< Filemon 1 >

1 Bulus, daurarren Yesu Almasihu, da kuma dan'uwa Timotawus zuwa ga Filimon, kaunataccen abokinmu da kuma abokin aikin mu,
基督耶穌的被囚者保祿,和弟茂德弟兄,致書給我們可愛的合作者費1肋孟,
2 da Afiya yar'uwanmu da Arkifus abokin aikin mu a filin daga, da kuma Ikilisiyar da take taruwa a gidan ka:
並給姊妺阿丕雅和我們的戰友阿爾希頗,以及在妳家中的教會。
3 Alheri da salama su kasance gare ka daga wurin Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu.
願恩寵與平安,由天主我們的父及主耶穌基督賜與你們。
4 Kowane lokaci ina gode wa Allah. Ina ambaton ku cikin addu'oi na.
在我的祈禱記念你時,我常感謝我的天主,
5 Na ji labarin kauna da bangaskiya da ka ke da ita a cikin Ubangiji Yesu da dukkan yan'uwa masu bi.
因為聽說你對主耶穌,和對眾聖徒所表現的愛德與信德。
6 Ina addu'a zumuntar bangaskiyarka ta inganta ga kawo sanin kowane kyakkyawan abu dake cikin mu a cikin Almasihu.
我祈求天主,為使你因信德而懷有的慷慨發生功效,使你認清我們所能行的一切善事,都是為基督而行的。
7 Na yi farinciki kwarai, na kuma ta'azantu saboda kaunarka, saboda zukatan masu bi sun kwanta ta wurin ka, dan'uwa.
弟兄,我由於你的愛德,確實獲得了極大的喜樂和安慰,因為與著你,聖徒的心都舒暢了。
8 Saboda haka, ko da ya ke ina da gabagadi a cikin Almasihu domin in ba ka umarni ka yi abinda ya kamata ka yi,
為此,我雖然在基督內,能放心大膽地命你去作這件該作的事,
9 duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu.
可是,我這年老的保祿,如今且為基督耶穌作囚犯的,寧願因著愛德求你,
10 Ina rokon ka saboda da na Onisimus, wanda na zama uba a gare shi sa'adda nake cikin sarkokina.
就是為失在鎖鏈中所生的兒子敖乃息摩來求你。
11 Domin a da kam, ba shi da amfani a wurin ka, amma yanzu yana da amfani a gare ka da kuma a gare ni.
他曾一度為你是無用的,可是,如今為你我都有用了;
12 Na kuma aike shi wurinka, shi wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai.
我現今把他給打發回去,[你收下]他,他是我的心肝。
13 Na so da na rike shi a wuri na, domin ya rika yi mini hidima a madadin ka, a lokacin da ni ke cikin sarkoki saboda bishara.
我本來願意將他留在我這裏,叫他替你服侍我這為福音而被囚 的人,
14 Amma ba na so in yi wani abu ba tare da sanin ka ba. Ba ni so nagarin aikinka ya zama na dole amma daga kyakkyawar nufi.
可是沒有你的同意,我什麼也不願意做,好叫你所行的善不是出於勉強,而是出於甘心。
15 Watakila dalilin da yasa ya rabu da kai na dan lokaci ke nan, domin ka karbe shi kuma har abada. (aiōnios g166)
也許他暫時離開了你,是為叫你永遠收下他, (aiōnios g166)
16 Daga yanzu ba za ya zama bawa ba kuma, amma fiye da bawa, wato kaunataccen dan'uwa. Shi kaunatacce ne musamman a gare ni, har fiye da haka ma a gare ka, a cikin jiki da kuma cikin Ubangiji.
不再當一個奴隸,而是超過奴隸,作可愛的弟兄:他為我特別可愛,但為你不拘是論肉身方面,或是論主方面,更加可愛。
17 Idan ka maishe ni abokin hidima, ka karbe shi kamar yadda za ka karbe ni.
所以,若你以我為同志,就嫉留他當作收留我罷!
18 Idan kuwa ya yi maka abinda ba daidai ba ko kuwa kana bin sa wani abu, ka dauka yana wurina.
他若虧負了你或欠下你什麼,就算在我的賬上罷!
19 Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna: zan biya ka. Ba kuwa cewa sai na gaya maka cewa ina bin ka bashin kanka ba.
我中親手簽字:「我必要償還。」至於你,你所欠於我的,竟是你本身:這我就不必對你說了!
20 I, dan'uwa, ka yi mani alheri cikin Ubangiji; ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu.
弟兄,望你使我在主內得此恩惠,並在基督內使我心舒暢!
21 Saboda Ina da tabbaci game da biyayyarka, na rubuta maka. Na san za ka yi fiye da abinda na roka.
我自信你必聽從,才給你寫了這信,我知道就是超過我所的,你也必 作。
22 Harwayau, ka shirya mani masauki. Domin ina fata ta wurin adu'oinku, nan ba da dadewa ba za a maida ni wurin ku.
同時也請你給準備一個住處,因為我希望因 的祈禱,主必要把我賜給你們。
23 Efafaras, abokina cikin Almasihu Yesu a kurkuku yana gaishe ka,
為基督耶穌與我一同被囚的厄帕夫辣、
24 haka ma Markus da Aristarkus, da Dimas, da Luka abokan aikina.
我的合作者馬爾谷、阿黎斯塔苛、德瑪斯、路加都問攸候你。
25 Bari Alherin Ubangiji Yesu Almasihu ya kasance da Ruhunka. Amin.
願主基督的恩寵,與你們的心靈同在! 阿們。

< Filemon 1 >