< Ru’uya ta Yohanna 16 >
1 Na ji babban murya na kira daga cikin haikali tana ce wa malai'iku bakwai, ''Ku je ku zuba tasoshi bakwai na fushin Allah a kan duniya.”
And I herde a great voyce out of ye temple sayinge to the seven angels: goo youre wayes poure out youre vialles of wrath apon the erth.
2 Mala'ika na fari ya je ya zuba tasarsa a kan duniya; munanan gyambuna masu zafi suka fito wa mutane wadanda suke da alamar dabbar, wadanda suka bauta wa siffarsa.
And the fyrst went and poured out his viall apo the erth and there fell anoysom and a sore botche apo the me which had the marke of the best and ap on the which worshipped his ymage.
3 Mala'ika na biyu ya zuba tasarsa cikin teku. Ya zama jini, kamar jinin wanda ya mutu, kuma kowane abu mai rai da ke cikin tekun ya mutu.'
And the seconde angell shed out his viall apon ye see and it turned as it were into the bloud of a deed ma: and every lyvinge thynge dyed in the see.
4 Malaika na uku ya zuba tasarsa a cikin rafuffuka da mabulbulan ruwa, sai suka zama jini.
And ye thyrde angell shed out his vyall apon the ryvers and fountaynes of waters and they turned to bloud.
5 Na ji mala'ikan ruwaye ya ce, ''Kai mai adalci ne - wanda ya ke yanzu wanda yake kuma a da, Mai Tsarkin nan, domin ka shari'anta wadannan abubuwa.
And I herde an angell saye: lorde which arte and wast thou arte ryghteous and holy because thou hast geve soche iudgmentes
6 Domin sun zubar da jinin masu ba da gaskiya da annabawa, ka basu jini su sha; shine abinda da ya dace da su.
for they shed out the bloude of sayntes and prophettes and therfore hast thou geven them bloud to drynke: for they are worthy.
7 Na ji bagadi ya amsa, ''I, Ubangiji Allah Mai iko duka, shari'un ka gaskiya ne da adalci.''
And I herde another out of the aultre saye: even soo lorde god almyghty true and righteous are thy iudgementes.
8 Mala'ika na hudu ya zuba tasarsa a kan rana, kuma aka ba shi izini ya kone jama'a da wuta.
And the fourth angell poured out his viall on the sunne and power was geve vnto him to vexe men with heate of fyre.
9 Suka kone da zafi mai tsanani, kuma suka sabi sunan Allah, wanda ke da iko akan annobai. Ba su tuba ba ko su daukaka shi.
And the men raged in gret heate and spake evyll of the name of God which had power over those plages and they repented not to geve him glory.
10 Sai malaika na biyar ya zuba tasarsa a kan kursiyin dabban, sai duhu ya rufe mulkinsa. Suka cicciji harsunansu saboda zafi.
And the fifte angell poured out his vyall apon the seate of the beste and his kyngdome wexed derke and they gnewe their tonges for sorowe
11 Suka yi sabon Allah na sama domin zafi da gyambunansu, suka kuma ki su tuba daga abin da suka yi.
and blasphemed the god of heven for sorowe and payne of their sores and repented not of their dedes.
12 Mala'ika na shida ya zuba tasarsa cikin babban rafi, Yufiretis. Ruwansa ya bushe domin a shirya hanya da sarakuna za su zo daga gabas.
And the sixte angell poured out his vyall apon the gret ryver Euphrates and the water dryed vp that the wayes of the kyngss of the este shulde be prepared.
13 Na ga kazamun ruhohi uku suna kama da kwadin da ke fitowa daga bakin diragon, da makaryacin annabi.
And I sawe thre vnclene sprettes lyke frogges come out of the mouthe of the dragon and out of the mouthe of the beeste and out of the mouthe of the falce prophett.
14 Gama su ruhohin aljanu ne masu aikata alamun ban mamaki. Sun fita za su wurin sarakunan dukan duniya domin su tattaro su wuri daya saboda yaki a babbar ranar Allah Mai iko duka.
For they are the sprettes of devyls workynge myracles to go out vnto the kynges of the erth and of the whole worlde to gaddre them to the battayle of that gret daye of God allmyghty.
15 (''Duba! Ina zuwa kamar barawo! Mai albarka ne wanda ke zaune a fadake, wanda ke sanye da tufafinsa domin ba zai fita tsirara a ga tsiraicin sa ba.”)
Beholde I come as a thefe. Happy is he that watcheth and kepeth his garmentes Lest he be founde naked and men se his filthynes.
16 Aka kawo su tare a wurin da ake kira Armagiddon da Ibraniyanci.
And he gaddered them togedder into a place called in the hebrue tonge Armagedon.
17 Mala'ika na bakwai ya zuba tasarsa cikin iska. Sa'annan babbar murya ta fito daga cikin haikali da kuma kursiyin, cewa, ''An gama!''
And the seventhe angell poured out his viall in to the ayre. And there came a voyce out of heven from the seate sayinge: it is done.
18 Aka yi walkiya, da kararraki masu tsanani, da aradu da babbar girgizar kasa - girgizar da ta fi kowacce da aka taba yi tun da 'yan adam suke a duniya, girgizar da girma ta ke.
And there folowed voyces thondringes and lightnynges and there was a grett erthquake soche as was not sence men were apon the erth so myghty an erthquake and so grett.
19 Babban birnin ya rabu kashi uku, kuma biranen al'ummai suka fadi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, sai ya ba wancan birnin koko cike da ruwan innabi wanda aka yi daga fushinsa mai tsanani.
And the greate cite was devyded into thre parties And the cities of nacions fell. And grett Babilon came in remembraunce before God to geve vnto hyr the cuppe of wyne of the fearcenes of his wrathe.
20 Kowanne tsibiri ya bace, sai ba a kara ganin duwatsun ba.
Every yle fled awaye and the mountaynes were not founde.
21 Manyan duwatsun kankara, masu nauyin talanti, suka fado daga sama kan mutane. Suka zagi Allah domin annobar kankarar saboda annobar ta yi tsanani.
And ther fell a gret hayle as it had bene talentes out of heven apon the men and the men blasphemed God be cause of the plage of the hayle for it was grett and the plage of it sore.