< Mattiyu 7 >
1 Kada ku yi hukunci, domin ku ma kada a hukunta ku. Domin da irin hukuncin da ku kan hukunta da shi za a hukunta ku.
Dømmer ikke, for at I ikke skulle dømmes; thi med hvad Dom I dømme, skulle I dømmes,
2 Mudun da kukan auna, da shi za a auna maku.
og med hvad Maal I maale, skal der tilmaales eder.
3 Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba?
Men hvorfor ser du Skæven, som er i din Broders Øje, men Bjælken i dit eget Øje bliver du ikke var?
4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon?
Eller hvorledes kan du sige til din Broder: Lad mig drage Skæven ud af dit Øje; og se, Bjælken er i dit eget Øje.
5 Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka.
Du Hykler! drag først Bjælken ud af dit Øje, og da kan du se klart til at tage Skæven ud af din Broders Øje.
6 Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku.
Giver ikke Hunde det hellige, kaster ikke heller eders Perler for Svin, for at de ikke skulle nedtræde dem med deres Fødder og vende sig og sønderrive eder.
7 Roka, kuma za a ba ku. Nema, kuma za ku samu. Kwankwasa kuma za a bude maku.
Beder, saa skal eder gives; søger, saa skulle I finde; banker paa, saa skal der lukkes op for eder.
8 Ai duk wanda ya roka, zai karba, kuma duk wanda ya nema zai samu, wanda ya kwankwasa kuma za a bude masa.
Thi hver den, som beder, han faar, og den, som søger, han finder, og den, som banker paa, for ham skal der lukkes op.
9 Ko, kuwa wane mutum ne a cikin ku, dan sa zai roke shi gurasa, ya ba shi dutse?
Eller hvilket Menneske er der iblandt eder, som, naar hans Søn beder ham om Brød, vil give ham en Sten?
10 Ko kuwa in ya roke shi kifi, zai ba shi maciji?
Eller naar han beder ham om en Fisk, mon han da vil give ham en Slange?
11 Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa?
Dersom da I, som ere onde, vide at give eders Børn gode Gaver, hvor meget mere skal eders Fader, som er i Himlene, give dem gode Gaver, som bede ham!
12 Saboda haka, duk abinda ku ke so mutane su yi maku, ku ma sai ku yi masu, domin wannan shi ne dukan shari'a da koyarwar annabawa.
Altsaa, alt hvad I ville, at Menneskene skulle gøre imod eder, det skulle ogsaa I gøre imod dem; thi dette er Loven og Profeterne.
13 Ku shiga ta matsattsiyar kofa, don kofar zuwa hallaka na da fadi, hanyar ta mai saukin bi ce, masu shiga ta cikin ta suna da yawa.
Gaar ind ad den snævre Port; thi den Port er vid, og den Vej er bred, som fører til Fortabelsen, og de ere mange, som gaa ind ad den;
14 Domin kofar zuwa rai matsattsiya ce, hanyar ta mai wuyar bi ce, masu samun ta kuwa kadan ne.
thi den Port er snæver, og den Vej er trang, som fører til Livet, og de ere faa, som finde den.
15 Ku kula da annabawan karya, wadanda su kan zo maku da siffar tumaki, amma a gaskiya kyarketai ne masu warwashewa.
Men vogter eder for de falske Profeter, som komme til eder i Faareklæder, men indvortes ere glubende Ulve.
16 Za ku gane su ta irin ''ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya?
Af deres Frugter skulle I kende dem. Sanker man vel Vindruer af Torne eller Figener af Tidsler?
17 Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya.
Saaledes bærer hvert godt Træ gode Frugter, men det raadne Træ bærer slette Frugter.
18 Kyakkyawan itace ba zai taba haifar da munanan 'ya'ya ba, haka kuma mummunan itace ba zai taba haifar da kyawawan 'ya'ya ba.
Et godt Træ kan ikke bære slette Frugter, og et raaddent Træ kan ikke bære gode Frugter.
19 Duk itacen da ba ya ba da 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.
Hvert Træ, som ikke bærer god Frugt, omhugges og kastes i Ilden.
20 Domin haka, ta irin 'ya'yansu za a gane su.
Altsaa skulle I kende dem af deres Frugter.
21 Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama.
Ikke enhver, som siger til mig: Herre, Herre! skal komme ind i Himmeriges Rige, men den, der gør min Faders Villie, som er i Himlene.
22 A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?'
Mange skulle sige til mig paa hin Dag: Herre, Herre! have vi ikke profeteret ved dit Navn, og have vi ikke uddrevet onde Aander ved dit Navn, og have vi ikke gjort mange kraftige Gerninger ved dit Navn?
23 Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!'
Og da vil jeg bekende for dem: Jeg kendte eder aldrig; viger bort fra mig, I, som øve Uret!
24 Saboda haka, dukan wanda yake jin maganata, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidan sa a bisa dutse.
Derfor, hver den, som hører disse mine Ord og gør efter dem, ham vil jeg ligne ved en forstandig Mand, som byggede sit Hus paa Klippen,
25 Da ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, iska ta taso ta buga gidan, amma bai fadi ba, domin an gina shi bisa dutse.
og Skylregnen faldt, og Floderne kom, og Vindene blæste og sloge imod dette Hus, og det faldt ikke; thi det var grundfæstet paa Klippen.
26 Amma duk wanda ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta ba, za a misalta shi da wawan mutum da ya gina gidansa a kan rairayi.
Og hver den, som hører disse mine Ord og ikke gør efter dem, skal lignes ved en Daare, som byggede sit Hus paa Sandet,
27 Ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, sai iska ta taso ta buga gidan. Sai kuma ya rushe, ya kuwa yi cikakkiyar ragargajewa.''
og Skylregnen faldt, og Floderne kom, og Vindene blæste og stødte imod dette Hus, og det faldt, og dets Fald var stort.”
28 Ya zama sa'adda Yesu ya gama fadin wadannan maganganu, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa,
Og det skete, da Jesus havde fuldendt disse Ord, vare Skarerne slagne af Forundring over hans Lære;
29 Domin yana koya masu da iko, ba kamar marubuta ba.
thi han lærte dem som en, der havde Myndighed, og ikke som deres skriftkloge.