< Filibbiyawa 3 >

1 A karshe, 'yan'uwana, ku yi farin ciki cikin Ubangiji. In sake rubuta maku wadannan abubuwa ba wani abu mai nauyi ba ne a gare ni. Wadannan abubuwa zasu tsare ku.
종말로 나의 형제들아 주 안에서 기뻐하라! 너희에게 같은 말을 쓰는 것이 내게는 수고로움이 없고 너희에게는 안전하니라
2 Ku yi hankali da karnuka. Ku yi hankali da miyagun ma'aikata. Ku yi hankali da masu yanke-yanke.
개들을 삼가고 행악하는 자들을 삼가고 손할례당을 삼가라
3 Gama mune kaciyar. Don mune muke sujada ta wurin Ruhun Allah. Mune masu fahariya chikin Almasihu Yesu, kuma ba mu da gabagadi cikin jiki.
하나님의 성령으로 봉사하며 그리스도 예수로 자랑하고 육체를 신뢰하지 아니하는 우리가 곧 할례당이라
4 Ko da shike, ni kaina ina gabagadi ga jiki. Idan wani zai iya tunanin gabagadi ga jiki, ni na fi shi.
그러나 나도 육체를 신뢰할 만하니 만일 누구든지 다른 이가 육체를 신뢰할 것이 있는 줄로 생각하면 나는 더욱 그러하리니
5 An yi mani kaciya a rana ta takwas, daga mutanen Israila, na kabilar Biliyaminu, Bayahuden Yahudawa; ga zancen shari'a Bafarisiye nake.
내가 팔일 만에 할례를 받고 이스라엘의 족속이요 베냐민의 지파요 히브리인 중의 히브리인이요 율법으로는 바리새인이요
6 Wajen himma na tsanantawa ikilisiya. Ga zancen adalci cikin sharia, na zama mara abin zargi.
열심으로는 교회를 핍박하고 율법의 의로는 흠이 없는 자로라
7 Amma duk wadannan abubuwan da suka zama riba a gare ni, na dauke su asara ne saboda Almasihu.
그러나 무엇이든지 내게 유익하던 것을 내가 그리스도를 위하여 다 해로 여길 뿐더러
8 I, lallai ina lisafta dukan wadannan abubuwa asara saboda mafificin sanin Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shine na yi asarar dukan abubuwa. Na maishe su marasa amfani domin in ribato Almasihu,
또한 모든 것을 해로 여김은 내 주 그리스도 예수를 아는 지식이 가장 고상함을 인함이라 내가 그를 위하여 모든 것을 잃어버리고 배설물로 여김은 그리스도를 얻고
9 a iske ni cikinsa. Ba ni da wani adalcin kaina ta wurin shari'a. Maimakon haka, ina da adalci ta wurin bangaskiya cikin Almasihu, adalcin dake daga wurin Allah ta wurin Bangaskiya.
그 안에서 발견되려 함이니 내가 가진 의는 율법에서 난 것이 아니요 오직 그리스도를 믿음으로 말미암은 것이니 곧 믿음으로 하나님께로서 난 의라
10 Yanzu ina so in san shi da ikon tashinsa, da tarayya cikin shan wuyarsa. In kuma zama kamarsa wajen mutuwarsa,
내가 그리스도와 그 부활의 권능과 그 고난에 참예함을 알려하여 그의 죽으심을 본받아
11 domin ta ko kaka in kai ga tashi daga cikin matattu.
어찌하든지 죽은 자 가운데서 부활에 이르려 하노니
12 Ba wai na rigaya na sami wadannan abubuwa bane, ko kuma na riga na zama cikakke. Amma ina nace bi domin in cafki wannan da Almasihu Yesu ya cafko ni dominsa.
내가 이미 얻었다 함도 아니요 온전히 이루었다 함도 아니라 오직 내가 그리스도 예수께 잡힌 바 된 그것을 잡으려고 좇아가노라
13 'Yan'uwa, ban dauka cewa na riga na cafka ba tukuna. Amma akwai abu daya da nake yi: ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa ga abin da ke gaba.
형제들아 나는 아직 내가 잡은 줄로 여기지 아니하고 오직 한 일, 즉 뒤에 있는 것은 잊어버리고 앞에 있는 것을 잡으려고
14 Ina nacewa zuwa ga manufar nan in kai ga samun ladar nasara na madaukakin kiran Allah cikin Almasihu Yesu.
푯대를 향하여 그리스도 예수 안에서 하나님이 위에서 부르신 부름의 상을 위하여 좇아가노라
15 Dukan mu wadanda muke kammalallu, sai mu yi tunani ta wannan hanyar, idan kuwa kun yi tunanin wani abu daban, to Allah zai bayyana maku wannan kuma.
그러므로 누구든지 우리 온전히 이룬 자들은 이렇게 생각할지니 만일 무슨 일에 너희가 달리 생각하면 하나님이 이것도 너희에게 나타내시리라
16 Sai dai, in da muka rigaya muka kai, bari mu rike shi haka.
오직 우리가 어디까지 이르렀든지 그대로 행할 것이라
17 Ku zama masu koyi da ni, 'yan'uwa. Ku duba da kyau wadannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare ku.
형제들아 너희는 함께 나를 본받으라 또 우리로 본을 삼은 것같이 그대로 행하는 자들을 보이라
18 Mutane da dama suna tafiya -sune wadanda na ba ku labarin su, yanzu kuma ina fada maku har da hawaye - kamar makiyan gicciyen Almasihu ne.
내가 여러 번 너희에게 말하였거니와 이제도 눈물을 흘리며 말하노니 여러 사람들이 그리스도 십자가의 원수로 행하느니라
19 Karshen su hallaka ne. Domin allahn su ciki ne, fahariyar su kuma tana cikin kunyar su. Tunanin su na kan al'amuran duniya.
저희의 마침은 멸망이요 저희의 신은 배요 그 영광은 저희의 부끄러움에 있고 땅의 일을 생각하는 자라
20 Amma mu 'yangarincin mu a sama yake, daga inda muke sauraron mai ceto, Ubangiji Yesu Almasihu.
오직 우리의 시민권은 하늘에 있는지라 거기로서 구원하는 자 곧 주 예수 그리스도를 기다리노니
21 Za ya sake jikinmu na kaskanci ya siffanta shi kamar jikin darajarsa, siffantacce ta karfin ikonsa inda ya sarayar da dukan abubuwa a gare shi.
그가 만물을 자기에게 복종케 하실 수 있는 자의 역사로 우리의 낮은 몸을 자기 영광의 몸의 형체와 같이 변케 하시리라

< Filibbiyawa 3 >