< Mattiyu 26 >
1 Yayin da Yesu ya gama fadi masu wadannan maganganu, sai ya cewa almajiransa,
2 “Kun sani sauran kwana biyu idin ketarewa ya zo, kuma za'a bada Dan mutum domin a gicciye shi.
3 Sa'annan manyan firistoci da dattawan jama'a suka taru a fadar babban firist, mai suna Kayafa.
4 Suka shirya yadda zasu kama Yesu a boye su kuma kashe shi.
5 Amma suna cewa, “Ba a lokacin idin ba, domin kada tarzoma ta tashi daga cikin mutane.”
6 Sa'adda Yesu yake Baita'anya a gidan Saminu Kuturu,
7 daidai lokacin da ya zauna a gefen teburin cin abinci, sai wata mata ta shigo da kwalbar mai, mai tsada, ta zuba wa Yesu a kansa.
8 Amma da almajiransa suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Ina dalilin yin irin wannan asara?
9 Ai da an sayar da wannan mai da kudi mai yawa a rabawa talakawa.”
10 Amma da yake Yesu ya san tunaninsu, sai yace masu, “Don me kuke damun matar nan? Ta yi abu mai kyau domina.
11 Kuna da talakawa tare da ku koyaushe, amma ni ba zan kasance da ku ba koyaushe.
12 Don a sa'adda ta zuba man nan a jikina, ta yi haka ne don jana'iza ta.
13 Hakika Ina gaya maku, duk inda za ayi wannan bishara a dukan duniya, abin da matar nan tayi za'a rika ambatar da shi don tunawa da ita.”
14 Sai daya daga cikin sha biyun, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya tafi wurin manyan firistocin,
15 yace, ''Me kuke da niyyar bani idan na mika maku shi?” Suka auna masa azurfa talatin.
16 Daga wannan lokacin yayi ta neman zarafi da zai bada shi a wurinsu.
17 To a rana ta fari na idin ketarewa almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Ina kake so mu shirya maka da zaka ci abincin idin ketarewa?”
18 Yace, “Ku shiga cikin birnin zaku sami wani mutum sai kuce masa, 'Mallam yace, “lokaci na ya kusa. Zan ci idin ketarewa a gidanka, da almajiraina.”'''
19 Almajiran suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su, suka shirya abincin idin ketarewar.
20 Da yamma ta yi, sai ya zauna domin ya ci tare da almajiransa goma sha biyu.
21 Sa'adda suke ci, yace, “Hakika ina gaya maku, daya daga cikin ku zai bada ni.”
22 Suka yi bakin ciki, suka fara tambayarsa daya bayan daya, ''Na tabbata ba ni bane ko, Ubangiji?”
23 Sai ya amsa, “Wanda ke sa hannu tare da ni cikin kwano daya shi ne zai bada ni.
24 Dan mutum zai tafi, kamar yadda aka rubuta akan sa. Amma kaiton mutumin da ta wurin sa za'a bada Dan mutum! Gwamma da ba'a haifi mutumin nan ba.”
25 Yahuza da zai bada shi yace, “Mallam ko ni ne?” Yace masa, “Ka fada da kanka.”
26 Yayin da suke ci, sai Yesu ya dauki gurasa, ya sa albarka, ya karya. Ya ba almajiran yace, “Ku karba, ku ci, wannan jiki nane.”
27 Sai ya dauki kokon yayi godiya, Ya ba su yace, “Ku sha, dukanku.
28 “Gama wannan jinina ne na alkawari wanda aka zubar domin gafarar zunuban mutane da yawa.
29 Amma ina gaya maku, ba zan kara shan ruwan inabin nan ba, sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a cikin mulkin Ubana.”
30 Da suka raira waka, sai suka ka tafi dutsen zaitun.
31 Sai Yesu yace masu, “Dukan ku zaku yi tuntube a wannan dare sabili da ni, gama a rubuce yake, ''Zan bugi makiyayin, garken tumakin kuma za su watse.'
32 Amma bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa Galili.”
33 Amma Bitrus yace masa, “Ko dama duka zasu fadi sabili da kai, ni kam bazan fadi ba.”
34 Yesu yace masa, ''Hakika ina gaya maka, a wannan daren kafin carar zakara, za ka yi musun sani na sau uku.”
35 Bitrus yace masa, koda zan mutu tare da kai, bazan yi musunka ba.” Sai sauran almajiran suma suka fadi haka.
36 Sa'anna Yesu ya tafi tare da su, wurin da ake kira Getsaimani sai yace wa almajiransa, ''Ku zauna a nan ni kuma zan je gaba in yi addu'a.”
37 Ya dauki Bitrus da kuma 'ya'ya biyu na Zabadi tare da shi, sai ya fara damuwa da juyayi.
38 Sai yace masu, “Raina na cikin damuwa sosai har ga mutuwa. Ku kasance anan kuna tsaro tare da ni.”
39 Ya dan taka zuwa gaba kadan, sai ya fadi a fuskarsa, yayi addu'a. Yace, “Ya Ubana, in zai yiwu, bari kokon nan ya wuce ni. Duk da haka, ba nufina za'a bi ba, amma naka nufin.”
40 Ya koma wurin almajiran ya same su suna barci, sai ya cewa Bitrus, “Kai, ba zaku yi tsaro tare da ni ba koda sa'a daya?
