< Mattiyu 11 >

1 Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa gargadi, sai ya bar wannan wuri, ya tafi biranensu domin yayi koyorwa, da wa'azi.
Et factum est, cum consummasset Iesus, praecipiens duodecim discipulis suis, transiit inde ut doceret, et praedicaret in civitatibus eorum.
2 Da Yahaya mai baftisma ya ji daga kurkuku irin ayyukan da Yesu ke yi, sai ya aika sako ta wurin almajiransa.
Ioannes autem cum audisset in vinculis opera Christi, mittens duos de discipulis suis,
3 Ya ce masa. “Kai ne mai zuwa”? ko mu sa ido ga wani.
ait illi: Tu es, qui venturus es, an alium expectamus?
4 Yesu ya amsa ya ce masu, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji.
Et respondens Iesus ait illis: Euntes renunciate Ioanni quae audistis, et vidistis.
5 Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara.
Caeci vident, claudi ambulant, leprosi mundantur, surdi audiunt, mortui resurgunt, pauperes evangelizantur:
6 Kuma mai albarka ne wanda baya tuntube sabili da ni.
et beatus est, qui non fuerit scandalizatus in me.
7 Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa?
Illis autem abeuntibus, coepit Iesus dicere ad turbas de Ioanne: Quid existis in desertum videre? arundinem vento agitatam?
8 Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna.
Sed quid existis videre? hominem mollibus vestitum? Ecce qui mollibus vestiuntur, in domibus regum sunt.
9 Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi.
Sed quid existis videre? prophetam? Etiam dico vobis, et plus quam prophetam.
10 Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'.
Hic est enim, de quo scriptum est: Ecce ego mitto angelum meum ante faciem tuam, qui praeparabit viam tuam ante te.
11 Ina gaya maku gaskiya, cikin wadanda mata suka haifa, babu mai girma kamar Yahaya mai baftisma. Amma mafi kankanta a mulkin sama ya fi shi girma.
Amen dico vobis, non surrexit inter natos mulierum maior Ioanne Baptista: qui autem minor est in regno caelorum, maior est illo.
12 Tun daga kwanakin Yahaya mai baftisma zuwa yanzu, mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu husuma kuma su kan kwace shi da karfi.
A diebus autem Ioannis Baptistae usque nunc, regnum caelorum vim patitur, et violenti rapiunt illud.
13 Gama dukan annabawa da shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya.
Omnes enim prophetae, et lex usque ad Ioannem prophetaverunt:
14 kuma in zaku karba, wannan shine Iliya wanda za ya zo.
et si vultis recipere, ipse est Elias, qui venturus est.
15 Wanda ke da kunnuwan ji, ya ji.
Qui habet aures audiendi, audiat.
16 Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna
Cui autem similem aestimabo generationem istam? Similis est pueris sedentibus in foro: qui clamantes coaequalibus
17 suna cewa mun busa maku sarewa baku yi rawa ba, mun yi makoki, baku yi kuka ba.
dicunt: Cecinimus vobis, et non saltastis: lamentavimus, et non planxistis.
18 Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, “Yana da aljannu”.
Venit enim Ioannes neque manducans, neque bibens, et dicunt: Daemonium habet.
19 Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita.
Venit filius hominis manducans, et bibens, et dicunt: Ecce homo vorax, et potator vini, publicanorum, et peccatorum amicus. Et iustificata est sapientia a filiis suis.
20 Sannan Yesu ya fara tsautawa biranen nan inda ya yi yawancin ayukansa, domin ba su tuba ba.
Tunc coepit exprobrare civitatibus, in quibus factae sunt plurimae virtutes eius, quia non egissent poenitentiam.
21 “Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka.
Vae tibi Corozain, vae tibi Bethsaida: quia, si in Tyro, et Sidone factae essent virtutes quae factae sunt in vobis, olim in cilicio, et cinere poenitentiam egissent.
22 Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku.
Verumtamen dico vobis: Tyro, et Sidoni remissius erit in die iudicii, quam vobis.
23 Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. (Hadēs g86)
Et tu Capharnaum, numquid usque in caelum exaltaberis? usque in infernum descendes. quia, si in Sodomis factae fuissent virtutes, quae factae sunt in te, forte mansissent usque in hanc diem. (Hadēs g86)
24 Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku.”
Verumtamen dico vobis, quia terrae Sodomorum remissius erit in die iudicii, quam tibi.
25 A wannan lokaci Yesu ya ce, “Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara.
In illo tempore respondens Iesus dixit: Confiteor tibi, Pater, Domine caeli et terrae, quia abscondisti haec a sapientibus, et prudentibus, et revelasti ea parvulis.
26 I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka.
Ita Pater: quoniam sic fuit placitum ante te.
27 An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa.
Omnia mihi tradita sunt a Patre meo. Et nemo novit Filium, nisi Pater: neque Patrem quis novit, nisi Filius, et cui voluerit Filius revelare.
28 Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da fama da nauyin kaya, ni kuma zan ba ku hutawa.
Venite ad me omnes, qui laboratis, et onerati estis, et ego reficiam vos.
29 Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali'u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku.
Tollite iugum meum super vos, et discite a me, quia mitis sum, et humilis corde: et invenietis requiem animabus vestris.
30 Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.”
Iugum enim meum suave est, et onus meum leve.

< Mattiyu 11 >