< Markus 1 >

1 Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah.
这里讲述了上帝之子耶稣基督福音的初始。
2 kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya. Duba, ina aika manzona, a gabanka, wanda zai shirya maka hanya.
正如以赛亚先知所写:“我派遣使者提前来到,备好你要走的道路。
3 Akwai murya mai kira a jeji, tana cewa ka shirya hanyar Ubangiji. ka daidaita ta.
在荒野中有人在呼喊:‘预备主的道,修直他的路!’”
4 Yahaya ya zo, yana baptisma acikin jeji yana wa'azin tuba, domin gafarar zunubai.
施洗约翰出现在荒野中,宣讲悔改的洗礼,因此救赎罪行。
5 Dukan kasar Yahudiya da mutanen Urshalima suka zo wurin sa, a ka kuma yi masu baptisma a kogin urdun. suna furta zunubansu.
犹太和全耶路撒冷的人都来到他身边,承认自己的罪,在约旦河里接受他的洗礼。
6 Yahaya yana saye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma da damara ta fata a kugunsa, abincinsa fara ce da zuma.
约翰身穿驼毛衣服,腰束皮带,以蝗虫和野蜜为食。
7 Yana wa'azi, ya ce “akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba.
他这样宣讲:“在我之后将有一人到来,能力远比我强大,我甚至连弯腰给他提鞋的资格都没有。
8 Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki''.
我用水给你们施洗,他却会用圣灵给你们施洗。”
9 Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun.
这时耶稣从加利利的拿撒勒前来,在约旦河里接受约翰的洗礼。
10 Sa'adda Yesu ya fito daga ruwan, sai sama ta bude, sai Ruhu ya sauko a bisansa da kamanin kurciya.
他从水中出来的那一刻,天裂开了,圣灵如鸽子般落在他身上。
11 Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, “Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai''.
天空传来一个声音:“你是我的爱子,你让我喜悦。”
12 Sai Ruhu ya iza shi zuwa jeji.
圣灵随即将耶稣派到荒野。
13 Yana a jeji kwana arba'in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima.
他在那里将待上四十天,受到撒旦的诱惑,身边是各种野兽,还有天使来看护他。
14 Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa'azin bisharar Allah.
之后,耶稣在约翰被捕后来到加利利,宣讲上帝的福音。
15 Yana cewa, “Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara”.
他说:“预言的时间已到,上帝之国已来临,要悔改并相信福音。”
16 Sa'adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan'uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne.
耶稣沿着加利利海边行走,看见西门和他弟弟安得烈在海上撒网,他们靠打鱼过活。
17 Yesu ya ce masu ku zo, ku biyo ni, ni kuwa sai in maisheku masuntan mutane”.
耶稣对他们说:“跟从我吧,我要让你们成为获得人的渔夫。”
18 Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi.
他们立刻丢下渔网,跟从了他。
19 Sa'adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan'uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa.
耶稣稍往前走了几步,看见西庇太的儿子雅各和弟弟约翰,正在船上整理渔网,
20 Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma'aikatansu, sai su ka bi shi.
耶稣召唤他们,他们立刻离开父亲西庇太和雇工,跳下船跟从耶稣而去。
21 Da su ka shigo cikin kafanahum, a ranar asabar, Yesu ya shiga majami'a ya koya masu.
他们去往迦百农,耶稣随即在安息日进入会堂向民众宣讲。
22 Su ka yi mamakin koyarwarsa, domin ya na koya masu da iko ba kamar marubuta ba.
民众对他的教导感到惊讶万分,因为他宣讲的方式非常权威,不像是其他的宗教老师。
23 A nan cikin majami'a akwai wani mutum mai kazamin ruhu, sai ya yi ihu da karfi.
忽然,会堂中一个被恶灵附体之人开始喊叫:
24 Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah”.
“拿撒勒人耶稣,你为什么要来打扰我们?你是来毁灭我们的吗?我知道你是谁,你是上帝的圣者。”
25 Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, “Ka yi shiru ka fita daga cikinsa”.
耶稣打断恶灵的话:“住口!从他身上出来!”
26 Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa'annan ya fita daga jikinsa.
恶灵嘶叫着,附体之人陷入惊厥,恶灵从他身体被驱赶出来。
27 Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!”
众人都很惊讶,对彼此说:“这是什么?这新教义的权威太大了!即使恶灵也服从于他的命令!”
28 Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili.
耶稣的名声立刻传遍加利利一带。
29 Bayan da suka bar majami'a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya.
他们走出会堂,与雅各和约翰一起去往西门和安得烈的家。
30 Surikar Saminu tana kwance ba lafiya tana fama da zazzabi. Sai suka gaya wa Yesu game da ita.
西门的岳母此刻正发烧躺在床上,众人把这件事告诉了耶稣。
31 Sai ya zo, ya kama hannunta, ya daga ta, sai zazzabin ya sake ta, ta fara yi masu hidima.
耶稣走到她面前,拉着她的手,扶她起来,高烧立刻退去,于是她开始为众人做饭。
32 Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu.
黄昏过后,有人不断把生病和被鬼附体之人带到耶稣面前。
33 Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa.
全城的人都聚集在门外。
34 ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi.
耶稣医好了很多人的疾病,驱走很多恶鬼。他命令恶鬼不要说话,因为鬼知道他是谁。
35 Ya tashi da sassafe, tun da sauran dare, ya tafi wurin da ba kowa, a can ya yi add'ua.
次日凌晨,天还没有亮,耶稣便起身来到荒郊野外进行祷告。
36 Saminu da wandanda suke tare da shi suka neme shi.
西门和其他人去寻找耶稣。
37 Suka sa me shi, sai su ka ce masa, “kowa yana nemanka”.
找到他后就对他说:“大家都在找你呢!”
38 Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan''.
耶稣对他们说:“我们必须到附近的其他城镇去,这样我就可以在那里传授福音,我就是为此而来。”
39 Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa'azi a majimi'un su yana kuma fitar da aljanu.
于是他走遍加利利各地,在会堂里传道,进行驱鬼。
40 Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, “in ka yarda kana iya warkar da ni.
有一个麻风病人前来寻求帮助。他跪在耶稣面前说:“主啊!如果你愿意,就能治愈我。”
41 Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa “Na yarda. Ka sarkaka”.
耶稣动了怜悯的心,便伸手摸他,说:“我愿意,你治愈了!”
42 Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa.
这人的麻风病立刻消失了,他痊愈了。
43 Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi.
在那人离开以前,耶稣认真地警告他说:
44 Ya ce masa “ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida.
“不要向任何人讲述这件事。去祭司那里,让他看看你的样子,然后按照摩西的要求,为这洁净献祭,向大家作证。”
45 Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina.
但那人离开后仍然到处宣讲,把这事传开了,这也让耶稣无法再公开走进城市,只好留在外面的荒野。可仍有很多人从各处赶到他这里。

< Markus 1 >