41 Ku yi tsaro kuma, kuyi addu'a domin kada ku fada cikin jaraba. Ruhu dai ya yarda amma, jiki ba karfi.”
42 Sai ya koma karo na biyu yayi addu'a, Yace, “Ya Ubana, in wannan kokon ba zai wuce ba sai na sha shi, bari nufinka ya kasance.”
43 Ya sake dawowa, ya same su suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi.
44 Sai ya sake barinsu ya tafi. Ya koma karo na uku yana addu'a yana fadin kalmomi iri daya.
45 Sai Yesu ya koma wurin almajiran yace masu, “Har yanzu barci kuke kuna hutawa? Duba, lokaci ya kusato, kuma an bada Dan mutum ga hannun masu zunubi.
46 Ku tashi mu tafi. Duba, wanda zai badani ya kusato.”
47 Sa'adda yana cikin magana Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya zo. Babban taro ya zo tare da shi daga wurin manyan firistoci da dattawan jama'a. Suna rike da takubba da kulake.
48 To mutumin da zai bada Yesu ya rigaya ya basu alama, cewa, ''Duk wanda na sumbata, shine. Ku kama shi.''
49 Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, “Gaisuwa, Mallam!” sai ya sumbace shi.
50 Yesu kuwa yace masa, “Aboki, kayi abin da ya kawo ka.” Sai suka iso suka sa hannuwansu kan Yesu suka kama shi.
51 Nan take, daya daga cikin wadanda suke tare da Yesu ya mika hannunsa, ya zare takobinsa, ya sare wa bawan babban firist din kunne.
52 Sai Yesu yace, masa, “Ka maida takobinka cikin kubensa, domin duk wadanda suka dauki takobi su ma ta wurin takobi za su hallaka.
53 Ko kana tunanin ba zan iya kiran Ubana ba, ya kuma aiko da rundunar Mala'iku fiye da goma sha biyu?
54 Amma to tayaya za'a cika nassi, cewa dole wannan ya faru?''
55 A wannan lokacin Yesu yace wa taron, “Kun zo da takubba da kulake ku kama ni kamar dan fashi? Ina zaune kowace rana a haikali ina koyarwa, amma baku kama ni ba.
56 Amma duk wannan ya faru ne don a cika abinda annabawa suka rubuta.” Bayan haka sai dukkan almajiran suka bar shi suka gudu.
57 Wadanda suka kama Yesu, suka kai shi wurin Kayafa babban firist, inda marubuta da duttawan jama'a suka taru.
58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har zuwa farfajiyar babban firist din. Ya shiga ya zauna da masu tsaro domin ya ga abinda zai faru.
59 A wannan lokaci manyan firistoci da duk 'yan majalisar suka fara neman shaidar karya akan Yesu, domin su samu su kashe shi.
60 Amma ba su samu ko daya ba, ko dayake an samu shaidun karya dayawa da suka gabata. Amma daga baya sai wasu su biyu suka fito
61 sukace ''Wannan mutum yace zan iya rushe haikalin Allah, in kuma gina shi cikin kwana uku.'''
62 Babban Firist din ya tashi tsaye yace masa, “Ba zaka ce komai ba? Wace irin shaida ce ake yi akanka?”
63 Amma Yesu yayi shiru. Babban Firist ya ce, “Na umarce ka da sunan Allah mai rai, ka gaya mana ko kai Almasihu ne, Dan Allah.''
64 Yesu ya amsa masa, “Ka fada da bakin ka. Amma ina gaya maka, daga yanzu zaka ga Dan mutun na zaune a hannun dama na iko, ya na zuwa akan gizagizai na sama.”
65 Sai babban firist din ya yayyaga rigarsa, yana cewa, “Yayi sabo! don me ku ke neman wata shaida kuma? Duba, yanzu kun ji sabon.
66 Menene tunaninku?” Suka amsa sukace, “Ya cancanci mutuwa.”
67 Sai suka tofa masa yawu a fuska, suka kuma yi masa duka, suka kuma mammare shi da tafin hannuwansu,
68 sukace, ''Ka yi mana anabci, kai Almasihu. Wanene wanda ya dokeka.
69 To Bitrus kuwa na zaune a farfajiyar, sai wata yarinya baiwa ta zo wurinsa tana cewa, “Kaima kana tare da Yesu na Galili.”
70 Amma ya yi musun haka a gaban su duka, yace, “Ban ma san abinda kike magana akai ba.”
71 Da ya fita zuwa bakin kofa, nan ma wata yarinyar baiwa ta gan shi tace wa wadanda suke wurin, “Wannan mutumin ma yana tare da Yesu Banazare.”
72 Sai yayi musun haka kuma, har da rantsuwa, yace, “Ban san mutumin nan ba.”
73 Bayan dan lokaci kadan wadanda suke a tsaye suka zo wurin Bitrus suka ce masa, “Hakika kai daya daga cikin su ne, gama harshen ka ya tonaka.”
74 Sai ya fara rantsuwa irin ta la'ana, yana cewa, ''Ban san wannan mutumin ba,” nan da nan zakara yayi cara.
75 Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya fada, “Kafin carar zakara zaka yi musun sani na sau uku.” Sai ya fita waje yayi kuka mai zafi.''