸀τῆςἐν Θυατείροις ἐκκλησίας γράψον· Τάδε λέγει ὁ υἱὸς τοῦ θεοῦ, ὁ ἔχων τοὺς ὀφθαλμοὺς αὐτοῦ ὡς φλόγα πυρός, καὶ οἱ πόδες αὐτοῦ ὅμοιοι χαλκολιβάνῳ·
19 ''Na san abin da ka yi, kaunar ka, da bangaskiya da hidima da tsawon jimrewar ka. Na san abinda ka yi bada dadewa ba ya fi abinda ka yi da fari.
Οἶδά σου τὰ ἔργα, καὶ τὴν ⸂ἀγάπην καὶ τὴν πίστιν καὶ τὴν διακονίαν καὶ τὴν ὑπομονήν σου, καὶ τὰ ἔργα σου τὰ ἔσχατα πλείονα τῶν πρώτων.
20 Amma ga rashin jin dadi na da kai: Kana hakurce wa matar nan Yezebel, wadda take kiran kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta, ta rudi bayina suyi fasikanci kuma su ci abincin da aka mika wa gumaka sadaka.
ἀλλὰ ἔχω κατὰ σοῦ ὅτι ἀφεῖς τὴν ⸀γυναῖκαἸεζάβελ, ἡ ⸀λέγουσαἑαυτὴν προφῆτιν, καὶ διδάσκει καὶ πλανᾷ τοὺς ἐμοὺς δούλους πορνεῦσαι καὶ φαγεῖν εἰδωλόθυτα.
21 Na bata lokaci domin ta tuba amma bata so ta tuba da fasikancin ta.
καὶ ἔδωκα αὐτῇ χρόνον ἵνα μετανοήσῃ, καὶ οὐ θέλει μετανοῆσαι ἐκ τῆς πορνείας αὐτῆς.
22 Duba! zan jefa ta a kan gadon jinya, wadanda kuma suka yi zina da ita za su shiga babbar wahala, sai dai in sun tuba daga ayukan ta.
ἰδοὺ βάλλω αὐτὴν εἰς κλίνην, καὶ τοὺς μοιχεύοντας μετʼ αὐτῆς εἰς θλῖψιν μεγάλην, ἐὰν μὴ ⸀μετανοήσωσινἐκ τῶν ἔργων αὐτῆς·
23 Zan buga 'ya'yanta da mutuwa, kuma dukan ikilisiyoyi zasu san cewa nine wanda nake bincike tunani da zukata. Zan ba kowanen ku bisa ga ayyukansa.
καὶ τὰ τέκνα αὐτῆς ἀποκτενῶ ἐν θανάτῳ· καὶ γνώσονται πᾶσαι αἱ ἐκκλησίαι ὅτι ἐγώ εἰμι ὁ ἐραυνῶν νεφροὺς καὶ καρδίας, καὶ δώσω ὑμῖν ἑκάστῳ κατὰ τὰ ἔργα ὑμῶν.
24 Amma ga sauran ku dake cikin Tayatira, ga kowanen ku wanda bai rike wannan koyarwar ba, kuma bai san abinda wadansu suke kira zurfafan abubuwan Shaidan ba—ga ku na ce ban sa muku wata nawaya ba.'
ὑμῖν δὲ λέγω τοῖς λοιποῖς τοῖς ἐν Θυατείροις, ὅσοι οὐκ ἔχουσιν τὴν διδαχὴν ταύτην, οἵτινες οὐκ ἔγνωσαν τὰ βαθέα τοῦ Σατανᾶ, ὡς λέγουσιν, οὐ βάλλω ἐφʼ ὑμᾶς ἄλλο βάρος·
25 Duk da haka dole ku tsaya da karfi har in zo.
πλὴν ὃ ἔχετε κρατήσατε ἄχρι οὗ ἂν ἥξω.
26 Wanda yayi nasara da wanda ya yi abin da na yi har karshe, a gareshi zan bada iko akan al'ummai
καὶ ὁ νικῶν καὶ ὁ τηρῶν ἄχρι τέλους τὰ ἔργα μου, δώσω αὐτῷ ἐξουσίαν ἐπὶ τῶν ἐθνῶν,
27 Zai yi mulkin su da sandar karfe, zai farfasa su kamar randunan yumbu.”
καὶ ποιμανεῖ αὐτοὺς ἐν ῥάβδῳ σιδηρᾷ ὡς τὰ σκεύη τὰ κεραμικὰ ⸀συντρίβεται
28 Kamar yadda na karba daga wurin Ubana, ni kuma zan bashi tauraron asubahi.
ὡς κἀγὼ εἴληφα παρὰ τοῦ πατρός μου, καὶ δώσω αὐτῷ τὸν ἀστέρα τὸν πρωϊνόν.
29 Bari wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fadawa ikilisiyioyi.””
ὁ ἔχων οὖς ἀκουσάτω τί τὸ πνεῦμα λέγει ταῖς ἐκκλησίαις.