< Mattiyu 24 >

1 Yesu ya fita daga cikin haikalin ya kama hanyar sa. Almajiran sa suka zo suna nuna masa ginin haikali.
Καὶ ἐξελθὼν ὁ Ἰησοῦς ἀπὸ τοῦ ἱεροῦ ἐπορεύετο, καὶ προσῆλθον οἱ μαθηταὶ αὐτοῦ ἐπιδεῖξαι αὐτῷ τὰς οἰκοδομὰς τοῦ ἱεροῦ.
2 Amma ya amsa masu yace, “kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za'a bari akan dan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba.”
ὁ δὲ ἀποκριθεὶς εἶπεν αὐτοῖς Οὐ βλέπετε ταῦτα πάντα; ἀμὴν λέγω ὑμῖν, οὐ μὴ ἀφεθῇ ὧδε λίθος ἐπὶ λίθον ὃς οὐ καταλυθήσεται.
3 Yayin da ya zauna a kan dutsen zaitun, almajiran sa suka zo wurin sa a boye suka ce, “me zai zama alamar zuwanka da kuma na karshen duniya?” (aiōn g165)
Καθημένου δὲ αὐτοῦ ἐπὶ τοῦ ὄρους τῶν Ἐλαιῶν προσῆλθον αὐτῷ οἱ μαθηταὶ κατ’ ἰδίαν λέγοντες Εἰπὲ ἡμῖν, πότε ταῦτα ἔσται, καὶ τί τὸ σημεῖον τῆς σῆς παρουσίας καὶ συντελείας τοῦ αἰῶνος; (aiōn g165)
4 Yesu ya amsa yace dasu, “Ku kula kada wani yasa ku kauce.”
καὶ ἀποκριθεὶς ὁ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτοῖς Βλέπετε μή τις ὑμᾶς πλανήσῃ.
5 Gama da yawa za su zo da sunana. Za su ce, “ni ne almasihu,” kuma za su sa da yawa su kauce.
πολλοὶ γὰρ ἐλεύσονται ἐπὶ τῷ ὀνόματί μου λέγοντες Ἐγώ εἰμι ὁ Χριστός, καὶ πολλοὺς πλανήσουσιν.
6 Za ku ji labarin yake-yake da kuma shelar yake-yake. Ku kula kar ku tsorata, domin dole abubuwan nan su faru; amma karshen dai tukunna.
μελλήσετε δὲ ἀκούειν πολέμους καὶ ἀκοὰς πολέμων· ὁρᾶτε, μὴ θροεῖσθε· δεῖ γὰρ γενέσθαι, ἀλλ’ οὔπω ἐστὶν τὸ τέλος.
7 Gama al'umma zata tayarwa al'umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za'a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam.
ἐγερθήσεται γὰρ ἔθνος ἐπὶ ἔθνος καὶ βασιλεία ἐπὶ βασιλείαν, καὶ ἔσονται λιμοὶ καὶ σεισμοὶ κατὰ τόπους·
8 Amma dukkan wadannan farkon ciwon haihuwa ne kawai.
πάντα δὲ ταῦτα ἀρχὴ ὠδίνων.
9 Bayan haka za'a bada ku ga tsanani a kuma kashe ku. Dukkan al'ummai za su tsane ku saboda sunana.
τότε παραδώσουσιν ὑμᾶς εἰς θλῖψιν καὶ ἀποκτενοῦσιν ὑμᾶς, καὶ ἔσεσθε μισούμενοι ὑπὸ πάντων τῶν ἐθνῶν διὰ τὸ ὄνομά μου.
10 Daga nan da yawa za su yi tuntube, kuma su ci amanar juna, su kuma tsani juna.
καὶ τότε σκανδαλισθήσονται πολλοὶ καὶ ἀλλήλους παραδώσουσιν καὶ μισήσουσιν ἀλλήλους·
11 Annabawan karya da yawa za su taso kuma susa da yawa su kauce.
καὶ πολλοὶ ψευδοπροφῆται ἐγερθήσονται καὶ πλανήσουσιν πολλούς·
12 Domin mugunta zata ribambanya, kaunar masu yawa zata yi sanyi.
καὶ διὰ τὸ πληθυνθῆναι τὴν ἀνομίαν ψυγήσεται ἡ ἀγάπη τῶν πολλῶν.
13 Amma duk wanda ya jure har karshe, zai sami ceto.
ὁ δὲ ὑπομείνας εἰς τέλος, οὗτος σωθήσεται.
14 Za'a yi wa'azin wannan bisharar mulkin a dukkan duniya don ya zama shaida akan dukkan al'ummai. Daganan karshen zai zo.
