< Mattiyu 22 >

1 Yesu ya sake yi masu magana da misalai, yace,
Καὶ ἀποκριθεὶς ὁ Ἰησοῦς πάλιν εἶπεν αὐτοῖς ἐν παραβολαῖς λέγων·
2 “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure.
ὡμοιώθη ἡ βασιλεία τῶν οὐρανῶν ἀνθρώπῳ βασιλεῖ, ὅστις ἐποίησε γάμους τῷ υἱῷ αὐτοῦ.
3 Ya aiki bayinsa su kira wadanda aka gayyata su zo liyafar auren, amma suka ki zuwa.
καὶ ἀπέστειλε τοὺς δούλους αὐτοῦ καλέσαι τοὺς κεκλημένους εἰς τοὺς γάμους, καὶ οὐκ ἤθελον ἐλθεῖν.
4 Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.”
πάλιν ἀπέστειλεν ἄλλους δούλους λέγων· εἴπατε τοῖς κεκλημένοις· ἰδοὺ τὸ ἄριστόν μου ἡτοίμασα, οἱ ταῦροί μου καὶ τὰ σιτιστὰ τεθυμένα, καὶ πάντα ἕτοιμα· δεῦτε εἰς τοὺς γάμους.
5 Amma mutanen ba su dauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyarsu. Wani ga gonarsa, wani ga kasuwancinsa.
οἱ δὲ ἀμελήσαντες ἀπῆλθον, ὁ μὲν εἰς τὸν ἴδιον ἀγρόν, ὁ δὲ εἰς τὴν ἐμπορίαν αὐτοῦ·
6 Sauran kuma suka kama bayin sarkin, suka wulakanta su, suka kuma kashe su.
οἱ δὲ λοιποὶ κρατήσαντες τοὺς δούλους αὐτοῦ ὕβρισαν καὶ ἀπέκτειναν.
7 Amma sarkin ya ji haushi. Ya aika sojojinsa, ku kashe masu kisan kan nan, ku kuma kone birnin su.
ἀκούσας δὲ ὁ βασιλεὺς ἐκεῖνος ὠργίσθη, καὶ πέμψας τὰ στρατεύματα αὐτοῦ ἀπώλεσε τοὺς φονεῖς ἐκείνους καὶ τὴν πόλιν αὐτῶν ἐνέπρησε.
8 Sai ya ce wa bayinsa, 'An gama shirya bikin, amma wadanda aka gayyata ba su cancanta ba.
τότε λέγει τοῖς δούλοις αὐτοῦ· ὁ μὲν γάμος ἕτοιμός ἐστιν, οἱ δὲ κεκλημένοι οὐκ ἦσαν ἄξιοι·
9 Saboda haka ku je bakin hanya ku gayyaci iyakar yawan mutanen da za ku samu zuwa bukin auren.'
πορεύεσθε οὖν ἐπὶ τὰς διεξόδους τῶν ὁδῶν, καὶ ὅσους ἐὰν εὕρητε καλέσατε εἰς τοὺς γάμους.
10 Bayin suka tafi hanya suka tattaro dukan mutanen da suka samu, da masu kyau da marassa kyau. Zauren auren kuwa ya cika makil da baki.
καὶ ἐξελθόντες οἱ δοῦλοι ἐκεῖνοι εἰς τὰς ὁδοὺς συνήγαγον πάντας ὅσους εὗρον, πονηρούς τε καὶ ἀγαθούς· καὶ ἐπλήσθη ὁ γάμος ἀνακειμένων.
11 Amma da sarkin ya zo don ya ga bakin, sai ya ga wani wanda bai sa kayan aure ba.
εἰσελθὼν δὲ ὁ βασιλεὺς θεάσασθαι τοὺς ἀνακειμένους εἶδεν ἐκεῖ ἄνθρωπον οὐκ ἐνδεδυμένον ἔνδυμα γάμου,
12 Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.
καὶ λέγει αὐτῷ· ἑταῖρε, πῶς εἰσῆλθες ὧδε μὴ ἔχων ἔνδυμα γάμου; ὁ δὲ ἐφιμώθη.
13 Sai sarkin ya ce wa bayinsa, 'Ku daure mutumin nan hannu da kafa, ku jefa shi cikin duhun, inda za ayi kuka da cizon hakora.'
τότε εἶπεν ὁ βασιλεὺς τοῖς διακόνοις· δήσαντες αὐτοῦ πόδας καὶ χεῖρας ἄρατε αὐτὸν καὶ ἐκβάλετε εἰς τὸ σκότος τὸ ἐξώτερον· ἐκεῖ ἔσται ὁ κλαυθμὸς καὶ ὁ βρυγμὸς τῶν ὀδόντων.
