< Markus 9 >
1 Sai ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
耶稣又对他们说:“告诉你们实话,站在这里的有些人,在死前必定会看见上帝的天国带着力量降临人间。”
2 Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kadai. Sai kamaninsa ya sake a gabansu.
六天后,耶稣带着彼得、雅各和约翰爬上高山,然后在他们面前改变了形象。
3 Sai tufafinsa ya zama fari fat, yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya.
他的衣服闪耀着洁白的光芒,人间任何漂白的布料都比不上这样的白色。
4 Sai Iliya da Musa suka bayyana gare su, suna magana da Yesu.
然后以利亚和摩西现身在他们面前,跟耶稣谈话。
5 Sai Bitrus ya amsa ya ce, malam, bari mu da muke anan mu kafa bukka uku, daya ta ka, daya ta Musa, da ta Iliya,
彼得对耶稣说:“拉比,我们在这里太好了!我们可以搭三个庇护所,一个为你,一个为摩西,一个为以利亚。”
6 Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai.)
(彼得其实不知道该说什么,因为他们都非常害怕!)
7 Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, “ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi.
有一片云朵飘到他们头顶,云中传来一个声音:“这是吾子,我之所爱,你们要听他。”
8 Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai.
门徒们正在张望之际,忽然就看不见别的人了,只有耶稣和他们在一起。
9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwabe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan da Dan Mutum ya tashi daga mattatu.
他们下山的时候,耶稣吩咐他们,人子死而复生之前,不要将所见告诉其他人。
10 Sai suka bar zancen a tsakaninsu, amma suka tamabayi junansu “mene ne tashin matattu” ke nufi.
门徒把这句话记在心里,但她们彼此争论死而复生是什么意思。
11 Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?”
他们就问耶稣:“宗教老师为什么说以利亚必须先来呢?”
12 Ya ce masu, laile ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan. Don me a ka rubuta cewa Dan Mutum, zai sha wuya iri iri a kuma ki shi?
耶稣说:“的确,以利亚要先来做好准备,但为什么经书中又说人子要受许多苦,被人侮辱呢?
13 Amma ina gaya muku Iliya ya riga, ya zo, amma sun yi masa abin da suke so su yi kamar yadda littatafai suka yi magana a kansa.”
但我告诉你们,以利亚已降临,他们任意地虐待他,就像经书中记载的那样。”
14 Sa'adda suka dawo wurin sauran almajiran, suka ga taron jama'a masu yawa suna ta muhawara tare da manyan malaman attaura.
他们回到其他门徒那里,看见一大群人围着他们,还有宗教老师在和他们辩论。
15 Da ganin sa, sai dukan taron yayi mamaki kwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi.
众人看见了耶稣都很惊奇,就跑上前去向他问候。
16 Ya tambayi almajiransa, “Wacce muhawara ce kuke yi da su?”
他问他们:“你们和他们辩论什么?”
17 Daya daga cikin taron ya amsa masa”malam, ga shi na kawo maka dana don yana da beben aljani.
民众当中有一人回答他:“老师,我把我的儿子带到你这里来,他被恶灵附体,无法说话。
18 Duk lokacin da ya tasar masa yakan buga shi har kasa, na kuma yi wa almajiranka magana su fitar sun kasa.
无论在哪里,恶灵都会抓住他,把他摔倒,让他口吐白沫、咬牙切齿、浑身僵硬。我请你的门徒把恶灵赶出去,他们却办不到。”
19 Ya amsa masu ya ce ya ku mutanen zamaninnan marasa bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku ina jimrewa? ku dai kawo mini shi.
耶稣回答他们:“唉!这些没有信心的人啊!我在这里必须待到什么时候?我还要忍受你们多久?把他带到我这里来吧。”
20 Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan ya buge yaron jikinsa na rawa. Sai yaron ya fadi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa.
