< Markus 2 >

1 Da ya dawo Kafarnahum bayan yan kwanaki kadan, aka ji cewa yana gida.
几天后耶稣重返迦百农,关于他回到这里的消息立刻传遍各地。
2 Da yawa suka taru a can, ba wuri har kofa, sai Yesu ya yi masu magana.
许多人纷纷聚集到他屋子里,甚至簇拥在门前。于是耶稣就对他们讲道。
3 Sai wadansu mutane su ka zo wurinsa dauke da wuni mutum shanyayye, mutane hudu na dauke da shi.
这时有四个人把一个瘫痪的男人带到耶稣那里,
4 Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai.
但因为太拥挤,无法将他带到耶稣面前。于是他们跑到屋顶上,将屋顶拆下来,在耶稣上方的开口处,将瘫痪男人和他躺的垫子送了下去。
5 Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, “Da, an gafarta maka zunuban ka”.
耶稣看见他们的信心,就对瘫痪之人说:“朋友,你的罪被宽恕了。”
6 Amma wadansu marubuta da ke zaune a nan, suka yi tunani aransu.
当时有几名宗教老师也坐在那里,心中暗自思量:
7 Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi “sai Allah kadai?”
“这个人为什么这样说话?他说的都是亵渎上帝之语。除了上帝以外,还有谁能赦免罪恶?”
8 Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, “Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku?
耶稣很了解他们的想法,就对他们说:“你们为什么这么想这件事?
9 Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'?
说‘你的罪被救赎了’,或‘站起来行走吧’,哪一个更容易?
10 Amma domin ku san cewa Dan mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya, ya ce wa shanyayyen,
但为了说服你们,相信人子也有宽恕罪的力量,
11 ''Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka.”
我要对你(瘫痪之人)说:‘起来吧,拿起你的垫子回家去吧。’”
12 Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, ''suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba.”
那人就起来,立刻拿着垫子当着大家的面离开了。众人颇感惊奇,开始颂赞上帝,说:“我们从来没有见过这样的事。”
13 Ya sake fita gefen tafki, dukan taron jama'a suka zo wurinsa, sai ya koya masu.
耶稣走出去,来到加利利海边,众人都汇聚到他面前来,他开始教导民众。
14 Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, “Ka biyo ni.” Ya tashi, ya bi shi.
他继续往前走,看见亚勒腓的儿子利未坐在交税亭处,于是就对他说:“跟我来吧!”利末就起来跟从了耶稣。
15 Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi.
后来耶稣在利未家里吃饭,有很多税吏和“罪人”过来和他和门徒一起吃饭;因为已经有很多人开始跟随耶稣。
16 Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, “Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?”
看见耶稣与罪人和税吏一起吃饭,法利赛派的宗教老师就对耶稣的门徒说:“他为什么和税吏和罪人一起吃饭?”
17 Da Yesu ya ji wannan ya ce masu, “Mutane wadanda ke da lafiya a jiki ba su bukatar likita; sai dai ko marasa lafiya ke bukatarsa. Ban zo domin in kira mutane masu a dalci ba, amma mutane masu zunubi.”
耶稣听言,对他们说:“健康人不需要医生,病患才需要,我来此并非召唤正义之人,而是要感召罪人。”
18 Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, “Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?”
此刻约翰的门徒和法利赛人正在禁食。于是有人过来问耶稣说:“为什么约翰和法利赛人的门徒常常禁食,你的门徒却不禁食?”
19 Sai Yesu yace masu, “Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba.
耶稣回答:“在婚礼中,宾客与新郎在一起时怎么能禁食呢?
20 Amma kwanaki za su zo da za a dauki angon daga gare su, a wadancan kwanakin ne, za su yi azumi.
但等到新郎离开他们,他们就会禁食了。
21 Babu wanda zai dinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar riga, sai rigar ta yage, kuma ta yi mummunar yagewa.
没有人会用新布去缝补旧衣服,因为补丁会把衣服扯破,裂开更大的口子。
22 Babu wanda zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsohuwar salka, ai sai salkar ta fashe kuma ruwan inabin ya zube. duka biyu ruwan inabin da salkar arasa su. A maimakon haka, sai ka sanya sabon ruwan inabi cikin sabuwar salka.”
没有人会用旧羊皮袋装新酒,因为皮袋会被胀破,酒漏出来的同时皮袋也损坏了。人们总是会把新酒装在新皮袋里。”
23 A ranar asabar Yesu ya tafi cikin gonakin hatsi, sai almajiransa su ka fara zagar hatsi,
安息日那天,耶稣走过麦田,门徒们饿了,于是摘了些麦穗充饥。
24 Sai Farisawa su ka ce masa, “Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?”
法利赛人询问耶稣:“你看,你的门徒正在做安息日不允许的事情。”
25 Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi?
但耶稣对他们说:“大卫和他的下属在饥饿时做了什么,你没有读过吗?
26 Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi.”
他走进亚比亚他担任祭司的圣殿,吃下了只有牧师才能吃的圣饼,事实上他们并不允许这么做。”
27 Yesu yace, “Asabar an yi ta don mutum ne, ba a yi mutum don Asabar ba.
耶稣又告诉他们:“安息日为人之益处而存在,而非人为安息日之益处而存在。
28 Saboda haka, Dan Mutum Ubangiji ne, har da na Asabar.”
因为人子是安息日的主。”

< Markus 2 >