< Markus 6 >

1 Ya bar su ya zo garinsu, almajiransa su ka biyo shi.
I vyšel odtud a přišel do vlasti své, a šli za ním učedlníci jeho.
2 Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa?
A když bylo v sobotu, počal učiti v škole, a mnozí slyšíce, divili se, řkouce: Odkud tento má tyto věci? A jaká jest to moudrost, kteráž jest jemu dána, že i takové moci dějí se skrze ruce jeho?
3 Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu.
Zdaliž tento není tesař, syn Marie, bratr Jakubův a Jozesův a Judův a Šimonův? A zdaliž nejsou i sestry jeho zde u nás? I zhoršili se na něm.
4 Yesu ya ce, “Annabi ba ya rasa daraja sai a gidansa da garinsa da cikin danginsa.”
I řekl jim Ježíš: Není prorok beze cti, jediné v vlasti své a v rodině své a v domu svém.
5 Bai iya yin wani aikin al'ajibi a wurin ba sai dai mutane kadan marasa lafiya ya dorawa hannu ya warkar da su.
I nemohl tu znamení žádného učiniti, jediné málo nemocných, vzkládaje na ně ruce, uzdravil.
6 Rashin bangaskiyarsu ya ba shi mamaki. Sai ya tafi cikin kauyuka na kewaye da su ya yi ta koyarwa.
I podivil se jejich nevěře, a obcházel vůkol po městečkách, uče.
7 Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu,
A svolav dvanácte, počal je posílati po dvou a dvou, a dal jim moc nad duchy nečistými.
8 ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu,
A přikázal jim, aby ničehož nebrali na cestu, jediné toliko hůl, ani mošny, ani chleba, ani na pase peněz,
9 sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu.
Ale jen obuté míti nohy v střevíce, a aby neobláčeli dvou sukní.
10 Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi.
A pravil jim: Kdežkoli vešli byste do domu, tu ostaňte, dokudž nevyšli byste odtud.
11 Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin.
A kdož by koli vás nepřijali, ani vás slyšeli, vyjdouce odtud, vyrazte prach z noh vašich na svědectví jim. Amen pravím vám: Lehčeji bude Sodomským a Gomorským v den soudný nežli městu tomu.
12 Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu.
Tedy oni vyšedše, kázali, aby pokání činili.
13 Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su.
A ďábelství mnohá vymítali, a mazali olejem mnohé nemocné, a uzdravovali je.
14 Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa.
A uslyšev o tom Herodes král, (neb zjevné učiněno bylo jméno jeho, ) i pravil, že Jan Křtitel vstal z mrtvých, a protož se dějí divové skrze něho.
15 Wadansu kuma suna cewa, “Iliya,” Har yanzu wadansu suna cewa daya “daga cikin annabawa ne na da can.”
Jiní pak pravili, že jest Eliáš; a jiní pravili, že jest prorok, aneb jako jeden z proroků.
16 Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, “Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi.”
To uslyšev Herodes, řekl: Kteréhož jsem já sťal, Jana, tenť jest. Ontě z mrtvých vstal.
17 Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya( matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta.
Ten zajisté Herodes byl poslal a jal Jana a vsadil jej do žaláře pro Herodiadu manželku Filipa bratra svého, že ji byl za manželku pojal.
18 Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba.
Nebo pravil Jan Herodesovi: Neslušíť tobě míti manželky bratra svého.
19 Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba.
Herodias pak lest skládala proti němu, a chtěla jej o hrdlo připraviti, ale nemohla.
20 Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi.
Nebo Herodes ostýchal se Jana, věda jej býti muže spravedlivého a svatého. I šetřil ho, a slýchaje jej, mnoho i činil, a rád ho poslouchal.
21 Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili.
A když přišel den příhodný, že Herodes, pamatuje den svého narození, učinil večeři knížatům svým a hejtmanům a předním mužům z Galilee,
22 Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, “ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi”.
A dcera té Herodiady tam vešla a tancovala, zalíbilo se Herodesovi i spoluhodovníkům, i řekl král děvečce: Pros mne, zač chceš, a dámť.
23 Ya rantse mata da cewa”Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne”
I přisáhl jí: Že začkoli prositi budeš, dám tobě, by pak bylo až do polovice království mého.
24 Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, “me zan ce ya bani?” Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma.
Ona pak vyšedši, řekla mateři své: Zač budu prositi? A ona řekla: Za hlavu Jana Křtitele.
25 Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, “Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire.”
A všedši hned s chvátáním k králi, prosila ho, řkuci: Chci, abys mi dal hned na míse hlavu Jana Křtitele.
26 Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a.
Král pak zarmoutiv se velmi, pro přísahu a pro spoluhodovníky nechtěl jí oslyšeti.
