< Markus 8 >
1 A kwanakin nan, akwai wani gagaruman taron mutane, kuma basu da abincin ci. Yesu ya kirawo almajiransa yace masu,
In those days, when there was a very great multitude, and they had nothing to eat, Jesus called his disciples to himself and said to them,
2 “Ina tausayin taron mutanen nan domin kwana uku kenan suna nan tare da ni babu abinci.
“I have compassion on the multitude, because they have stayed with me now three days and have nothing to eat.
3 Idan na salame su su koma gidajensu ba tare da sun ci abinci ba, za su galabaita a hanya domin gidajensu na da nisa.”
If I send them away fasting to their home, they will faint on the way, for some of them have come a long way.”
4 Almajiransa suka amsa masa cewa, “A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?”
His disciples answered him, “From where could one satisfy these people with bread here in a deserted place?”
5 Ya tambaye su, “gurasa nawa kuke da su?” Sai suka ce, “Bakwai.”
He asked them, “How many loaves do you have?” They said, “Seven.”
6 Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa'annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu.
He commanded the multitude to sit down on the ground, and he took the seven loaves. Having given thanks, he broke them and gave them to his disciples to serve, and they served the multitude.
7 Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen.
They also had a few small fish. Having blessed them, he said to serve these also.
8 Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai.
They ate and were filled. They took up seven baskets of broken pieces that were left over.
9 Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su.
Those who had eaten were about four thousand. Then he sent them away.
10 Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta.
Immediately he entered into the boat with his disciples and came into the region of Dalmanutha.
11 Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi.
The Pharisees came out and began to question him, seeking from him a sign from heaven and testing him.
12 Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, “Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar.”
He sighed deeply in his spirit and said, “Why does this generation seek a sign? Most certainly I tell you, no sign will be given to this generation.”
13 Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin.
He left them, and again entering into the boat, departed to the other side.
14 A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan.
They forgot to take bread; and they did not have more than one loaf in the boat with them.
15 Ya gargade su, “ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus.”
He warned them, saying, “Take heed: beware of the yeast of the Pharisees and the yeast of Herod.”
16 Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, “Saboda ba mu da gurasa ne.”
They reasoned with one another, saying, “It’s because we have no bread.”
17 Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?”
Jesus, perceiving it, said to them, “Why do you reason that it’s because you have no bread? Do not you perceive yet or understand? Is your heart still hardened?
18 Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba?
Having eyes, do not you see? Having ears, do not you hear? Do not you remember?
19 Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, “Goma sha biyu.”
When I broke the five loaves among the five thousand, how many baskets full of broken pieces did you take up?” They told him, “Twelve.”
20 Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, “bakwai.”
“When the seven loaves fed the four thousand, how many baskets full of broken pieces did you take up?” They told him, “Seven.”
21 Ya ce masu, “har yanzu baku gane ba?”
He asked them, “Do not you understand yet?”
22 Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi.
He came to Bethsaida. They brought a blind man to him and begged him to touch him.
23 Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi “kana ganin wani abu kuwa?”
He took hold of the blind man by the hand, and brought him out of the village. When he had spat on his eyes, and laid his hands on him, he asked him if he saw anything.
24 Ya daga ido sai ya ce, “ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa.”
He looked up, and said, “I see men, but I see them like walking trees.”
25 Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau.
Then again he laid his hands on his eyes. He looked intently, and was restored, and saw everyone clearly.
26 Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, “kada ka shiga cikin garin”
He sent him away to his house, saying, “Do not enter into the village, nor tell anyone in the village.”
27 Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, “Shin wanene mutane ke ce da ni?”
Jesus went out, with his disciples, into the villages of Caesarea Philippi. On the way he asked his disciples, “Who do men say that I am?”
28 Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, “Iliya”. wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa”.
They told him, “John the Baptizer, and others say Elijah, but others, one of the prophets.”
29 Ya tambaye su, “Amma me ku ke ce da ni?” Bitrus ya ce, “Kai ne Almasihu.”
He said to them, “But who do you say that I am?” Peter answered, “You are the Christ.”
30 Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi.
He commanded them that they should tell no one about him.
31 Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu.
He began to teach them that the Son of Man must suffer many things, and be rejected by the elders, the chief priests, and the scribes, and be killed, and after three days rise again.
32 Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa.
He spoke to them openly. Peter took him and began to rebuke him.
33 Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa'annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, “Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba.”
But he, turning around and seeing his disciples, rebuked Peter, and said, “Get behind me, Satan! For you have in mind not the things of God, but the things of men.”
34 Sai ya kira taron jama'ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, “Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni.
He called the multitude to himself with his disciples and said to them, “Whoever wants to come after me, let him deny himself, and take up his cross, and follow me.
35 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi.
For whoever wants to save his life will lose it; and whoever will lose his life for my sake and the sake of the Good News will save it.
36 Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa.
For what does it profit a man to gain the whole world and forfeit his life?
37 Me mutum zai bayar amaimakon ransa?
For what will a man give in exchange for his life?
38 Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki.”
For whoever will be ashamed of me and of my words in this adulterous and sinful generation, the Son of Man also will be ashamed of him when he comes in his Father’s glory with the holy angels.”