< Mattiyu 23 >
1 Sai Yesu yayi wa taron da alamajiransa magana.
Then, Jesus spake unto the multitudes and unto his disciples,
2 Ya ce, “Marubuta da Farisawa suna zaune a mazaunin Musa.
saying—Upon Moses’ seat, have sat down, the Scribes and the Pharisees:
3 Don haka, duk abinda suka umarceku kuyi, kuyi wadannan abubuwa ku kuma kiyaye su. Amma kada kuyi koyi da ayyukansu, gama suna fadar abubuwa amma kuma ba su aikata su.
All things, therefore, whatsoever they tell you, do and observe, —but, according to their works, do ye not, for they, say, and do not, perform.
4 I, sukan daura kaya masu nauyi, masu wuyar dauka, daga nan su dauka su jibga wa mutane a kafada. Amma su kan su baza su mika danyatsa ba su dauka.
But they bind together heavy burdens, and lay upon men’s shoulders, whereas, they, with their finger, are not willing to move them.
5 Duk ayyukan su suna yi ne don mutane su gani, suna dinka aljihunan nassinsu da fadi, suna fadada iyakokin rigunansu.
But, all their works, they do, to be gazed at, by men, —for they make broad their amulets, and make large their fringes,
6 Su na son mafifitan wuraren zama a gidan biki, da mafifitan wuraren zama a majami'u,
And dearly love the first couch in the chief meals, and the first seats in the synagogues,
7 da kuma gaisuwar musamman a wuraren kasuwanci, a kuma rika ce da su 'mallam.'
And the salutations in the market-places, and to be called by men, Rabbi.
8 Amma ba sai an kira ku 'mallam, ba' domin malami daya kuke da shi, ku duka kuwa 'yan'uwan juna ne.
But, ye, —do not be called Rabbi, —for, one, is your Teacher, and, all ye, are brethren;
9 Kada ku kira kowa 'Ubanku' a duniya, domin Uba daya ne ku ke da shi, kuma yana sama.
And, father, be none of you called, upon the earth, for, one, is your Father, the Heavenly;
10 Kada kuma a kira ku malamai, saboda malamin ku daya ne, shi ne Almasihu.
Neither be called leaders, for, your leader, is one, the Christ;
11 Amma wanda yake babba a cikin ku zaya zama bawanku.
And, the greatest of you, shall be to you, a minister;
12 Duk wanda ya daukaka kansa za a kaskantar dashi. Duk wanda ya kaskantar da kansa kuma za a daukaka shi.
And, whoever shall exalt himself, shall be, abased, and, whoever shall abase himself, shall be, exalted,
13 Amma kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kun toshewa mutane kofar mulkin sama. Baku shiga ba, kuma ba ku bar wadanda suke so su sami shiga ba.
But alas for you, Scribes and Pharisees, hypocrites; because ye are locking up the kingdom of the heavens before men, —for, ye, are not entering, neither, them who are entering, suffer ye to enter.
14 kaiton ku marubuta da Farisawa, domin kuna hallaka gwauraya -
15 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kuna tafiya ketaren tekuna da kasashe domin samun almajiri daya tak, in kwa kun samu kukan mai da shi biyunku danwuta. (Geenna )
Alas for you, Scribes and Pharisees, hypocrites: because ye compass sea and dry land, to make one convert—and, when it is done, ye make him a son of gehenna, twofold more than ye. (Geenna )
16 Kaiton ku, makafin jagora, kuda kuke cewa, Kowa ya rantse da Haikali, ba komai. Amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, rantsuwarsa ta daure shi.'
Alas for you, blind guides! that say—Whosoever shall swear by the Temple, it is, nothing, but, whosoever shall swear by the gold of the Temple, is bound:
17 Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?
Foolish and blind! for which is, greater, The gold, or the Temple that hath hallowed the gold?
18 Kuma, 'Kowa ya rantse da bagadi, ba komai bane. Amma duk wanda ya rantse da baikon da aka dora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.'
And, whosoever shall swear by the altar, it is, nothing, but, whosoever shall swear by the gift that is upon it, is bound:
19 Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah?
Blind! for which is greater, The gift, or the altar that halloweth the gift?
20 Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagadi, ya rantse da shi da duk abinda ke kansa.
