< Ru’uya ta Yohanna 17 >

1 Daya daga cikin mala'ikun nan bakwai wanda ke rike da tasoshi bakwai ya zo ya ce mani, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwarnan da ke zaune a kan ruwaye masu yawa.
One of the seven angels who had the seven bowls came and spoke with me, saying, “Come here. I will show you the judgment of the great prostitute who sits on many waters,
2 Da ita ce sarakunan duniya suka yi fasikanci. Da ruwan inabinta na fasikanci marar dacewa ta sa mazaunan duniya suka bugu.”
with whom the kings of the earth committed sexual immorality. Those who dwell in the earth were made drunken with the wine of her sexual immorality.”
3 Sai mala'ikan ya dauke ni cikin Ruhu ya tafi da ni jeji, sai na ga mace zaune bisa jan dabba cike da sunayen sabo. Dabbar tana da kawuna bakwai da kahonni goma.
He carried me away in the Spirit into a wilderness. I saw a woman sitting on a scarlet-colored beast, full of blasphemous names, having seven heads and ten horns.
4 Matar kuwa tana sanye da tufafi na shunayya da kuma jar garura, ta kuma ci ado da kayan zinariya da duwatsu masu tamani da lu'u-lu'ai. Tana rike da kokon zinariya a hannunta cike da abubuwan kyama da na kazantar fasikancinta marar dacewa.
The woman was dressed in purple and scarlet, and decked with gold and precious stones and pearls, having in her hand a golden cup full of abominations and the impurities of the sexual immorality of the earth.
5 Bisa goshinta an rubuta wani suna mai boyayyar ma'ana: “Babila mai girma, uwar karuwai da na kazamtattun abubuwan duniya.”
And on her forehead a name was written, “MYSTERY, BABYLON THE GREAT, THE MOTHER OF THE PROSTITUTES AND OF THE ABOMINATIONS OF THE EARTH.”
6 Sai na ga matar a buge da jinin masu ba da gaskiya da kuma jinin wadanda aka kashe su domin Yesu. Da na gan ta, na yi mamaki kwarai da gaske.
I saw the woman drunken with the blood of the saints and with the blood of the martyrs of Jesus. When I saw her, I wondered with great amazement.
7 Amma mala'ikan ya ce mani, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka ma'anar matar da kuma na dabbar da ke dauke da ita, dabban nan da ke da kawuna bakwai da kahonni goma.
The angel said to me, “Why do you wonder? I will tell you the mystery of the woman and of the beast that carries her, which has the seven heads and the ten horns.
8 Dabban da ka gani da, yanzu ba ta, amma ta na kusan hawowa daga rami marar iyaka. Sa'annan za ta je hallaka. Wadanda ke zaune a duniya, wadanda ba a rubuta sunayensu cikin littafin rai ba tun kafuwar duniya - za su yi mamaki idan suka ga dabbar da da ta kasance, ba ta nan yanzu, amma ta kusa zuwa. (Abyssos g12)
The beast that you saw was, and is not; and is about to come up out of the Abyss (Abyssos g12) and to go into destruction. Those who dwell on the earth and whose names have not been written in the book of life from the foundation of the world will marvel when they see that the beast was, and is not, and shall be present.
9 Wannan al'amari na bukatar hikima. Kawunnan bakwai, tuddai ne bakwai da macen ke zaune a kai.
Here is the mind that has wisdom. The seven heads are seven mountains on which the woman sits.
10 Su kuma sarakuna ne bakwai. Sarakuna biyar sun fadi, daya na nan, amma dayan bai zo ba tukuna; sa'anda ya zo zai kasance na dan lokaci kadan.
They are seven kings. Five have fallen, the one is, and the other has not yet come. When he comes, he must continue a little while.
11 Dabban da ya kasance a da, amma yanzu ba shi, shi ma sarki ne na takwas; amma shi daya ne cikin sarakunan nan bakwai, kuma zai tafi hallaka.
The beast that was, and is not, is himself also an eighth, and is of the seven; and he goes to destruction.
12 Kahonnin nan goma da ka gani sarakuna goma ne wadanda ba a nada su ba tukuna, amma za su karbi iko kamar na sarakai na sa'a daya tare da dabban.
The ten horns that you saw are ten kings who have received no kingdom as yet, but they receive authority as kings with the beast for one hour.
13 Ra'ayinsu daya ne, za su ba da sarautarsu da ikon su ga dabban.
These have one mind, and they give their power and authority to the beast.
14 Za su yi yaki da Dan Rago. Dan Ragon zai ci nasara a kansu domin shi Ubangijin iyayengiji ne da Sarkin sarakuna - kuma tare da shi sune kirayayyun, zababbun, amintattun.”
These will war against the Lamb, and the Lamb will overcome them, for he is Lord of lords and King of kings; and those who are with him are called, chosen, and faithful.”
15 Mala'ikan ya ce mani, “Ruwayen da ka gani, inda karuwar ke zaune, jama'a ce, da taro masu dumbin yawa, da al'ummai da harsuna.
He said to me, “The waters which you saw, where the prostitute sits, are peoples, multitudes, nations, and languages.
16 Kahonnin nan goma da ka gani - su da dabban za su ki karuwar. Za su washe ta su tsiranceta, za su lankwame namanta, za su kone ta gaba daya da wuta.
The ten horns which you saw, they and the beast will hate the prostitute, will make her desolate, will strip her naked, will eat her flesh, and will burn her utterly with fire.
17 Gama Allah ya sa a zukantansu su yi nufinsa ta wurin amincewarsa, su sadaukar da ikonsu na yin mulki ga dabban har sai maganar Allah ta cika.
For God has put in their hearts to do what he has in mind, to be of one mind, and to give their kingdom to the beast, until the words of God should be accomplished.
18 Matar da ka gani ita ce babban birnin nan da ke mulki bisa sarakunan duniya.”
The woman whom you saw is the great city which reigns over the kings of the earth.”

< Ru’uya ta Yohanna 17 >