< Filibbiyawa 4 >
1 Saboda haka, kaunatattu 'yan'uwana da nake marmari, farin ciki na da rawani na, a wannan hanya ku tsaya daram cikin Ubangiji, kaunatattun abokai.
2 Ina rokon Afodiya, ina rokon Sintiki, ku zama da ra'ayi daya cikin Ubangiji.
3 Babu shakka, ina sake rokon ku, abokan tarayyar takunkumina na gaske: ku taimaka wa matayen nan. Domin mun yi wahala tare a cikin yada bishara tare da Kilimas da sauran abokan aiki na, wanda sunayensu na rubuce cikin littafin rai.
4 Yi farin ciki cikin Ubangiji kullayomi. Ina sake cewa, yi farin ciki.
5 Bari dukan mutane su ga jimirin ku. Ubangiji ya yi kusa.
6 Kada ku damu da kowanne abu, maimakon haka, cikin komai tare da addu'a, da rokeroke, da godiya, bari rokeroken ku su sanu ga Allah.
7 Salamar Allah, da ta zarce dukan ganewa za ta tsare zuciyarku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.
8 A karshe, 'yan'uwa, duk abin da ke mai gaskiya, duk abin da ya isa ban girma, duk abin da ke mai adalci, duk abin da ke mai tsabta, duk abin da ke karbabbe, duk abin da ke kawo kauna, duk abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai yabo, yi tunani a kan wadannan abubuwan.
9 Wadannan abubuwan da kuka koya kuka karba kuka ji kuka gani a rayuwa ta, ku aikata wadannan abubuwan. Allah mai salama zai kasance tare da ku.
10 Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba.
11 Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi.
12 Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata.
13 Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni.
14 Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na.
15 Kun kuma sani, ku Filibiyawa, cewa da farkon bishara, lokacin da na bar Makidoniya, babu ikilisiya da ta tallafe ni cikin batun bayarwa da karba sai ku kadai.
16 Ko lokacin da nake Tassalonika, kun aika da gudumawar biyan bukatu na fiye da sau daya.
17 Ba domin ina neman kyauta ba ne. A maimakon haka, ina neman amfani da zai kawo karuwa cikin ajiyar ku.
18 Na karbi dukan abubuwan, ina da shi a yalwace. An kosar da ni. Na karba ta hanun Abafroditus abubuwa daga wurinku. Shesheki na dadin kamshi mai dandanno, karbabbiyar hadaya mai gamsarwa ga Allah.
19 Allah na zai cika dukan bukatunku bisa ga yalwarsa da ke cikin daukaka cikin Almasihu Yesu.
20 Yanzu bari daukaka ta tabbata ga Allah da Ubanmu har abada abadin. Amin. (aiōn )
21 Gai da kowanne mai bi cikin Almasihu Yesu. Dukan 'yan'uwa da ke tare da ni suna gaisuwa.
22 Dukan masu bi a nan suna gaisuwa, musamman wadanda suke gidan Kaisar.
23 Bari alherin Ubangijin Yesu Almasihu ya zauna tare da ruhunku. Amin