καὶ κηρυχθήσεται τοῦτο τὸ εὐαγγέλιον τῆς βασιλείας ἐν ὅλῃ τῇ οἰκουμένῃ εἰς μαρτύριον πᾶσιν τοῖς ἔθνεσιν, καὶ τότε ἥξει τὸ τέλος.
15 Don haka, idan kun ga abin kyama mai lalatarwa, wanda Annabi Daniyel ya yi maganar sa, Ya tsaya a wuri mai tsarki (bari mai karatu ya fahimta),
Ὅταν οὖν ἴδητε τὸ βδέλυγμα τῆς ἐρημώσεως τὸ ῥηθὲν διὰ Δανιὴλ τοῦ προφήτου ἑστὸς ἐν τόπῳ ἁγίῳ, ὁ ἀναγινώσκων νοείτω,
16 bari wadanda ke yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu,
τότε οἱ ἐν τῇ Ἰουδαίᾳ φευγέτωσαν εἰς τὰ ὄρη,
17 Bari wanda yake kan bene kada ya sauko don daukar wani abu a cikin gidansa,
ὁ ἐπὶ τοῦ δώματος μὴ καταβάτω ἆραι τὰ ἐκ τῆς οἰκίας αὐτοῦ,
18 kuma wanda yake gona kar ya dawo gida domin daukar babbar rigarsa.
καὶ ὁ ἐν τῷ ἀγρῷ μὴ ἐπιστρεψάτω ὀπίσω ἆραι τὸ ἱμάτιον αὐτοῦ.
19 Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin!
οὐαὶ δὲ ταῖς ἐν γαστρὶ ἐχούσαις καὶ ταῖς θηλαζούσαις ἐν ἐκείναις ταῖς ἡμέραις.
20 Ku yi addu'a kada gudun ku ya zama lokacin hunturu, ko ranan asabaci.
προσεύχεσθε δὲ ἵνα μὴ γένηται ἡ φυγὴ ὑμῶν χειμῶνος μηδὲ σαββάτῳ·
21 Domin za'ayi tsanani mai girma, wanda ba'a taba yin irin shi ba, tun farkon duniya har ya zuwa yau, a'a ba za ayi irin shi ba kuma.
ἔσται γὰρ τότε θλῖψις μεγάλη, οἵα οὐ γέγονεν ἀπ’ ἀρχῆς κόσμου ἕως τοῦ νῦν οὐδ’ οὐ μὴ γένηται.
22 In ba don an rage kwanakin ba, da ba mahalukin da zai tsira. Amma albarkacin zababbun, za a rage kwanakin.
καὶ εἰ μὴ ἐκολοβώθησαν αἱ ἡμέραι ἐκεῖναι, οὐκ ἂν ἐσώθη πᾶσα σάρξ· διὰ δὲ τοὺς ἐκλεκτοὺς κολοβωθήσονται αἱ ἡμέραι ἐκεῖναι.
23 Sa'annan idan wani yace maku, duba, “ga Almasihu a nan!” ko, “ga Almasihu a can!” kar ku gaskata.
τότε ἐάν τις ὑμῖν εἴπῃ Ἰδοὺ ὧδε ὁ Χριστός, ἤ Ὧδε, μὴ πιστεύσητε·
24 Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun.
ἐγερθήσονται γὰρ ψευδόχριστοι καὶ ψευδοπροφῆται, καὶ δώσουσιν σημεῖα μεγάλα καὶ τέρατα ὥστε πλανῆσαι, εἰ δυνατὸν, καὶ τοὺς ἐκλεκτούς.
25 Kun gani, na gaya maku kafin lokacin ya zo.
ἰδοὺ προείρηκα ὑμῖν.
26 Saboda haka, idan suka ce maku, “ga shi a jeji,” kar ku je jejin. Ko, “ga shi a can cikin kuryar daki,” kar ku gaskata.
ἐὰν οὖν εἴπωσιν ὑμῖν Ἰδοὺ ἐν τῇ ἐρήμῳ ἐστίν, μὴ ἐξέλθητε· Ἰδοὺ ἐν τοῖς ταμείοις, μὴ πιστεύσητε·
27 Yadda walkiya ke haskakawa daga gabas zuwa yamma, haka nan zuwan Dan mutum zai zama.
ὥσπερ γὰρ ἡ ἀστραπὴ ἐξέρχεται ἀπὸ ἀνατολῶν καὶ φαίνεται ἕως δυσμῶν, οὕτως ἔσται ἡ παρουσία τοῦ Υἱοῦ τοῦ ἀνθρώπου·
28 Duk inda mushe yake, nan ungulai suke taruwa.
ὅπου ἐὰν ᾖ τὸ πτῶμα, ἐκεῖ συναχθήσονται οἱ ἀετοί.
