< Mattiyu 28 >

1 Da daddare ranar Asabaci, rana ta fari ga mako ta fara gabatowa, Maryamu Magadaliya da daya Maryamun suka zo don su ziyarci kabarin.
Vespere autem Sabbati, quæ lucescit in prima Sabbati, venit Maria Magdalene, et altera Maria videre sepulchrum.
2 Sai aka yi girgizar kasa mai karfi, saboda mala'ikan Ubangiji ya sauko daga sama ya kuma murgine dutsen ya zauna a kai.
Et ecce terræmotus factus est magnus. Angelus enim Domini descendit de cælo: et accedens revolvit lapidem, et sedebat super eum:
3 Kamanninsa kamar walkiya, tufafinsa kuma fari fat kamar suno.
erat autem aspectus eius sicut fulgur: et vestimentum eius sicut nix.
4 Masu tsaron suka razana don tsoro suka zama kamar matattun mutane.
Præ timore autem eius exterriti sunt custodes, et facti sunt velut mortui.
5 Mala'ikan ya yi wa matan magana cewa, “Kada ku ji tsoro, nasan kuna neman Yesu wanda aka gicciye.
Respondens autem Angelus dixit mulieribus: Nolite timere vos: scio enim, quod Iesum, qui crucifixus est, quæritis.
6 Baya nan, amma ya tashi kamar yadda ya fada. Ku zo ku ga wurin da aka kwantar da shi.
non est hic: surrexit enim, sicut dixit. Venite, et videte locum, ubi positus erat Dominus.
7 Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku.”
Et cito euntes, dicite discipulis eius quia surrexit: et ecce præcedit vos in Galilæam: ibi eum videbitis. Ecce prædixi vobis.
8 Matan suka yi hanzari suka bar kabarin da tsoro da murna, suka ruga domin su sanar wa almajiransa.
Et exierunt cito de monumento cum timore, et gaudio magno, currentes nunciare discipulis eius.
9 Sai ga Yesu ya tare su, yace masu, “A gaishe ku.” Sai matan suka kama kafar sa, suka kuma yi masa sujada.
Et ecce Iesus occurrit illis, dicens: Avete. Illæ autem accesserunt, et tenuerunt pedes eius, et adoraverunt eum.
10 Sai Yesu yace masu, “Kada ku ji tsoro. Ku je ku fada wa 'yan'uwana su je Galili. Can zasu ganni.”
Tunc ait illis Iesus: Nolite timere. Ite, nunciare fratribus meis ut eant in Galilæam; ibi me videbunt.
11 Sa'adda matan suke tafiya, sai wadansu masu tsaro suka shiga gari suka fada wa Shugabanin Firistoci dukan abin da ya faru.
Quæ cum abiissent, ecce quidam de custodibus venerunt in civitatem, et nunciaverunt principibus sacerdotum omnia, quæ facta fuerant.
12 Firistocin suka hadu da dattawa suka tattauna al'amarin, sai suka bada kudi masu yawa ga sojojin
Et congregati cum senioribus consilio accepto, pecuniam copiosam dederunt militibus,
13 Sukace masu, “Ku gaya wa sauran cewa, “Almajiran Yesu sun zo da daddare sun sace gangar jikinsa lokacin da muke barci.”
dicentes: Dicite quia discipuli eius nocte venerunt, et furati sunt eum, nobis dormientibus.
14 Idan wannan rahoto ya isa wurin gwamna, za mu lallashe shi mu ja hankalinsa mu raba ku da damuwa.”
Et si hoc auditum fuerit a præside, nos suadebimus ei, et securos vos faciemus.
15 Sai sojojin suka karbi kudin suka yi abinda aka umarcesu. Wannan rahoto ya bazu a tsakanin Yahudawa, ya ci gaba har zuwa yau.
At illi accepta pecunia, fecerunt sicut erant edocti. Et divulgatum est verbum istud apud Iudæos, usque in hodiernum diem.
16 Amma almajiran sha daya suka tafi Galili, kan dutsen da Yesu ya umarcesu.
Undecim autem discipuli abierunt in Galilæam in montem, ubi consituerat illis Iesus.
17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma wadansu suka yi shakka.
Et videntes eum adoraverunt: quidam autem dubitaverunt.
18 Yesu ya zo wurin su ya yi masu magana, yace, “Dukan iko dake sama da kasa an ba ni.
Et accedens Iesus locutus est eis, dicens: Data est mihi omnis potestas in cælo, et in terra.
19 Sai kuje ku almajirantar da dukan al'ummai. Kuna yi masu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki.
Euntes ergo docete omnes gentes: baptizantes eos in nomine Patris, et Filii, et Spiritus Sancti:
20 Ku koya masu su kiyaye dukan abin da na umarce ku. Duba, ni kuma kullum ina tare da ku har karshen zamani.” (aiōn g165)
docentes eos servare omnia quæcumque mandavi vobis: et ecce ego vobiscum sum omnibus diebus, usque ad consummationem sæculi. (aiōn g165)

< Mattiyu 28 >