< Mattiyu 8 >

1 Da Yesu ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawa suka bi shi.
जब यीशु उस पहाड़ से उतरा, तो एक बड़ी भीड़ उसके पीछे हो ली।
2 Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
और, एक कोढ़ी ने पास आकर उसे प्रणाम किया और कहा, “हे प्रभु यदि तू चाहे, तो मुझे शुद्ध कर सकता है।”
3 Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa.
यीशु ने हाथ बढ़ाकर उसे छुआ, और कहा, “मैं चाहता हूँ, तू शुद्ध हो जा” और वह तुरन्त कोढ़ से शुद्ध हो गया।
4 Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu?
यीशु ने उससे कहा, “देख, किसी से न कहना, परन्तु जाकर अपने आपको याजक को दिखा और जो चढ़ावा मूसा ने ठहराया है उसे चढ़ा, ताकि उनके लिये गवाही हो।”
5 Da Yesu ya shiga kafarnahum, sai wani hafsa ya zo gunsa ya roke shi,
और जब वह कफरनहूम में आया तो एक सूबेदार ने उसके पास आकर उससे विनती की,
6 Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.”
“हे प्रभु, मेरा सेवक घर में लकवे का मारा बहुत दुःखी पड़ा है।”
7 Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”
उसने उससे कहा, “मैं आकर उसे चंगा करूँगा।”
8 Sai hafsan, ya ce, “Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke.
सूबेदार ने उत्तर दिया, “हे प्रभु, मैं इस योग्य नहीं, कि तू मेरी छत के तले आए, पर केवल मुँह से कह दे तो मेरा सेवक चंगा हो जाएगा।
9 Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,”
क्योंकि मैं भी पराधीन मनुष्य हूँ, और सिपाही मेरे हाथ में हैं, और जब एक से कहता हूँ, जा, तो वह जाता है; और दूसरे को कि आ, तो वह आता है; और अपने दास से कहता हूँ, कि यह कर, तो वह करता है।”
10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba.
१०यह सुनकर यीशु ने अचम्भा किया, और जो उसके पीछे आ रहे थे उनसे कहा, “मैं तुम से सच कहता हूँ, कि मैंने इस्राएल में भी ऐसा विश्वास नहीं पाया।
11 Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama.
११और मैं तुम से कहता हूँ, कि बहुत सारे पूर्व और पश्चिम से आकर अब्राहम और इसहाक और याकूब के साथ स्वर्ग के राज्य में बैठेंगे।
12 Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.”
१२परन्तु राज्य के सन्तानबाहर अंधकार में डाल दिए जाएँगे: वहाँ रोना और दाँतों का पीसना होगा।”
13 Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke.
१३और यीशु ने सूबेदार से कहा, “जा, जैसा तेरा विश्वास है, वैसा ही तेरे लिये हो।” और उसका सेवक उसी समय चंगा हो गया।
14 Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi.
१४और यीशु ने पतरस के घर में आकर उसकी सास को तेज बुखार में पड़ा देखा।
15 Yesu ya taba hannunta, zazzabin ya sake ta, ta kuma tashi ta fara yi masa hidima.
१५उसने उसका हाथ छुआ और उसका ज्वर उतर गया; और वह उठकर उसकी सेवा करने लगी।
16 Da maraice ya yi, sai mutanen suka kakkawo wa Yesu masu aljanu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljanun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.
१६जब संध्या हुई तब वे उसके पास बहुत से लोगों को लाए जिनमें दुष्टात्माएँ थीं और उसने उन आत्माओं को अपने वचन से निकाल दिया, और सब बीमारों को चंगा किया।
17 Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.”
१७ताकि जो वचन यशायाह भविष्यद्वक्ता के द्वारा कहा गया था वह पूरा हो: “उसने आप हमारी दुर्बलताओं को ले लिया और हमारी बीमारियों को उठा लिया।”
18 Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili.
१८यीशु ने अपने चारों ओर एक बड़ी भीड़ देखकर झील के उस पार जाने की आज्ञा दी।
19 Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”
१९और एक शास्त्री ने पास आकर उससे कहा, “हे गुरु, जहाँ कहीं तू जाएगा, मैं तेरे पीछे-पीछे हो लूँगा।”
20 Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.”
२०यीशु ने उससे कहा, “लोमड़ियों के भट और आकाश के पक्षियों के बसेरे होते हैं; परन्तुमनुष्य के पुत्रके लिये सिर धरने की भी जगह नहीं है।”
21 Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.”
२१एक और चेले ने उससे कहा, “हे प्रभु, मुझे पहले जाने दे, कि अपने पिता को गाड़ दूँ।”
22 Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.”
२२यीशु ने उससे कहा, “तू मेरे पीछे हो ले; औरमुर्दों को अपने मुर्दे गाड़ने दे।”
23 Da Yesu ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi.
२३जब वह नाव पर चढ़ा, तो उसके चेले उसके पीछे हो लिए।
24 Sai ga wata babbar iska ta taso a tekun, har rakuman ruwa suka fara shan kan jirgin. Amma Yesu yana barci.
२४और, झील में एक ऐसा बड़ा तूफान उठा कि नाव लहरों से ढँपने लगी; और वह सो रहा था।
25 Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”
२५तब उन्होंने पास आकर उसे जगाया, और कहा, “हे प्रभु, हमें बचा, हम नाश हुए जाते हैं।”
26 Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit.
२६उसने उनसे कहा, “हे अल्पविश्वासियों, क्यों डरते हो?” तब उसने उठकर आँधी और पानी को डाँटा, और सब शान्त हो गया।
27 Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”.
२७और वे अचम्भा करके कहने लगे, “यह कैसा मनुष्य है, कि आँधी और पानी भी उसकी आज्ञा मानते हैं।”
28 Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya.
२८जब वह उस पार गदरेनियों के क्षेत्र में पहुँचा, तो दो मनुष्य जिनमें दुष्टात्माएँ थीं कब्रों से निकलते हुए उसे मिले, जो इतने प्रचण्ड थे, कि कोई उस मार्ग से जा नहीं सकता था।
29 Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”
२९और, उन्होंने चिल्लाकर कहा, “हे परमेश्वर के पुत्र, हमारा तुझ से क्या काम? क्या तू समय से पहले हमें दुःख देने यहाँ आया है?”
30 To akwai wani garken aladu masu yawa na kiwo, babu nisa da su.
३०उनसे कुछ दूर बहुत से सूअरों का झुण्ड चर रहा था।
31 Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”
३१दुष्टात्माओं ने उससे यह कहकर विनती की, “यदि तू हमें निकालता है, तो सूअरों के झुण्ड में भेज दे।”
32 “Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa.
३२उसने उनसे कहा, “जाओ!” और वे निकलकर सूअरों में घुस गई और सारा झुण्ड टीले पर से झपटकर पानी में जा पड़ा और डूब मरा।
33 Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun.
३३और चरवाहे भागे, और नगर में जाकर ये सब बातें और जिनमें दुष्टात्माएँ थीं; उनका सारा हाल कह सुनाया।
34 Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu.
३४और सारे नगर के लोग यीशु से भेंट करने को निकल आए और उसे देखकर विनती की, कि हमारे क्षेत्र से बाहर निकल जा।

< Mattiyu 8 >