14 Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba.”'
πολλοὶ γάρ εἰσι κλητοί, ὀλίγοι δὲ ἐκλεκτοί.
15 Sai Farisawan suka tafi suka shirya makirci akan yadda zasu kama shi ta maganarsa.
Τότε πορευθέντες οἱ Φαρισαῖοι συμβούλιον ἔλαβον ὅπως αὐτὸν παγιδεύσωσιν ἐν λόγῳ.
16 Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane.
καὶ ἀποστέλλουσιν αὐτῷ τοὺς μαθητὰς αὐτῶν μετὰ τῶν Ἡρῳδιανῶν λέγοντες· διδάσκαλε, οἴδαμεν ὅτι ἀληθὴς εἶ καὶ τὴν ὁδὸν τοῦ Θεοῦ ἐν ἀληθείᾳ διδάσκεις, καὶ οὐ μέλει σοι περὶ οὐδενός· οὐ γὰρ βλέπεις εἰς πρόσωπον ἀνθρώπων·
17 To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?”
εἰπὲ οὖν ἡμῖν, τί σοι δοκεῖ; ἔξεστι δοῦναι κῆνσον Καίσαρι ἢ οὔ;
18 Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, “Don me kuke gwada ni, ku munafukai?
γνοὺς δὲ ὁ Ἰησοῦς τὴν πονηρίαν αὐτῶν εἶπε· τί με πειράζετε, ὑποκριταί;
19 Ku nuna mani sulen harajin.” Sai suka kawo masa sulen.
ἐπιδείξατέ μοι τὸ νόμισμα τοῦ κήνσου. οἱ δὲ προσήνεγκαν αὐτῷ δηνάριον.
20 Yesu yace masu, “Hoto da sunan wanene wadannan?”
καὶ λέγει αὐτοῖς· τίνος ἡ εἰκὼν αὕτη καὶ ἡ ἐπιγραφή;
21 Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.”
λέγουσιν αὐτῷ· Καίσαρος. τότε λέγει αὐτοῖς· ἀπόδοτε οὖν τὰ Καίσαρος Καίσαρι καὶ τὰ τοῦ Θεοῦ τῷ Θεῷ.
22 Da suka ji haka, suka yi mamaki. Sai suka bar shi suka tafi.
καὶ ἀκούσαντες ἐθαύμασαν, καὶ ἀφέντες αὐτὸν ἀπῆλθον.
23 A ran nan sai wadansu Sadukiyawa, wadanda suka ce ba tashin matattu, suka zo wurinsa. Suka tambaye shi,
Ἐν ἐκείνῃ τῇ ἡμέρᾳ προσῆλθον αὐτῷ Σαδδουκαῖοι, οἱ λέγοντες μὴ εἶναι ἀνάστασιν, καὶ ἐπηρώτησαν αὐτὸν
24 cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya.
λέγοντες· διδάσκαλε, Μωσῆς εἶπεν, ἐάν τις ἀποθάνῃ μὴ ἔχων τέκνα, ἐπιγαμβρεύσει ὁ ἀδελφὸς αὐτοῦ τὴν γυναῖκα αὐτοῦ καὶ ἀναστήσει σπέρμα τῷ ἀδελφῷ αὐτοῦ.
25 Akwai wasu 'yan'uwa bakwai. Na farkon yayi aure sai ya mutu. Da shike bai bar 'ya'ya ba. Ya bar wa dan'uwansa matarsa.
ἦσαν δὲ παρ᾽ ἡμῖν ἑπτὰ ἀδελφοί· καὶ ὁ πρῶτος γαμήσας ἐτελεύτησε, καὶ μὴ ἔχων σπέρμα ἀφῆκε τὴν γυναῖκα αὐτοῦ τῷ ἀδελφῷ αὐτοῦ·
26 Sai dan'uwansa na biyu shi ma yayi haka, haka kuma na ukun, har zuwa dan'uwan na bakwai.
ὁμοίως καὶ ὁ δεύτερος καὶ ὁ τρίτος, ἕως τῶν ἑπτά.
27 Bayan dukansu, sai matar ta mutu.
ὕστερον δὲ πάντων ἀπέθανε καὶ ἡ γυνή.
28 To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.”
ἐν τῇ οὖν ἀναστάσει τίνος τῶν ἑπτὰ ἔσται ἡ γυνή; πάντες γὰρ ἔσχον αὐτήν.