He therefore that hath sworn by the altar, sweareth by it, and by all that is upon it;
21 Kuma duk wanda ya rantse da Haikali ya rantse dashi da kuma wanda yake cikin sa.
And, he that hath sworn by the Temple, sweareth by it, and by him who dwelleth therein;
22 Kuma duk wanda ya rantse da sama, ya rantse da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune akai.
And, he that hath sworn by heaven, sweareth by the throne of God, and by him who sitteth thereupon.
23 Kaiton ku Farisawa da marubuta, munafukai! Kukan fitar da zakkar doddoya, da karkashi, da lamsur, amma kun yar da al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, da jinkai da bangaskiya. Wadannan ne ya kamata kuyi, ba tare da kunyi watsi da sauran ba.
Alas for you, Scribes and Pharisees, hypocrites; because ye tithe the mint and the anise and the cummin, —and have dismissed the weightier matters of the law—the justice, the mercy, and the faith; whereas, these, it was binding, to do, and, those, not to, dismiss.
24 Makafin jagora, ku kan burtsar da kwaro dan mitsil, amma kukan hadiye rakumi!
Blind guides! Straining out the gnat, but, the camel, swallowing.
25 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! kuna wanke bayan moda da kwano, amma aciki cike suke da zalunci da keta.
Alas for you, Scribes and Pharisees, hypocrites; because ye cleanse the outside of the cup and of the dish, —while, within, they are full of plunder and intemperance.
26 Kai makahon Bafarise! Sai ka fara tsarkake cikin modar da kwanon domin bayansu ma su tsarkaka.
Blind Pharisee! cleanse, first, the inside, of the cup [and of the dish], that, the outside thereof, may become, clean.
27 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar kasa kuke, masu kyaun gani daga waje, daga ciki kuwa sai kasusuwan matattu da kazanta iri iri.
Alas for you, Scribes and Pharisees, hypocrites; because ye make yourselves like sepulchres whitewashed, which, outside, indeed, appear, beautiful, but, within, are full, of dead men’s bones and all uncleanness, —
28 Haka nan kuke a idanun mutane ku adalai ne, amma a ciki sai munafunci da mugun aiki.
Thus, ye also, outside, indeed, appear to men, righteous, but, within, are full, of hypocrisy and lawlessness.
29 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Ku kan gina kaburburan annabawa, kuna kuma kawata kaburburan adalai.
Alas for you, Scribes and Pharisees, hypocrites; because ye build the sepulchres of the prophets, and adorn the monuments of the righteous,
30 Kuna cewa, 'Da muna nan a zamanin Ubanninmu, da bamu basu goyon baya ba wajen zubar da jinin annabawa.'
and say—If we had been in the days of our fathers, we would not have been their partners in the blood of the prophets:
31 Domin haka kun shaida kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.
So that ye bear witness against yourselves, that ye are, sons, of them who murdered the prophets.
32 Sai kuma kuka cika ma'aunin ubanninku!
And, ye, fill ye up the measure of your fathers!
33 macizai, Ku 'ya'yan ganshekai, Yaya zaku tsere wa hukuncin Gidan wuta? (Geenna )
Serpents! broods of vipers! how should ye flee from the judgment of gehenna? (Geenna )
34 Saboda haka, duba, ina aiko maku da annabawa, da masu hikima da marubuta. Za ku kashe wadansun su kuma ku gicciye su. Zaku yiwa wasu bulala a majami'un ku, kuna bin su gari gari.
For this cause, lo! I, send unto you, prophets and wise men and scribes, —some from among them, ye will slay and crucify, And some from among them ye will—scourge in your synagogues, and pursue from city to city:
35 Sakamakon hakan alhakin jinin dukkan adalai da aka zubar a duniya ya komo a kan ku, tun daga jinin Habila adali har ya zuwa na Zakariya dan Barakiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikali da bagadi.
That there may come upon you—all righteous blood poured out upon the earth, from the blood of Abel the righteous, unto the blood of Zachariah, son of Barachiah, whom ye murdered between the Temple and the altar.
36 Hakika, Ina gaya maku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.
Verily, I say unto you—All these things, will have come, upon this generation.
37 Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki.
Jerusalem! Jerusalem! that slayeth the prophets, and stoneth them that have been sent unto her, —how often, would I have gathered thy children, like as a hen gathereth her chickens under her wings, —and ye would not!
38 Ga shi an bar maku gidan ku a yashe!
Lo! your house is left to you;
39 Ina dai gaya maku, ba za ku kara gani na ba, sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji.”'
For I say unto you—in no wise, may ye see me, henceforth, until ye say, Blessed, is he that cometh, in the name of the Lord!