< Mattiyu 13 >

1 A waccan rana Yesu ya fito daga gida ya zauna a gefen teku.
in illo die exiens Iesus de domo sedebat secus mare
2 Taro mai yawan gaske kuwa suka kewaye shi, sai ya shiga cikin kwalekwale ya zauna. Dukan taron kuwa na tsaye a bakin tekun.
et congregatae sunt ad eum turbae multae ita ut in naviculam ascendens sederet et omnis turba stabat in litore
3 Sai Yesu ya fada masu abubuwa da yawa cikin misalai. Ya ce, “Wani mai shuka, ya tafi yayi shuka.
et locutus est eis multa in parabolis dicens ecce exiit qui seminat seminare
4 Da yayi shukar, wadansu irin suka fadi a kan hanya, sai tsunsaye suka zo suka cinye su.
et dum seminat quaedam ceciderunt secus viam et venerunt volucres et comederunt ea
5 Wadansu irin kuwa suka fadi a kan duwatsu, wurin da babu kasa. Nan da nan sai suka tsira, domin kasar babu zurfi.
alia autem ceciderunt in petrosa ubi non habebat terram multam et continuo exorta sunt quia non habebant altitudinem terrae
6 Amma da rana ta taso, sai suka yankwane domin ba su yi saiwa ba, suka kuwa bushe suka zube.
sole autem orto aestuaverunt et quia non habebant radicem aruerunt
7 Wasu irin kuwa suka fada a cikin kayayuwa. Kayayuwan kuwa suka shake su.
alia autem ceciderunt in spinas et creverunt spinae et suffocaverunt ea
8 Wasu irin kuwa suka fada a wuri mai kyau suka ba da tsaba, wani ya ba da dari, wasu sitin, wasu kuma talatin.
alia vero ceciderunt in terram bonam et dabant fructum aliud centesimum aliud sexagesimum aliud tricesimum
9 Duk mai kunnen ji, bari ya ji.
qui habet aures audiendi audiat
10 Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, “Don me ka ke yi wa taron magana da misali?”
et accedentes discipuli dixerunt ei quare in parabolis loqueris eis
11 Yesu ya amsa ya ce masu, “An baku 'yanci ku fahimci asiran mulkin sama, amma gare su ba a bayar ba.
qui respondens ait illis quia vobis datum est nosse mysteria regni caelorum illis autem non est datum
12 Domin wanda yake da shi, za a kara masa, zai kuma samu dayawan gaske. Amma duk wanda ba shi da shi, sai a dauke har ma abin da yake dashi.
qui enim habet dabitur ei et abundabit qui autem non habet et quod habet auferetur ab eo
13 Saboda haka na yi masu magana cikin misalai, amma ko da ya ke sun gani, duk da haka ba su gani ba. Kuma ko da yake sun ji, hakika ba su ji ba, balle ma su fahimta.
ideo in parabolis loquor eis quia videntes non vident et audientes non audiunt neque intellegunt
14 A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, “Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba.
et adimpletur eis prophetia Esaiae dicens auditu audietis et non intellegetis et videntes videbitis et non videbitis
15 Domin zuciyar mutanen nan ta duhunta, sun taurare ga saurare, kuma sun rufe idanunsu domin kada su gani da idanunsu, ko kuwa su ji da kunnuwansu, ko kuwa su fahimta da zukatansu, saboda su juyo kuma in warkar da su'.
incrassatum est enim cor populi huius et auribus graviter audierunt et oculos suos cluserunt nequando oculis videant et auribus audiant et corde intellegant et convertantur et sanem eos
16 Amma idanunku masu albarka ne, domin sun gani, haka ma kunnuwanku, domin sun ji.
vestri autem beati oculi quia vident et aures vestrae quia audiunt
17 Hakika ina gaya muku, annabawa da mutane dayawa masu aldalci sun yi marmarin ganin abin da kuka gani, amma ba su sami ganin su ba. Sun yi marmarin jin abin da kuka ji, ba su kuwa ji su ba.
