< Mattiyu 14 >
1 A lokacin nan ne, Hiridus mai mulki ya ji labarin Yesu.
In that time, Herod the Tetrarch heard the news about Jesus.
2 Ya ce wa barorinsa, “Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa”.
And he said to his servants: “This is John the Baptist. He has risen from the dead, and that is why miracles are at work in him.”
3 Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan'uwansa Filibus.
For Herod had apprehended John, and bound him, and put him in prison, because of Herodias, the wife of his brother.
4 Ya ce masa, “Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.”
For John was telling him, “It is not lawful for you to have her.”
5 Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama'a, domin sun dauke shi a matsayin annabi.
And though he wanted to kill him, he feared the people, because they held him to be a prophet.
6 Amma da ranar bikin haihuwar Hirudus ta kewayo, diyar Hirudiya tayi rawa a lokacin har ta burge Hirudus.
Then, on Herod’s birthday, the daughter of Herodias danced in their midst, and it pleased Herod.
7 Sai ya yi mata alkawari har da rantsuwa cewa ta roki komenene ta ke so, zai ba ta.
And so he promised with an oath to give her whatever she would ask of him.
8 Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, “Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire.
But, having been advised by her mother, she said, “Give me here, on a platter, the head of John the Baptist.”
9 Sarki ya husata da rokonta, amma domin rantsuwar da ya yi kuma domin mutanen da ke a wurin bukin tare da shi, sai ya umurta a yi haka.
And the king was greatly saddened. But because of his oath, and because of those who sat at table with him, he ordered it to be given.
10 Ya aika aka yanke kan Yahaya acikin kurkuku.
And he sent and beheaded John in prison.
11 Sai aka kawo kansa bisa tire, aka mika wa yarinyar, ta kuwa kai wa mahaifiyarta.
And his head was brought on a platter, and it was given to the girl, and she brought it to her mother.
12 Sai almajiransa suka zo, su ka dauki gawar su ka je su ka yi jana'iza. Bayan haka, su ka je su ka fada wa Yesu.
And his disciples approached and took the body, and they buried it. And arriving, they reported it to Jesus.
13 Sa'adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen.
When Jesus had heard it, he withdrew from there by boat, to a deserted place by himself. And when the crowds had heard of it, they followed him on foot from the cities.
14 Sai Yesu ya zo gabansu, ya kuma ga babban taron. Ya tausaya masu ya kuwa warkar da marasa lafiya dake cikinsu.
And going out, he saw a great multitude, and he took pity on them, and he cured their sick.
15 Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, “Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.”
And when evening had arrived, his disciples approached him, saying: “This is a deserted place, and the hour has now passed. Dismiss the crowds, so that, by going into the towns, they may buy food for themselves.”
16 Amma Yesu ya ce masu, “Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.”
But Jesus said to them: “They have no need to go. Give them something to eat yourselves.”
17 Suka ce masa, “Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.”
They answered him, “We have nothing here, except five loaves and two fish.”
18 Yesu ya ce, “Ku kawo mani su.”
He said to them, “Bring them here to me.”
19 Sai Yesu ya umarci taron su zauna akan ciyawa. Ya dauki gurasa biyar da kifi biyun. Ya dubi sama, ya sa albarka ya gutsuttsura ya kuma ba almajiran. Almajiran suka ba taron.
And when he had ordered the multitude to sit down upon the grass, he took the five loaves and the two fish, and gazing up to heaven, he blessed and broke and gave the bread to the disciples, and then the disciples to the multitudes.
20 Dukansu suka ci suka koshi. Sai suka dauki gutsattsarin gurasa da kifin, kwanduna goma sha biyu cike.
And they all ate and were satisfied. And they took up the remnants: twelve baskets full of fragments.
21 Wadanda su ka ci kuwa kimanin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara.
Now the number of those who ate was five thousand men, besides women and children.
22 Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron.
And Jesus promptly compelled his disciples to climb into the boat, and to precede him in crossing the sea, while he dismissed the crowds.
23 Bayan ya sallami taron sun tafi, sai ya haura kan dutse domin yayi addu'a. Da dare yayi, yana can shi kadai.
And having dismissed the multitude, he ascended alone onto a mountain to pray. And when evening arrived, he was alone there.
24 Amma yanzu fa kwale-kwalen na tsakiyar tekun, kuma da wuyar sarrafawa saboda rakuman ruwa da iska na gaba da su.
But in the midst of the sea, the boat was being tossed about by the waves. For the wind was against them.
25 Da asuba (wajen karfe uku na dare) Yesu ya nufo su yana tafiya akan teku.
Then, in the fourth watch of the night, he came to them, walking upon the sea.
26 Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, “Fatalwa ce,” suka yi kururuwa cikin tsoro.
And seeing him walking upon the sea, they were disturbed, saying: “It must be an apparition.” And they cried out, because of fear.
27 Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.”
And immediately, Jesus spoke to them, saying: “Have faith. It is I. Do not be afraid.”
28 Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.”
Then Peter responded by saying, “Lord, if it is you, order me to come to you over the waters.”
29 Yesu yace, “Zo” Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu.
And he said, “Come.” And Peter, descending from the boat, walked over the water, so as to go to Jesus.
30 Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
Yet truly, seeing that the wind was strong, he was afraid. And as he began to sink, he cried out, saying: “Lord, save me.”
31 Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?”
And immediately Jesus extended his hand and took hold of him. And he said to him, “O little in faith, why did you doubt?”
32 Bayan da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa.
And when they had ascended into the boat, the wind ceased.
33 Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.”
Then those who were in the boat drew near and adored him, saying: “Truly, you are the Son of God.”
34 Da suka haye, sun iso kasar Janisarata.
And having crossed the sea, they arrived in the land of Genesaret.
35 Da mutanen wurin suka gane Yesu, sai suka aika da sako zuwa dukan yankin, kuma suka kawo masa dukan marasa lafiya.
And when the men of that place had recognized him, they sent into all that region, and they brought to him all who had maladies.
36 Suka roke shi don su taba gezar rigarsa, kuma dukan wadanda suka taba shi sun warke.
And they petitioned him, so that they might touch even the hem of his garment. And as many as touched it were made whole.