29 Amma nan da nan bayan kwanakin tsananin nan, rana za ta duhunta, wata kuma ba zai ba da haskensa ba, taurari kuma za su fado daga sama, ikokin sammai za su girgiza.
Εὐθέως δὲ μετὰ τὴν θλῖψιν τῶν ἡμερῶν ἐκείνων ὁ ἥλιος σκοτισθήσεται, καὶ ἡ σελήνη οὐ δώσει τὸ φέγγος αὐτῆς, καὶ οἱ ἀστέρες πεσοῦνται ἀπὸ τοῦ οὐρανοῦ, καὶ αἱ δυνάμεις τῶν οὐρανῶν σαλευθήσονται.
30 Sa'annan alamar Dan Mutum za ta bayyana a sararin sama, kuma dukkan kabilun duniya za su yi bakin ciki. Za su ga Dan Mutun na zuwa a gajimarai da iko da daukaka mai girma.
καὶ τότε φανήσεται τὸ σημεῖον τοῦ Υἱοῦ τοῦ ἀνθρώπου ἐν οὐρανῷ, καὶ τότε κόψονται πᾶσαι αἱ φυλαὶ τῆς γῆς καὶ ὄψονται τὸν Υἱὸν τοῦ ἀνθρώπου ἐρχόμενον ἐπὶ τῶν νεφελῶν τοῦ οὐρανοῦ μετὰ δυνάμεως καὶ δόξης πολλῆς·
31 Zai aiki mala'ikunsa, da karar kaho mai karfi, kuma za su tattara dukkan zababbu daga dukkan kusurwoyi hudu, daga karshen sararin sama har zuwa wani karshen.
καὶ ἀποστελεῖ τοὺς ἀγγέλους αὐτοῦ μετὰ σάλπιγγος μεγάλης, καὶ ἐπισυνάξουσιν τοὺς ἐκλεκτοὺς αὐτοῦ ἐκ τῶν τεσσάρων ἀνέμων ἀπ’ ἄκρων οὐρανῶν ἕως ἄκρων αὐτῶν.
32 Kuyi koyi da itacen baure. Da zaran reshen sa ya yi toho ya fara bada ganye, za ku sani bazara ta kusa.
Ἀπὸ δὲ τῆς συκῆς μάθετε τὴν παραβολήν· ὅταν ἤδη ὁ κλάδος αὐτῆς γένηται ἁπαλὸς καὶ τὰ φύλλα ἐκφύῃ, γινώσκετε ὅτι ἐγγὺς τὸ θέρος·
33 Haka kuma, idan kun ga dukkan wadannan abubuwa, ya kamata ku sani, Ya yi kusa, ya na bakin kofa.
οὕτως καὶ ὑμεῖς ὅταν ἴδητε πάντα ταῦτα, γινώσκετε ὅτι ἐγγύς ἐστιν ἐπὶ θύραις.
34 Ina gaya maku gaskiya, wannan zamanin ba zai wuce ba, sai dukkan wadannan abubuwan sun faru.
ἀμὴν λέγω ὑμῖν ὅτι οὐ μὴ παρέλθῃ ἡ γενεὰ αὕτη ἕως ἂν πάντα ταῦτα γένηται.
35 Sama da kasa za su shude, amma kalmomina ba za su shude ba.
ὁ οὐρανὸς καὶ ἡ γῆ παρελεύσεται, οἱ δὲ λόγοι μου οὐ μὴ παρέλθωσιν.
36 Amma game da ranan nan ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai Uban kadai.
Περὶ δὲ τῆς ἡμέρας ἐκείνης καὶ ὥρας οὐδεὶς οἶδεν, οὐδὲ οἱ ἄγγελοι τῶν οὐρανῶν οὐδὲ ὁ Υἱός, εἰ μὴ ὁ Πατὴρ μόνος.
37 Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka zai zama game da zuwan Dan Mutum.
ὥσπερ γὰρ αἱ ἡμέραι τοῦ Νῶε, οὕτως ἔσται ἡ παρουσία τοῦ Υἱοῦ τοῦ ἀνθρώπου.
38 A wadannan kwankin kafin zuwan ruwan tsufana suna ci suna sha, suna aure suna aurarwa har ranar da Nuhu ya shiga jirgin,
ὡς γὰρ ἦσαν ἐν ταῖς ἡμέραις ἐκείναις ταῖς πρὸ τοῦ κατακλυσμοῦ τρώγοντες καὶ πίνοντες, γαμοῦντες καὶ γαμίζοντες, ἄχρι ἧς ἡμέρας εἰσῆλθεν Νῶε εἰς τὴν κιβωτόν,
39 ba su san kome ba har ruwan ya zo ya cinye su haka ma zuwan Dan Mutun zai zama.