amen quippe dico vobis quia multi prophetae et iusti cupierunt videre quae videtis et non viderunt et audire quae auditis et non audierunt
18 Ku saurari misalin nan na mai shuka.
vos ergo audite parabolam seminantis
19 Idan wani ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa. Wannan shine irin da aka shuka a kan hanya.
omnis qui audit verbum regni et non intellegit venit malus et rapit quod seminatum est in corde eius hic est qui secus viam seminatus est
20 Shi wanda aka shuka akan duwatsu, shine wanda ya ji maganar ya kuma karbe ta da murna nan da nan.
qui autem supra petrosa seminatus est hic est qui verbum audit et continuo cum gaudio accipit illud
21 Duk da haka, bai yi karfi cikin ta ba kuma nan ba da dadaiwa ba. Da wahala da tsanani suka taso saboda maganar, sai ya yi tuntube nan da nan.
non habet autem in se radicem sed est temporalis facta autem tribulatione et persecutione propter verbum continuo scandalizatur
22 Shi wanda aka shuka a cikin kayayuwa wannan shine wanda ya ji maganar, amma dawainiyar duniya da kuma yaudarar dukiya suka shake maganar, sai ya kasa ba da 'ya'ya. (aiōn g165)
qui autem est seminatus in spinis hic est qui verbum audit et sollicitudo saeculi istius et fallacia divitiarum suffocat verbum et sine fructu efficitur (aiōn g165)
23 Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin.”
qui vero in terra bona seminatus est hic est qui audit verbum et intellegit et fructum adfert et facit aliud quidem centum aliud autem sexaginta porro aliud triginta
24 Yesu ya sake ba su wani misali, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da wani mutum wanda ya shuka iri mai kyau a gona.
aliam parabolam proposuit illis dicens simile factum est regnum caelorum homini qui seminavit bonum semen in agro suo
25 Amma da mutane suka yi barci, magabcin sa ya zo ya shuka ciyayi a cikin alkamar, ya kuwa yi tafiyarsa.
cum autem dormirent homines venit inimicus eius et superseminavit zizania in medio tritici et abiit
26 Sa'adda suka yi toho suka kuma ba da tsaba, sai ciyayin suka bayyana.
cum autem crevisset herba et fructum fecisset tunc apparuerunt et zizania
27 Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi?
accedentes autem servi patris familias dixerunt ei domine nonne bonum semen seminasti in agro tuo unde ergo habet zizania
28 Ya ce masu, “Magabci ne ya yi wannan”. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?'
et ait illis inimicus homo hoc fecit servi autem dixerunt ei vis imus et colligimus ea
29 Mai gonar ya ce, 'A'a, kada a garin tuge ciyayin, ku tuge tare da alkamar.
et ait non ne forte colligentes zizania eradicetis simul cum eis et triticum
30 Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, “Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'”
sinite utraque crescere usque ad messem et in tempore messis dicam messoribus colligite primum zizania et alligate ea fasciculos ad conburendum triticum autem congregate in horreum meum
31 Sai Yesu ya sake yin magana da su cikin misalai, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da kwayar mustad, wanda wani mutum ya shuka a lambunsa.
aliam parabolam proposuit eis dicens simile est regnum caelorum grano sinapis quod accipiens homo seminavit in agro suo
32 Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.”
quod minimum quidem est omnibus seminibus cum autem creverit maius est omnibus holeribus et fit arbor ita ut volucres caeli veniant et habitent in ramis eius
33 Yesu ya sake fada masu wani misali. “Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi.”
aliam parabolam locutus est eis simile est regnum caelorum fermento quod acceptum mulier abscondit in farinae satis tribus donec fermentatum est totum
34 Duk wadannan abubuwa Yesu ya fada wa taron cikin misalai. Babu abinda ya fada masu da ba a cikin misali ba.
haec omnia locutus est Iesus in parabolis ad turbas et sine parabolis non loquebatur eis
35 Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.”
ut impleretur quod dictum erat per prophetam dicentem aperiam in parabolis os meum eructabo abscondita a constitutione mundi
36 Sai Yesu ya bar taron ya shiga cikin gida. Amajiransa suka zo wurin sa suka ce, “Ka fasarta mana misalan nan a kan ciyayin da ke gonar”
tunc dimissis turbis venit in domum et accesserunt ad eum discipuli eius dicentes dissere nobis parabolam zizaniorum agri
