< Mattiyu 19 >
1 Sai ya zama sa'adda Yesu ya gama wadannan maganganu, sai ya bar Galili ya zo kan iyakokin Yahudiya, ketaren kogin Urdun.
It happened when Jesus had finished these words, he departed from Galilee, and came into the borders of Judea beyond the Jordan.
2 Taro mai yawa suka bi shi, ya kuma warkar da su a wurin.
Large crowds followed him, and he healed them there.
3 Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce masa, ''Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?''
And Pharisees came to him, testing him, and saying to him, "Is it lawful for a man to divorce a wife for any reason?"
4 Yesu ya amsa ya ce, ''Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace?
He answered, and said, "Have you not read that he who created them from the beginning made them male and female,
5 Shi wanda ya yi su kuma ya ce, “Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?”
and said, 'For this reason a man will leave his father and mother, and be joined to his wife; and the two will become one flesh?'
6 Su ba biyu ba ne kuma, amma jiki daya. Don haka, duk abin da Allah ya hada, kada wani ya raba.''
So that they are no more two, but one flesh. What therefore God has joined together, let no one separate."
7 Sai suka ce masa, ''To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?''
They asked him, "Why then did Moses command us to give her a certificate of divorce, and divorce her?"
8 Sai ya ce masu, ''Saboda taurin zuciyarku, shi yasa Musa ya yarda maku ku saki matanku, amma da farko ba haka yake ba.
He said to them, "Moses, because of the hardness of your hearts, allowed you to divorce your wives, but from the beginning it has not been so.
9 Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina.''
I tell you that whoever divorces his wife, except for sexual immorality, and marries another, commits adultery. And he who marries her when she is divorced commits adultery."
10 Almajiran suka ce wa Yesu, ''Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba.''
The disciples said to him, "If this is the case of a husband with a wife, it is not expedient to marry."
11 Amma Yesu yace masu, ''Ba kowa ne zai karbi wannan koyarwa ba, amma sai wadanda an yardar masu su karbe ta.
But he said to them, "Not everyone can receive this saying, but those to whom it is given.
12 Akwai wadanda aka haife su babanni. Akwai wadanda mutane ne suka maida su babanni. Sa'annan akwai wadanda sun mayar da kansu babanni saboda mulkin sama. Duk wanda zai iya karbar wannan koyarwa, ya karba.''
For there are eunuchs who were born that way from their mother's womb, and there are eunuchs who were made eunuchs by men; and there are eunuchs who made themselves eunuchs for the kingdom of heaven's sake. He who is able to receive it, let him receive it."
13 Sai aka kawo masa yara kanana don ya dibiya hannuwansa akansu, yayi masu addu'a, amma almajiran suka kwabe su.
Then little children were brought to him, that he should lay his hands on them and pray; and the disciples rebuked them.
14 Amma Yesu ya ce masu, ''Ku bar yara kanana, kada ku hana su zuwa wuri na, domin mulkin sama na irinsu ne.''
But Jesus said, "Allow the little children, and do not forbid them to come to me; for the kingdom of heaven belongs to ones like these."
15 Ya sa hannuwa akan su, sa'annan ya bar wurin.
He placed his hands on them, and departed from there.
16 Sai wani mutum ya zo wurin Yesu, ya ce, ''Malam, wanne ayyuka nagari ne zan yi domin in sami rai madawwami?'' (aiōnios )
And look, someone came to him and said, "Teacher, what good thing must I do, that I may have everlasting life?" (aiōnios )
17 Yesu ya ce masa, ''Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.''
He said to him, "Why do you ask me about what is good? No one is good but one. But if you want to enter into life, keep the commandments."
18 Mutumin ya ce masa, ''Wadanne dokokin?'' Yesu ya ce masa, ''Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur,
He said to him, "Which ones?" And Jesus said, "'Do not murder.' 'Do not commit adultery.' 'Do not steal.' 'Do not offer false testimony.'
19 ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.''
'Honor your father and mother.' And, 'Love your neighbor as yourself.'"
20 Saurayin nan ya ce masa, ''Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?''
The young man said to him, "All these things I have kept. What do I still lack?"
21 Yesu ya ce masa, ''Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka biyo ni.''
Jesus said to him, "If you want to be perfect, go, sell what you have and give to the poor, and you will have treasure in heaven; and come, follow me."
22 Amma da saurayin nan ya ji abin da Yesu ya fada, ya koma da bakin ciki, domin shi mai arziki ne kwarai.
But when the young man heard the saying, he went away sad, for he was one who had great possessions.
23 Yesu ya ce wa almajiransa, ''Hakika ina gaya maku, zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama.
Jesus said to his disciples, "Truly I say to you, it is difficult for a rich person to enter the kingdom of heaven.
24 Ina sake gaya maku, zai fi wa rakumi sauki ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.''
Again I tell you, it is easier for a camel to go through a needle's eye, than for a rich person to enter into the Kingdom of God."
25 Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, ''Wanene zai sami ceto?''
When the disciples heard it, they were exceedingly astonished, saying, "Who then can be saved?"
26 Yesu ya dube su, ya ce, ''A wurin mutane wannan ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah, kome mai yiwuwa ne.''
Looking at them, Jesus said, "With humans this is impossible, but with God all things are possible."
27 Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, ''Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?''
Then Peter answered, "Look, we have left everything, and followed you. What then will we have?"
28 Yesu ya ce masu, ''Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
Jesus said to them, "Truly I tell you that you who have followed me, in the regeneration when the Son of Man will sit on the throne of his glory, you also will sit on twelve thrones, judging the twelve tribes of Israel.
29 Duk wanda ya bar gidaje, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, mahaifi, mahaifiya, 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkin su dari, ya kuma gaji rai madawwami. (aiōnios )
Everyone who has left houses, or brothers, or sisters, or father, or mother, or wife, or children, or lands, for my name's sake, will receive one hundred times, and will inherit everlasting life. (aiōnios )
30 Amma dayawa dake farko yanzu, za su zama na karshe, dayawa dake karshe kuma, su zama na farko.
But many will be last who are first; and first who are last.