< Filibbiyawa 1 >
1 Bulus da Timoti bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan wadan da aka kebe cikin Almasihu Yesu da ke a Filibi, tare da masu kula da ikilisiya da dikinoni.
Paulus et Timotheus servi Iesu Christi omnibus sanctis in Christo Iesu qui sunt Philippis cum episcopis et diaconis
2 Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubagijinmu Yesu Almasihu.
gratia vobis et pax a Deo Patre nostro et Domino Iesu Christo
3 Ina godiya ga Allahna duk lokacin da na tuna da ku.
gratias ago Deo meo in omni memoria vestri
4 Ko yaushe cikin addu'a ta dominku duka, da farin ciki na ke addu'a.
semper in cunctis orationibus meis pro omnibus vobis cum gaudio deprecationem faciens
5 Ina godiya domin tarayyar ku a cikin bishara tun daga rana ta fari har ya zuwa yanzu.
super communicatione vestra in evangelio a prima die usque nunc
6 Na tabbata game da wannan abu, shi wanda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da shi har ya kai ga kammala zuwa ranar Yesu Almasihu.
confidens hoc ipsum quia qui coepit in vobis opus bonum perficiet usque in diem Christi Iesu
7 Daidai ne in ji haka game da dukanku domin kuna zuciya ta. Dukanku abokan tarayya ta ne cikin alherin Allah wajen dauri na da kuma kariyar bishara, da tabbatar da bishara.
sicut est mihi iustum hoc sentire pro omnibus vobis eo quod habeam in corde vos et in vinculis meis et in defensione et confirmatione evangelii socios gaudii mei omnes vos esse
8 Domin Allah mashaidi na ne, a kan yadda ina da marmarin ku duka cikin zurfin kaunar Almasihu Yesu.
testis enim mihi est Deus quomodo cupiam omnes vos in visceribus Christi Iesu
9 Ina yin wannan addu'a: kaunar ku ta habaka gaba gaba a cikin sani da dukan fahimta.
et hoc oro ut caritas vestra magis ac magis abundet in scientia et omni sensu
10 Ina addu'a a kan haka domin ku gwada ku zabi mafifitan abubuwa. Ina addu'a domin ku zama sahihai marasa abin zargi a ranar Almasihu.
ut probetis potiora ut sitis sinceres et sine offensa in diem Christi
11 Wannan kuma domin a cika ku da 'ya'yan adalci da ake samu ta wurin Yesu Almasihu, zuwa ga daukaka da yabon Allah.
repleti fructu iustitiae per Christum Iesum in gloriam et laudem Dei
12 Yanzu ina so ku sani, 'yan'uwa, cewa al'amuran da suka faru da ni sun zama dalilan cin gaban bishara kwarai da gaske.
scire autem vos volo fratres quia quae circa me sunt magis ad profectum venerunt evangelii
13 Sakamakon haka, sarkokina cikin Almasihu sun zama sanannu ga dukan sojojin fada da kuma sauran jama'a,
ita ut vincula mea manifesta fierent in Christo in omni praetorio et in ceteris omnibus
14 har galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka karfafa kwarai sabili da sarkokina, suka fito a fili suka yi shelar maganar Allah gabagadi.
et plures e fratribus in Domino confidentes vinculis meis abundantius audere sine timore verbum Dei loqui
15 Lalle wadansu suna shelar Almasihu cikin kishi da husuma, wadansu kuwa domin kyakyawar manufa.
quidam quidem et propter invidiam et contentionem quidam autem et propter bonam voluntatem Christum praedicant
16 Masu shelar Almasihu domin kauna sun sani cewa an ajiye ni nan domin in kare bishara.
quidam ex caritate scientes quoniam in defensionem evangelii positus sum
17 Amma wadansu kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai da rashin gaskiya. A zaton su suna wahalar da ni cikin sarkokina.
quidam autem ex contentione Christum adnuntiant non sincere existimantes pressuram se suscitare vinculis meis
18 Sai kuma me? Ta kowace hanya, ko da gangan ko da gaske, shelar Almasihu ake yi, ina kuma murna da wannan! I, zan yi murna.
quid enim dum omni modo sive per occasionem sive per veritatem Christus adnuntiatur et in hoc gaudeo sed et gaudebo
19 Domin na sani wannan zai kai ga sanadiyar kubuta ta. Wannan zai faru sabili da addu'ar ku, da kuma taimakon Ruhun Yesu Almasihu.
scio enim quia hoc mihi proveniet in salutem per vestram orationem et subministrationem Spiritus Iesu Christi
20 Bisa ga abin da hakikance nake tsammani da tabbaci cewa ba zan kunyata ba. Maimakon haka, da dukan karfin hali kamar kullum, da yanzu kuma, ina da burin kawo daukaka ga Almasihu a cikin jikina. Ina da begen Almasihu ya sami daukaka a cikin jikina ko cikin rayuwa ko cikin mutuwa.
secundum expectationem et spem meam quia in nullo confundar sed in omni fiducia sicut semper et nunc magnificabitur Christus in corpore meo sive per vitam sive per mortem
21 Domin ni a gare ni rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce.
mihi enim vivere Christus est et mori lucrum
22 Amma idan ya zamanto rayuwata cikin jiki za ta kawo amfanin hidima to, ban san wanda zan zaba ba.
quod si vivere in carne hic mihi fructus operis est et quid eligam ignoro
23 Amma dukansu biyu suna jan hankali na. Ina da burin in bar nan in kasance tare da Almasihu, wannan ya fiye mani kwarai!
coartor autem e duobus desiderium habens dissolvi et cum Christo esse multo magis melius
24 Duk da haka rayuwata cikin jiki wajibi ne sabili da ku.
permanere autem in carne magis necessarium est propter vos
25 Tunda shike ina da tabbas a kan wannan, na kuma sani zan rayu, in cigaba da kasancewa da ku duka domin cigaban ku, da farincikin ku, cikin bangaskiya.
et hoc confidens scio quia manebo et permanebo omnibus vobis ad profectum vestrum et gaudium fidei
26 Sakamakon haka, takamar ku cikin Almasihu Yesu za ta bunkasa sabili da dawowa ta a gare ku.
ut gratulatio vestra abundet in Christo Iesu in me per meum adventum iterum ad vos
27 Ku tafiyar da al'amuran ku kamar yadda ya cancanci bisharar Almasihu, ku yi haka domin ko na zo in duba ku, ko bana nan inji yadda kuke tsaye daram cikin ruhu guda. Ina fatan in ji cewa da nufi daya kuke fama tare saboda bangaskiyar nan ta bishara.
tantum digne evangelio Christi conversamini ut sive cum venero et videro vos sive absens audiam de vobis quia stetistis uno spiritu unianimes conlaborantes fide evangelii
28 Kada ku tsorata da kome da magabtanku za su yi. Alama ce a gare su ta hallakar su. Amma ku kuwa alama ce ta ceton ku, wannan kuwa daga Allah ne.
et in nullo terreamini ab adversariis quae est illis causa perditionis vobis autem salutis et hoc a Deo
29 Gama an yi maku alheri, sabo da Almasihu, ba gaskantawa da Almasihu kawai ba, amma har ma shan wuya dominsa.
quia vobis donatum est pro Christo non solum ut in eum credatis sed ut etiam pro illo patiamini
30 Kuna da shan wuya irin tawa wanda kuka gani, wanda kun ji nake sha har yanzu.
eundem certamen habentes qualem et vidistis in me et nunc audistis de me