29 Amma Yesu ya amsa yace masu, “Kun bata, domin ba ku san litattafai ko ikon Allah ba.
ἀποκριθεὶς δὲ ὁ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτοῖς· πλανᾶσθε μὴ εἰδότες τὰς γραφὰς μηδὲ τὴν δύναμιν τοῦ Θεοῦ.
30 Domin a tashin matattu basu aure, ba kuma a bada su aure. Maimaikon haka, suna kama da mala'ikun sama.
ἐν γὰρ τῇ ἀναστάσει οὔτε γαμοῦσιν οὔτε ἐκγαμίζονται, ἀλλ᾽ ὡς ἄγγελοι Θεοῦ ἐν οὐρανῷ εἰσι.
31 Amma game da tashin matattu, ba ku karanta abinda Allah ya fada maku ba, cewa,
περὶ δὲ τῆς ἀναστάσεως τῶν νεκρῶν οὐκ ἀνέγνωτε τὸ ῥηθὲν ὑμῖν ὑπὸ τοῦ Θεοῦ λέγοντος,
32 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.”
ἐγώ εἰμι ὁ Θεὸς Ἀβραὰμ καὶ ὁ Θεὸς Ἰσαὰκ καὶ ὁ Θεὸς Ἰακώβ; οὐκ ἔστιν ὁ Θεὸς Θεὸς νεκρῶν, ἀλλὰ ζώντων.
33 Da taron suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
καὶ ἀκούσαντες οἱ ὄχλοι ἐξεπλήσσοντο ἐπὶ τῇ διδαχῇ αὐτοῦ.
34 Amma da Farisawan suka ji cewa Yesu ya kure Sadukiyawa, sai suka tattara kansu.
Οἱ δὲ Φαρισαῖοι ἀκούσαντες ὅτι ἐφίμωσε τοὺς Σαδδουκαίους, συνήχθησαν ἐπὶ τὸ αὐτό,
35 Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi-
καὶ ἐπηρώτησεν εἷς ἐξ αὐτῶν, νομικός, πειράζων αὐτὸν καὶ λέγων·
36 “Mallam, wace doka ce mafi girma a cikin shari'a?”
διδάσκαλε, ποία ἐντολὴ μεγάλη ἐν τῷ νόμῳ;
37 Yesu yace masa, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.'
ὁ δὲ Ἰησοῦς ἔφη αὐτῷ· ἀγαπήσεις Κύριον τὸν Θεόν σου ἐν ὅλῃ τῇ καρδίᾳ σου καὶ ἐν ὅλῃ τῇ ψυχῇ σου καὶ ἐν ὅλῃ τῇ διανοίᾳ σου.
38 Wannan itace babbar doka ta farko.
αὕτη ἐστὶ πρώτη καὶ μεγάλη ἐντολή.
39 Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.'
δευτέρα δὲ ὁμοία αὐτῇ· ἀγαπήσεις τὸν πλησίον σου ὡς σεαυτόν.
40 Akan wadannan dokoki ne dukkan shari'a da annabawa suka rataya.”
ἐν ταύταις ταῖς δυσὶν ἐντολαῖς ὅλος ὁ νόμος καὶ οἱ προφῆται κρέμανται.
41 Yayin da Farisawa suke tattare wuri daya, Yesu yayi masu tambaya.
Συνηγμένων δὲ τῶν Φαρισαίων ἐπηρώτησεν αὐτοὺς ὁ Ἰησοῦς
42 Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.”
λέγων· τί ὑμῖν δοκεῖ περὶ τοῦ Χριστοῦ; τίνος υἱός ἐστι; λέγουσιν αὐτῷ· τοῦ Δαυΐδ.
43 Yesu yace masu, “To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa,
λέγει αὐτοῖς· πῶς οὖν Δαυῒδ ἐν Πνεύματι Κύριον αὐτὸν καλεῖ λέγων,
44 “Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka.”
εἶπεν ὁ Κύριος τῷ Κυρίῳ μου, κάθου ἐκ δεξιῶν μου ἕως ἂν θῶ τοὺς ἐχθρούς σου ὑποπόδιον τῶν ποδῶν σου;
45 Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?”
εἰ οὖν Δαυῒδ καλεῖ αὐτὸν Κύριον, πῶς υἱὸς αὐτοῦ ἐστι;
46 Ba wanda ya iya bashi amsa, ba kuma wanda ya kara yi masa tambayoyi tun daga wannan rana.
καὶ οὐδεὶς ἐδύνατο αὐτῷ ἀποκριθῆναι λόγον, οὐδὲ ἐτόλμησέ τις ἀπ᾽ ἐκείνης τῆς ἡμέρας ἐπερωτῆσαι αὐτὸν οὐκέτι.

< Mattiyu 22 >