27 Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku.
I poslav hned kata, rozkázal přinésti hlavu Janovu.
28 Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta.
A on odšed, sťal jej v žaláři, a přinesl hlavu jeho na míse, a dal ji děvečce, a děvečka dala mateři své.
29 Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari.
To uslyšavše učedlníci jeho, přišli a vzali tělo jeho, a pochovali je v hrobě.
30 Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar.
Tedy sšedše se apoštolé k Ježíšovi, zvěstovali jemu všecko, i to, co činili, i co učili.
31 Sai ya ce da su “ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan,” domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci
I řekl jim: Pojďte vy sami obzvláštně na pusté místo, a odpočiňte maličko. Nebo bylo množství těch, kteříž přicházeli a odcházeli, takže jsou ani k jídlu chvíle neměli.
32 Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai.
I plavili se až na pusté místo soukromí.
33 Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo.
A vidouce je zástupové, že jdou pryč, poznali jej mnozí. I sběhli se tam ze všech měst pěšky, a předešli je, a shromáždili se k němu.
34 Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa.
Tedy vyšed Ježíš, uzřel zástup mnohý, a slitovalo mu se jich, že byli jako ovce, nemající pastýře. I počal je učiti mnohým věcem.
35 Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, “wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi.
A když se již prodlilo, přistoupivše k němu učedlníci jeho, řekli: Pustéť jest toto místo, a již se prodlilo,
36 Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci.
Rozpusť je, ať jdouce do okolních vesnic a městeček, nakoupí sobě chleba; nebo nemají, co by jedli.
37 Amma sai ya ba su amsa ya ce,”Ku ku basu abinci su ci mana”. Sai suka ce da shi, “ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?”
On pak odpověděv, řekl jim: Dejte vy jim jísti. I řkou jemu: Co tedy, jdouce koupíme za dvě stě grošů chleba, a dáme jim jísti?
38 Sai ya ce dasu, “Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani.” Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu.”
I dí jim: Kolik chlebů máte? Jděte a zvězte. A když zvěděli, řekli: Pět, a dvě rybě.
39 Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa.
I rozkázal jim, aby se kázali posaditi všechněm po houfích na zelené trávě.
40 Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin.
I usadili se rozdílně, místy po stu a místy po padesáti.
41 Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka.
A vzav těch pět chlebů a ty dvě rybě, popatřiv do nebe, dobrořečil, i lámal chleby, a dal učedlníkům svým, aby kladli před ně. A dvě rybě rozdělil též mezi všecky.
42 Dukansu suka ci suka koshi.
I jedli všickni, a nasyceni jsou.
43 Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin.
Potom sebrali drobtů dvanácte košů plných, i z ryb.
44 Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar.
A bylo těch, kteříž jedli ty chleby, okolo pět tisíců mužů.
45 Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen.
A hned přinutil učedlníky své vstoupiti na lodí, aby jej předešli přes moře do Betsaidy, až by on rozpustil zástup.
46 Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a.
A rozpustiv je, šel na horu, aby se modlil.
47 Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai.
A když bylo večer, byla lodí uprostřed moře, a on sám na zemi.
48 Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su.
A viděl je, a oni se s těžkostí plavili; (nebo byl vítr odporný jim.) A při čtvrtém bdění nočním přišel k nim, chodě po moři, a chtěl je pominouti.
49 Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu,
Oni pak uzřevše jej, an chodí po moři, domnívali se, že by obluda byla, i zkřikli.
50 gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, “Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!''
(Nebo jej všickni viděli, a zstrašili se.) A hned promluvil k nim a řekl jim: Doufejtež, jáť jsem, nebojte se.
51 Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai.
I vstoupil k nim na lodí, a utišil se vítr; a oni náramně sami v sobě se děsili a divili.
52 Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare.
Nebo nerozuměli byli, co se stalo při chlebích; bylo zajisté srdce jejich zhrublo.
53 Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka.
A když se přeplavili, přišli do země Genezaretské, a tu lodí přistavili.
54 Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne.
A když vyšli z lodí, hned jej poznali.
55 Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa.
A běhajíce po vší krajině té, počali na ložcích k němu nositi nemocné, kdežkoli zvěděli o něm, že by byl.
56 Ko ina ya shiga birni da kauye, ko a cikin kasar sukan kawo marasa lafiya a kasuwanni suna rokonsa su taba ko da habar rigarsa, dukan wadanda suka taba kuwa suka warke.
A kamžkoli vcházel do městeček neb do měst nebo do vsí, na ulicech kladli neduživé, a prosili ho, aby se aspoň podolka roucha jeho dotkli. A kolikož jich koli se jeho dotkli, uzdraveni byli.

< Markus 6 >