他们把孩子带到他跟前。那恶灵一见耶稣,就立刻让孩子倒在地上抽搐,口吐白沫打滚。
21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami.
耶稣问他父亲:“他这样多久了?” 他说:“从小就是这样。
22 Ya kuwa sha jefa shi a ruwa da wuta, don ya halakar da shi. Idan zaka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimakemu.
恶灵经常把他扔在火中想要烧死他,把他扔在水中想要淹死他。如果你能,求你可怜我们,帮助我们。”
23 Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai dukan abu mai yiwuwa ne, ga duk wanda ya gaskata.
耶稣说:“为什么你要说‘如果你能?’有信心者必有力量!”
24 Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata.
孩子的父亲立刻喊着说:“我真的信你!但我的信心不够,求你帮助我。”
25 Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, “kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa.
耶稣见民众围拢了来,开始斥责那恶灵说:“让人聋哑的恶灵,我命令你从他身上出来,不要再回去。”
26 Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, “Ai, yaron ya mutu.
那恶灵喊叫着,让这孩子陷入剧烈的抽搐,然后就从他身体里被驱赶出来。孩子仿佛已经死了,许多人都说:“他死了!”
27 Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye.
但耶稣拉着男孩的手,扶他起来,他就站起来了。
28 Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?”
然后耶稣走进屋子,门徒私下问他说:“为什么我们就无法驱赶那恶灵呢?”
29 Ya ce masu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.”
耶稣对他们说:“如果不祈祷,这种恶灵无法驱赶。”
30 Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke.
他们离开了,途经加利利。耶稣不想让任何人知道他们的行踪,
31 Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.
因为他正在教导门徒。他对他们说:“人子将遭到背叛,送到人类的官府,他们会杀害他,但他在死后三天就会复活。”
32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa.
门徒不明白这话,又不敢询问。
33 Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya?
他们来到迦百农的一个房间内住下。耶稣问他们:“你们在路上讨论什么呢?”
34 Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma.
门徒不说话,因为他们在路上争论谁最重要。
35 Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka.
耶稣坐下,唤来十二门徒,对他们说:“一个人如果想为首,就必在众人中成为最后,做众人的仆人。”
36 Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu.
耶稣拉过一个小孩子来,叫他站在门徒中间,然后把孩子抱起来拥抱着他,对门徒说:
37 Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni.”
“凡因我之名迎接这样的小孩子,就是迎接我,这样的人并非在迎接我,而是迎接那派我过来的人。”
38 Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu.
约翰对耶稣说:“老师,我们看见有人以你之名驱鬼,我们想要制止他,因为他不是我们中的一员。”
39 Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu.
耶稣说:“不要制止他,因为没有人能在以我之名行神迹的同时又诅咒我。
40 Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne.
不反对我们,就是支持我们。
41 Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba.
无论是谁,若以我之名给你一杯水,他这样做只因你属于基督,就不会失掉赏赐,相信我。
42 Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku.
但如果有人让这些信我的小孩子犯罪,最好就是在他的脖子上拴一块大磨石,让其淹没在海里。
43 Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu. (Geenna )
如果你的一只手让你犯罪,把它砍下来。残疾却能进永生,总好过双手下哥和拿,堕入不灭的哥和拿之火。 (Geenna )
44 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
45 Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu. (Geenna )
如果你的一只脚让你犯罪,把它砍下来。瘸腿却能获得永生,总好过两脚齐全却被丢在哥和拿。 (Geenna )
46 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
47 Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu. (Geenna )
如果你的一只眼睛让你犯罪,把它挖出来。一只眼睛进入上帝之国,总好过两眼齐全被丢进哥和拿, (Geenna )
48 Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa.
哥和拿里的虫不死,火永不灭。
49 Domin da wuta za a tsarkake kowa.
每个人会像被‘盐腌’一样,被火灼烧。
50 Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.
盐是好东西,但如果失去了它的味道,怎样才能让它恢复咸味呢?你们需要像盐一样,彼此和睦地生活。”