37 Yesu ya amsa kuma ya ce, “Shi wanda ya shuka iri mai kyau Dan Mutum ne.
qui respondens ait qui seminat bonum semen est Filius hominis
38 Gonar kuwa duniya ce; iri mai kyau kuma sune 'ya'yan mulkin. Ciyayin kuma sune 'ya'yan mugun,
ager autem est mundus bonum vero semen hii sunt filii regni zizania autem filii sunt nequam
39 magabcin da ya shuka su kuma shaidan ne. Girbin shine karshen duniya, kuma masu girbin sune mala'iku. (aiōn g165)
inimicus autem qui seminavit ea est diabolus messis vero consummatio saeculi est messores autem angeli sunt (aiōn g165)
40 Saboda haka, kamar yadda aka tara ciyayin aka kona su da wuta, haka ma zai faru a karshen duniya. (aiōn g165)
sicut ergo colliguntur zizania et igni conburuntur sic erit in consummatione saeculi (aiōn g165)
41 Dan Mutum zai aiki mala'ikunsa, kuma su tara dukan abubuwan da ke sa zunubi daga cikin mulkinsa, da kuma wadanda su ka yi aikin mugunta.
mittet Filius hominis angelos suos et colligent de regno eius omnia scandala et eos qui faciunt iniquitatem
42 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora.
et mittent eos in caminum ignis ibi erit fletus et stridor dentium
43 Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji.
tunc iusti fulgebunt sicut sol in regno Patris eorum qui habet aures audiat
44 Mulkin sama kamar dukiya ce da ke boye a gona. Mutum ya samu sai ya boye ta, ya tafi cikin murna, ya sayar da mallakarsa kuma ya sayi filin.
simile est regnum caelorum thesauro abscondito in agro quem qui invenit homo abscondit et prae gaudio illius vadit et vendit universa quae habet et emit agrum illum
45 Haka ma za a kwatanta mulkin sama da wani attajiri mai neman Lu'ulu'ai masu daraja.
iterum simile est regnum caelorum homini negotiatori quaerenti bonas margaritas
46 Da ya sami lu'ulu'u daya mai darajar gaske, ya je ya sayar da dukan mallakarsa ya kuma saye shi.
inventa autem una pretiosa margarita abiit et vendidit omnia quae habuit et emit eam
47 Haka kuma, za a kwatanta mulkin sama da taru da aka jefa cikin teku, ya kuwa tara hallitu iri-iri.
iterum simile est regnum caelorum sagenae missae in mare et ex omni genere congreganti
48 Da ya cika, sai masuntan suka jawo shi bakin tekun. Sai suka zauna suka tara kyawawan abubuwan a taska, amma munanan abubuwan, suka watsar da su.
quam cum impleta esset educentes et secus litus sedentes elegerunt bonos in vasa malos autem foras miserunt
49 Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci. (aiōn g165)
sic erit in consummatione saeculi exibunt angeli et separabunt malos de medio iustorum (aiōn g165)
50 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora.
et mittent eos in caminum ignis ibi erit fletus et stridor dentium
51 Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I”.
intellexistis haec omnia dicunt ei etiam
52 Sai Yesu ya ce masu, “Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa.”
ait illis ideo omnis scriba doctus in regno caelorum similis est homini patri familias qui profert de thesauro suo nova et vetera
53 Daga nan, sa'adda Yesu ya kammala ba da wadanan misalai, sai ya tafi ya bar wurin.
et factum est cum consummasset Iesus parabolas istas transiit inde
54 Sai Yesu ya shiga yankinsa ya koyar da mutane a masujadarsu. Saboda haka suka yi mamaki suna cewa, “Daga ina wannan mutumin ya sami hikimarsa da al'ajibai?
et veniens in patriam suam docebat eos in synagogis eorum ita ut mirarentur et dicerent unde huic sapientia haec et virtutes
55 Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba?
nonne hic est fabri filius nonne mater eius dicitur Maria et fratres eius Iacobus et Ioseph et Simon et Iudas
56 Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa?
et sorores eius nonne omnes apud nos sunt unde ergo huic omnia ista
57 Suka bata rai saboda shi. Amma Yesu ya ce masu, “Ai annabi bai rasa daraja sai dai ko a garinsa da kuma cikin iyalinsa.
et scandalizabantur in eo Iesus autem dixit eis non est propheta sine honore nisi in patria sua et in domo sua
58 Kuma bai yi al'ajibai dayawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.
et non fecit ibi virtutes multas propter incredulitatem illorum

< Mattiyu 13 >