< Mattiyu 16 >

1 Sai Farisawa da Sadukiyawa suka zo su gwada shi suka roke shi ya nuna masu alama daga sama.
The Pharisees and Sadducees came, and testing him, asked him to show them a sign from heaven.
2 Amma ya amsa ya ce masu, “Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,'
But he answered and said to them, "When it is evening, you say, 'It will be fair weather, for the sky is red.'
3 Kuma da safe ku ce, 'Zai zama yanayi mara kyau a yau, domin sama ta yi ja ta kuma gama gari, kun san yadda za ku bayyana kammanin sararin sama, amma ba ku iya bayyana alamun lokaci ba.
In the morning, 'It will be foul weather today, for the sky is red and threatening.' You know how to discern the appearance of the sky, but you cannot discern the signs of the times.
4 Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa.” Daga nan sai Yesu ya tafi.
An evil and adulterous generation seeks after a sign, and there will be no sign given to it, except the sign of Jonah." He left them, and departed.
5 Almajiran suka zo daga wancan gefe, amma sun manta su dauki gurasa,
The disciples came to the other side and had forgotten to take bread.
6 Yesu ya ce masu, “Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.”
Jesus said to them, "Watch out and guard yourselves against the yeast of the Pharisees and Sadducees."
7 Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, “Ko saboda bamu kawo gurasa bane.”
They reasoned among themselves, saying, "We brought no bread."
8 Yesu yana sane da wannan sai ya ce, “Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane?
But Jesus, becoming aware of this, said, "You of little faith, why are you discussing among yourselves about having no bread?
9 Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba?
Do you still not understand? Do you not remember the five loaves for the five thousand, and how many baskets you took up?
10 Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba?
Nor the seven loaves for the four thousand, and how many baskets you took up?
11 Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.”
Why is it that you do not understand that I did not speak to you concerning bread? But beware of the yeast of the Pharisees and Sadducees."
12 Sa'annan suka fahimta cewa ba yana gaya masu su yi hankali da yistin da ke cikin gurasa ba ne, amma sai dai su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa.
Then they understood that he did not tell them to beware of the yeast of bread, but of the teaching of the Pharisees and Sadducees.
13 A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake?
Now when Jesus came into the parts of Caesarea Philippi, he asked his disciples, saying, "Who do people say that the Son of Man is?"
14 Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.”
They said, "Some say John the Baptist, some, Elijah, and others, Jeremiah, or one of the prophets."
15 Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?”
He said to them, "But who do you say that I am?"
16 Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.”
Simon Peter answered, "You are the Christ, the Son of the living God."
17 Yesu ya amsa ya ce masa, “Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama.
And Jesus answered him, "Blessed are you, Simon Bar Jonah, for flesh and blood has not revealed this to you, but my Father who is in heaven.
18 Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba. (Hadēs g86)
I also tell you that you are Peter, and on this Rock I will build my church, and the gates of hell will not prevail against it. (Hadēs g86)
19 Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama,”
I will give to you the keys of the kingdom of heaven, and whatever you bind on earth will be bound in heaven, and whatever you loose on earth will be loosed in heaven."
20 Sai Yesu ya umarci almajiransa kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu.
Then he commanded the disciples that they should tell no one that he is the Christ.
21 Daga lokacin nan Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa a hannun dattawa, da manyan firistoci da malaman attaura, a kashe shi, a tashe shi zuwa rai a rana ta uku.
From that time, Jesus began to show his disciples that he must go to Jerusalem and suffer many things from the elders, chief priests, and scribes, and be killed, and the third day be raised up.
22 Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.”
Peter took him aside, and began to rebuke him, saying, "Far be it from you, Lord. This will never be done to you."
23 Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.”
But he turned, and said to Peter, "Get behind me, Satan. You are a stumbling block to me, for you are not setting your mind on the things of God, but on the things of humans."
24 Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni.
Then Jesus said to his disciples, "If anyone desires to come after me, let him deny himself, and take up his cross, and follow me.
25 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Duk wanda ya rasa ransa domina zai same shi.
For whoever desires to save his life will lose it, and whoever will lose his life for my sake will find it.
26 Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa?
For what will it profit a person, if he gains the whole world, and forfeits his life? Or what will a person give in exchange for his life?
27 Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa.
For the Son of Man will come in the glory of his Father with his angels, and then he will render to everyone according to his deeds.
28 Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.”
Truly I tell you, there are some standing here who will in no way taste of death, until they see the Son of Man coming in his Kingdom."

< Mattiyu 16 >