καὶ οὐκ ἔγνωσαν ἕως ἦλθεν ὁ κατακλυσμὸς καὶ ἦρεν ἅπαντας, οὕτως ἔσται καὶ ἡ παρουσία τοῦ Υἱοῦ τοῦ ἀνθρώπου.
40 Sa'annan mutane biyu zasu kasance a gona za a dauke daya, a bar daya a baya.
τότε ἔσονται δύο ἐν τῷ ἀγρῷ, εἷς παραλαμβάνεται καὶ εἷς ἀφίεται·
41 Mata biyu na nika a manika za a dauke daya, za a bar dayar.
δύο ἀλήθουσαι ἐν τῷ μύλῳ, μία παραλαμβάνεται καὶ μία ἀφίεται.
42 Don haka sai ku yi zaman tsaro, domin baku san ranar da Ubangijinku zai zo ba.
γρηγορεῖτε οὖν, ὅτι οὐκ οἴδατε ποίᾳ ἡμέρᾳ ὁ κύριος ὑμῶν ἔρχεται.
43 Amma ku san wannan, idan maigida ya san lokacin da barawo zai zo, zai zauna a shirye ba zai bar gidan sa har a balle a shiga ba.
ἐκεῖνο δὲ γινώσκετε ὅτι εἰ ᾔδει ὁ οἰκοδεσπότης ποίᾳ φυλακῇ ὁ κλέπτης ἔρχεται, ἐγρηγόρησεν ἂν καὶ οὐκ ἂν εἴασεν διορυχθῆναι τὴν οἰκίαν αὐτοῦ.
44 Don haka sai ku shirya, domin Dan Mutum zai zo a sa'ar da ba ku yi zato ba.
διὰ τοῦτο καὶ ὑμεῖς γίνεσθε ἕτοιμοι, ὅτι ᾗ οὐ δοκεῖτε ὥρᾳ ὁ Υἱὸς τοῦ ἀνθρώπου ἔρχεται.
45 To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci?
Τίς ἄρα ἐστὶν ὁ πιστὸς δοῦλος καὶ φρόνιμος ὃν κατέστησεν ὁ κύριος ἐπὶ τῆς οἰκετείας αὐτοῦ τοῦ δοῦναι αὐτοῖς τὴν τροφὴν ἐν καιρῷ;
46 Mai albarka ne bawan, da mai gidan zai same shi a kan aikin sa a lokacin da ya dawo.
μακάριος ὁ δοῦλος ἐκεῖνος ὃν ἐλθὼν ὁ κύριος αὐτοῦ εὑρήσει οὕτως ποιοῦντα·
47 Ina gaya maku gaskiya mai gidan zai dora shi a kan dukkan a binda yake da shi.
ἀμὴν λέγω ὑμῖν ὅτι ἐπὶ πᾶσιν τοῖς ὑπάρχουσιν αὐτοῦ καταστήσει αὐτόν.
48 Amma idan mugun bawa ya ce a zuciyarsa, “maigida na ya yi jinkiri,”
ἐὰν δὲ εἴπῃ ὁ κακὸς δοῦλος ἐκεῖνος ἐν τῇ καρδίᾳ αὐτοῦ Χρονίζει μου ὁ κύριος,
49 sai ya fara dukan sauran barorin, ya yi ta ci da sha tare da mashaya,
καὶ ἄρξηται τύπτειν τοὺς συνδούλους αὐτοῦ, ἐσθίῃ δὲ καὶ πίνῃ μετὰ τῶν μεθυόντων,
50 uban gidan bawan zai dawo a ranar da bawan bai zata ba, a lokacin da bai sani ba.
ἥξει ὁ κύριος τοῦ δούλου ἐκείνου ἐν ἡμέρᾳ ᾗ οὐ προσδοκᾷ καὶ ἐν ὥρᾳ ᾗ οὐ γινώσκει,
51 Uban gidansa zai datsa shi biyu, karshen sa zai zama daidai da na munafukai, za a sashi inda a ke kuka da cizon hakora.
καὶ διχοτομήσει αὐτὸν καὶ τὸ μέρος αὐτοῦ μετὰ τῶν ὑποκριτῶν θήσει· ἐκεῖ ἔσται ὁ κλαυθμὸς καὶ ὁ βρυγμὸς τῶν ὀδόντων.

< Mattiyu 24 >

The World is Destroyed by Water
The World is Destroyed by Water